Awanni arba’in da takwas suka shuɗe yana bisa kansa, ya jiƙa wannan ya yayyafa masa ya kwaɓa wannan ya goga masa sai dai fa Bawa ba ko gizau, haka bai farfaɗo daga suman da ya yi ba, daga Zawwa har Haadiru sun yi wata irin zabgewa a tsaye a tsayin kwanaki biyun nan sau ɗaya Zawwa ta kurɓi ruwa da wata curarriyar fura guda ɗaya.
Tana son Bawa, son da bata san yadda ya dasu a ruhinta ba a matsayinta na wacce ta yi zarra cikin sa’anninta ta hanyar auren mutumin daya ninka shekarunta. Sai dai haka nan ta samu kanta cikin shauƙin damuwa da dukkan lamuransa, ta sani idan da abinda ya tattaro dukkan nutsuwarta ga Bawan to kuwa ba kome ba ne sai nagartacciyar ƙaunar da yake gwada mata, ya yarda ya ɓata da kowa har ɗan daya haifa a cikinsa akan yaga wani abu mai kama da ɓacin rai a fuskarta.
Ta ja wani gwauron numfashi tana lalubo gefen zaninta ta fyace hancinta, ta ɗago rinannun idanuwanta ta kalli Kakanta da ke ta zana ƙasa yana shafewa ya haɗa wani irin gumi da bata taɓa ganinsa da shi ba. Zuciyarta ta daɗa curewa guri guda wani abu na tattaro mata sunan Hameedu na ajewa saman laɓɓanta, ta gama gasgata Bawa, Hameedu ya biyo kamar yadda bakinsa ya furta farkon sunan nasa, to abu ne ma da ta riga ta sani babu wanda Maigidanta zai iya bi da gudun nan cikin dare idan ba shi ba, tunda dai ba ɓarayi suka shigo musu ba da ɓarayi ne da tuni sun kame su. A kuma kaf duniya daga Babanta sai Hamidu sai kuma su na cikin gida suka san da tarkunan da ke kafe ƙofar gidansu. Ta daɗa jan hancinta tana rasa dalilin da zai sa Hameedu da Bawa su kasa tsere tsakiyar dare, tseren da ya farkarta daga barcinta mai nauyi ta biyo bayansa, sai kuma wani abu mai ƙarfi ya bugi kwakwalwarta ta fara jujjuya idanuwanta a ilahirin gurin babu wanda take nema, ta daɗa wara idanuwanta tana tuna tsabar tashin hankalin da take ciki ya sa ta manta yaro Huzaif da Bawa ya kawo mata ta riƙe kafin Hameedu ya dawo. Ke nan Hameedu ya shigo gidansu ne a tsakar daren nan domin ya ɗauki yaronsa sai Bawa ya ganshi, to amma me ya sa zai shigo a ɓoye me kuma ya sa zai gudu? Ai sai ta miƙe a kiɗime ta isa ga Kakanta ta duƙa gabansa.
“Mutanen ɓoye ne ko?”
Ya dube ta yana tsame hannunsa daga bisa faifan da ke cike da lallausan rairayi.
“Ba su ba ne, wasu irin miyagu ne da suke zame mini duhu a duk lokacin da zan cimmusu. Kaina ya ɗaure da tunanin abinda ya haɗa Bawa da ire-irensu, babu su ko kaɗan a nahiyar nan tamu.”
“Ka duba lamarin Hameedu ka gani, a daren da abin ya faru shi Bawa ya bi.”
Ya yi tsai yana kallonta sai kuma ya fara zana ƙasa yana gogewa tsawon daƙiƙu goma sha biyar, kafin ya daɗa dubanta fuskarsa na warwarewa daga yamutsewar da ta yi.
“Maza je ki kawo mini wani abu na tufafin Hameedu ko da hula ce, ki haɗo mini da wani abu da kika san Hameedu ya taɓa mallakawa maigidanki ko da tsohuwar riga ce.”
“M-me ka gani?”
Ya dubeta cikin ido yana jijjiga kai.
“Ban ga kome ba!”
Ta mike tsaye tana jin zuciyarta na narkewa, tana jin akwai wani abin daya ɓoye mata, sai kuma ta juya ta fice ta nufi gidansu Hameedu.
Tun a farfajiyar gidan ta fara fahimtar abinda ya faru, abubuwa da yawa an wawwatsar a gurin, da ta isa ɗakin Innar tasha mamakin ganin yadda ma’ajiyar tufafinsu take a buɗe an kwashe da yawa-yawan abinda ke cikinta. Dan ta daɗa tabbatarwa ta duba gurin kayan yaro Huzaifu da ita da kanta kwanaki can ta zo ta ɗibar masa kaya, nan ɗin ma babu kome sai marassa amfani, ta shiga laluben abinda ta zo ɗauka har ta yi sa’ar gano wata zungureriyar hular Hameedun. Ta juya za ta fice daga ɗakin a sannan ne idanuwanta suka sauka kan wani allo, ganin da rubutu saman allon yasa ta ƙarasa ta ɗauka tana mamakin wanda ya yi rubutu bai wanke ba. Ta tsurawa rubutun ido tana son gane ko sunayen Allah aka rubuta ta ji ta kasa fahimta. Ta nisa tana tsinewa wawancin da ya hanata koyon karatu da rubutu sai shiga Jeji kawai ta sani, ta ƙara ƙurawa rubutun ido har ta yi nasarar haɗa sunan Bawa da da yawan lokuta ya sha zana mata yadda ake rubuta sunansa da Ajami. Anan ta fahimci ba aya ba ne ko sunan Allah, rubutu ne aka yi da Hausar Ajami, rubutun da ke bata tabbacin saƙo ne.
Ta rungumo Allon ta yi gidanta ta lalubo wata tsohuwar ‘yar shara da Hameedu ya ɗinkawa Bawa a wani Idi ta fito.
Ko da ta isa gurin kakan ta bashi kayan bai ce kome ba sai wuta da ya fara haɗawa a wani babban kasko. Bayan wutar ta haɗu ya ɗauki hular nan ta Hameedu ya jefa ciki ya jawo wani baƙin ruwan magani mai yauƙi ya ɗiga a cikin wutar. Bayan shuɗewar wasu daƙiƙu sai ya ɗauko ‘yar sharar ita ma ya jefa ciki, ya buɗe kwalbar wani ruwan magani mai kalar ɗorawa ya ɗiga ciki. Wani tuƙuƙin hayaƙi ya turnuƙe gurin suka fara tari gabaɗayansu har zuwa lokacin da wutar ta cinye kayan hayaƙin ya fara bajewa.
Ya ɗauko wani ludayin duma ya ɗebi tokar ya zuba bisa wani ƙoƙo ya zuba garin barkono ya ɗauko wani tsattsaman nono ya hau kwaɓa tokar da shi. Bayan ya gama ya isa ga Bawa ya shafa kwaɓin a ƙirjinsa da kewayen idanunawansa biyu.
Suka zura masa ido shi da Zawwa da har ta fara sabon kuka tana sharar hanci, ji take tana daɗa karaya da kome na rayuwar duniya, ta miƙe za ta bar gurin tana daɗa binsa da kallo, a sannan ne taga kamar fatar saman idonsa ta motsa, ta dawo daɓass tana ganin yadda yake motsawa har ya buɗe gabaɗaya idanuwansa yana cije karkataccen bakinsa alamun cikin azabar ciwo yake.
“Ka ga ya farfaɗo, Bawa yi mini magana dan Allah, sannu ina ne ke maka ciwo…?”
Shirun da ya yi yana jujjuya kwayar idanuwansa ya sakata waigawa ɓarin da Kaka ke tsugune suka haɗa ido ya girgiza mata kai yana ɗauke kallonsa daga kanta.
Haadiru da shigowarsa ke nan ya matso da sauri yana kama shanyayyen hannun Bawan ya riƙe. Sai a sannan ta tuna da Allon nan ta miƙe da sauri ta kawo masa tana sharar kwalla.
Karɓa ya yi ya tsurawa rubutun ajamin ido, sai kuma ya hau zare ido yana buɗe bakinsa ya fara karanta musu a fili.
باو، كرك نيميني بزاك عني ب كو امفركن ك. كر كو م ك نيمي دوكيرك بازاك غنتب كو ا زاحيرنك. كي هاقوري د كلر سن رينا، كاي هاقوري د كومي دا زي فارو.