Skip to content
Part 28 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Fita min daga gida fita tun ban kira yara sun zo sun nada maka dukan tsiya ba, tayi maganar cikin wani yanayi dake kara baiyanar da tsananin bacin ranta.

Ya yi murmushi to ai gara ki hanzarta yin hakan kinga inda sai na tafi neman shedar zur kafin in samu biyan bukata a kotu sai ya zamo ba sai na yi hacan ba zan samu don hakan zan sake gaya miki ki bani kudina da na gaya miki jaka bakwai ko kin san tunda na ambacesu zan karbesu ai kin sanni sarai nima na sanki ni dake kar ta san kar ne kin san abinda zan iya da wanda ba zan 1ya ba, na rantse da kwarankwatsa da aradud a matsattsaku in baki bani kudin nan ba, Ya gyada kai nuna alamar wani babban abu zai auku ko yanzu din nan in gaya niki babu fa inda zani sai kin bani don ba zai zame min komai ba in kwana a kan gadon da mijinki ke kwanciya irin kuma tsakaninku bari ma ki gani. Yayi maza yu mike ya nufi hanyar shiga dakinta itama tayi maza ta sunkuci tabarya taje gabanshi ta tsaya.

Kasheni kenan za i yi da kika sunkuto wannan shirgegiyar tabaryar kamar za ki kashe maciji.

Ai gara maciji da kai Nalami ai kai tsohon banza ne tsohon najadu wanda ya tsuta bai san ya tsufa ba kullum kai kenan kana riga fuska da jiki da shuri don na kashcka ai babu abin da zai faru shigowa kayi cikin gidana wadanda suka sanka kuma sun san  mugun iri aka rage shiga dakin ka grni yanzu in ba nuna maka kai din lalataccen tsoho bane matsiyaci.

Cikin duk zagin da baba Lantaria tayi mishi na lura babu abinda yafi tsaya mishi a rai irin cwar da tayi mishi lalataccen tsoho don abinda yafi nanatawa kenan, ni ne lalataccen tsohon? Wato ni ne tsohon kuma ma lalatacce? Yanzu nan ni tsoho ne? Tayi maza ta ce na banza ma kuwa.

Ganin da yayi ta fara yi mishi cin mutunci irin wanda bai zata ba ya sa shi hamzarin fara kudundumarta yana rantse ranste saukin abin ma shi ne yana jin tsoron daga murya don gani yake tamkar in yaran unguwa suka gane shi ne zasu shigo su

sameshi anan din sa karasa aikin da suka fara, amma duk da haka sai da suka kacame suka haura sama suka sauko sai kuma na ji su suna daidaitawa a kan yanda zasu yi su warware lamarin a tsakaninsu ba tare da wasu sun ji maganar ba da kanshi ya ce ya yi mata ragin jaka biyu ta nemi biyar ta ajiye mishi amma babu sauki a haka don kar ta ga ya yi mata sassauci ta dauka ko tsoro ne yana dai so ne kawai su rabu lafiya saboda darajar tsohuwar sanaiya ba a san inda za a sake haduwa ba.

Kai kam bana fita in sake haduwa da kai a ko ina har abada kuma.

Ya ce to ai shi kenan ni kam ai duk mutumin da na sani bana yardamu yi rabuwar banza ni dea shi don ban san abin da gobe azta haifar ba a tsakaninmu na tafi zan dawo bayan kwana bakwai ina fata in zo in samu kudina a ajiye. Bai jira amsar ta ba ya sa hannu, ya gyara rawaninshi ya sa kai ya fita ya bar gidan.

Yana fita daga gidan yanayin baba Lantana ya sake canzawa kana ganinta zaka gane ta tsunduma cikin wani irin al’amari da ita kadai ta san abinda take ji maimakon ta ja bikinta ta yi shiru ko don ta huta gajiyar cacar bakin da sukayi tayi da  na Nalami sai kuma ta shiga kurme kurmcn Ashar da isine tsine wanda yawanci ni take yiwa.

Wannan tsinannen aure da me ya yi kama? Haka kawai ni banci nanin ba nanin zata ci ni, jalka biyar?

To jaka biyar ina na ganta ta sake rushewa da wani sabon kukan.

Watakila Sallau ya gaji ne da ji ko ganin abinda ke ta faruwa ya sa shi buda bakinshi ya ce mata to wannan abin duka baba ai ke ika jawa kanki, in ba haka ba yaushe ake haka ba fa ke kika haifi yarinyar nan ba da ya ce ki bashi ita ai sai ki gaya mishi ba taki bace, amma ba ki yi haka ba sai kika je kina ci mishi kudinshi kina shirya yadda za a yi a bashi ita ba tare da kin nemi hadin kan ta ba, ita gaskiya ai guda daya ce daga kinta kuma ance sai bata, mai kwadayi kuma kowa ya san yana tare da wulakanci yanzu wannan jaka biyar din…

Ban ji karshen zancen ba sai ca ji saukas mari mai karfi kau, bai sake cewa koami ba haka nan itama.

Washegari da safe babana ya yi shiri zai fita kasuwar timatirinshi nima na yi maza ne zo na tareshi da abin karyawar shi dana shirya misali wanda kunu ne kawai sai yan kosan da basu da wani yawa a dalilin ina tattalin kudin da ke wurin nawa saboda sun kusa karewa ban kuma hango wata hanya ta zuwan wasu ba sai dai addu’a kawai da nake tayi na neman rufin asiri wurin Ubangiji.

Yaya nake ganinka wani iri hak baba?  Nayi mishi tambayar saboda yanayin dana gani a tare da shi.

Jikin nawa ne bana jin dadinshi bani da keri ina kuma ganin wasu abubuwa kamar ‘ya’yan  sama suka yi min yawo a idona.

Ya’y,an rana suna yawo baba be jinin ne ya hau ba? Shi ne ba zaka gaya min ba zaika kama ita a haka? Na soma yi mishi kuka sosai, a’a to menene in na fi tan’? Na kalleshi kafin na ce mishi to baba amma in kaje kasuwa kaje ka fadi fa? Ai ka bar fitar kawai ka shiga daki ka yi kwanciyarka in kaji sauki gobe sai ka je. Bai yi magana ba na dauke kwandon tumatirin nashi naje na adana, ya yi min magana a hankali, to in na kwanta me za a ci a gidan ne’?

Tana daga daki tayi maza, yauwa gara dai kai da kanka ka yi mata wannan tambayar ta baka amsar.

Nayi kaar ban jita ba-na ce, to in babu abinci a gida baba sai kaje kana jiri a cikin mutane kana faduwa, suna kwasokasuna kawoka gida? Lafiyar ka bata fiye mana komai ba? Na soma kuka, saboda yawan ciwon nashi yana daga min hankali, loakcin da kake da shi ai ka ciyar da wanda ya kamata dama wanda bai kamata ba yanzu kuwa da baka da shi sai kowa ya yi hakuri wanda ba zai yi ba kuma ya san abinda yake ciki.

Ke na ce ke za ki zage ni ne? Na ce ba zan zage ki ba amma kuma ba zan barki ki tura min uba cikin halaka ba ina kallo shekara da shekaru ya yi yana kawowa don yanzu bai kawo ba kuma babu mai takura mishi, jeka ka kwanta kaji baba? Tayi maza ta ce, to ba dai dakina ba don ban ga yanda za a yi namiji ya kwanta mia a gado zankwankwan ba don takamar zuciyarshi ta mutu. Na sá hannu na bude dakin Sallau ya shiga, kwanta kan shimfidar shi, cikin raina na tabbatar da ma can dole ce kawai zata fitar da shi amma ba dadi yake ji ba.

Yana kwanciya na sake daukan kwano naje na sayo waina da miya na kawo mishi yaci ya koshi har ya rage sannan na kawo magani na bashi kamar yadda likita ya gaya min in tafiyarshi kalau ya sha sau daya in da alamar motsawar jiki ya sha sau biyu kafin mu zo ganinshi, ya kurkure baki ya gyara ya kwanta nima na dawo dakina a cinye masar da ya ragen na wanke kwanon na kife kafin naci gaba da harkokina.

Ina dakina a kwance ina sauraron farkawar Babana sai na jiwo baba Lantana tana kiran Sallau da sabe wai suje su karfbi abincisu ta gama girki na tashi naje na dauki kwano na kai mata a zubawa babana a nan in kai mishi nashi.

Wani irin lalataccen kallo tayi min kafin ta ce min yana daga kwancen ne zan rinka yin girki ina bashi yana kalmasa baki yana lamushewa? Ba ya ce bashi da lafiya ba mai ciwo yana cin abinci ne? Na zuba mata ido cikin tsananin mamakin kalaman nata kafin ince mata komai sai ta ci gaba ai ba nice zan ciyar miki da shi ba ban yi miki wannan alkawarin ba, duk ran da kika sashi ya kwanta a gida yaki zuwa kasuwa toni kuma babu shi a abinci na kin ganima don ki kara sanin banyi dashi ba kin ga barkono ga farin magi ga gishiri duk a ciki na zuba in kuma ke ce za ki fake da shi ki ci to banyi niya ba ni ba baiwarki ba ce in kin kallem kuma za ki gane ni ba matar da za a mayar baiwa ba ce.

Ban san yanda akayi ba naji bakina ya kama ce mata, to me kike da shi da za a ce ki ciyar da baba? Nace mai ciyar da miji in ya rasa ai babbar mata ce wacce ta san rama alheri da alheri ba mai ci ta goge baki ba saboda butulci.

Ina fadin hakan na ga Asabe ta fito daga dakinmu da gudu tana tambayata zaki zage ta ne? Tun kan in amsa baba Lantana ta soma kuka tana fadin to zagi kam na nawa ai ta riga ta zageni.

Kan in san menene abin yi tuni har Asabe ta rufeni da duka tana tambayata wannan wane irin raini ne a gabana za ki zage ta.

Sanin da baba Lantana tayi na kullum mukayi fadan dambe tsakanina da Asabe ita ke kwarata ya sa wucewa ta shiga dakinta ta barmu muna danben.

Danbe mai tsanani muka fara yi sai dai ba a je ko ina ba sai ga shi na sunkuceta na fyadata da kasa a gigice ta kurma ihu mai tsanani wanda ya yi dalilin fitowar baba Lantana cikin sauri da kyar ta iya banbareni a kan Asaben tana rabamu ta nufi kan Sallau ta wankeshi da mari, gigitaccen mari tambayarshi kana kallo aka yi hakan ina amfanin zamanka a wurin? Ya ce uhun baba kenan kema ba kina kallo aka fara ba kika wuce kika tafi? Ni na daina irin wannan abin na daina shigarwa kowa fada ni dukan su daya ne a wurina dukansu yan uwana ne in banda rashin kunyar tsiya meke hadani da Asabe da zanje ina tayata fadan rashin gaskiya.

Tayi ta zage-zage da addu’o’in da ta ga zata iya yi mishi.

Ina daki ina jinta tana cewa Asabe ke dama baki shirya fadan ba kika zo kika rarumeta? To dame wannan abinda kikayi yayi kama ai in ba sake danben nan aka yi ki ka yi mata dukan tsiya ba to raini kawai kika kara jawa -kanki a tsakaninku da can da kike dukanta ma yaya kika kare da wulakancinta balle yanzu da ta jibgeki ta yi miki irin wannan kayarwar?

Lalle ne na gaya miki daga nan zuwa gobe ki san abinda kike ciki da ita.

Duk da na ji maganganun baba Lantana banyi nufin sake yin wani fadan da Asabe ba don nima na fi ganin tsananin sa’a ce ta sani kada ita, amma da gari ya waye da safe naje na sayowa babana abin karyawa zan wuce ta ta sa hannu ta kabe min shi ya kife a kasa na daga ido na kalleta cikin salati mai karfi naji ta ce min, wai rama abinda nayi mata jiya tayi inji in da dadi ai gurin danben da na jata da shi ne na yi dalilin kifewar abincin ta sai kawai na ji tsoron ya gushemin ban tsaya tambayarta yaushe aka yi hakan ba sai na sunkuya na kwashe abinda zan iya kwashewa naje na ajiyewa kaina na sake daukan wani kwanon naje na sayo wa babana wani na kawo mishi sai da naji ya gaya ci na bashi maganinshi ya sha sannan na fito na shigo dakinmu na kama diro da kayan Asabe ina yin watsi da su a waje ina fadin in baki rama abinda nayi miki ta hanyar wulakanta abincin da ubana zai ci ba ai ba zan kara gane ke baki da uban ba Asabe wanda ya san darajar ubanshi ai zai san na uban wani don haka yau za ki bar min gidan nawa uban tunda ya rufa miki asiri baki gane haan ab.

Da gudu ta baro wurin baba Lantana da suke tare ta zata rarume ni nayi maza na juya kanta muka rincabe da danbe ba a je ko ina ba yauma na raruma Asabe na dagata sama na fyadata da kasa.

Baba Lantana tana ganin haka ta zabura da gudu ta dauko itace wai zata bugamin tana fadin na gaji da danben rashin da kike yi min a gida don haka yau za ku gamu da ni za ku ji a jikinku kumą ta fara nufowa da itacen nata nayi maza na kamashi na rike na kalleta cikin natsuwa na ce mata babu sauran duka a tsakanina da ke wanda kikayi min a baya ya isa, na sakar mata itacen ya fadi kasa.

Ta zabura ta nufi dakin da babana yake kwance tana fadin, ina malam din yake kana jin abinda yake faruwa amma kayi gum da bakinka kamar na yi maza na katseta ta hanyar gaya mata cewar ya isa haka kar ki sake zaginshi a gabana kar kuma ki nemi ki daga mishi hankali.

In nayi hakan me zaki yi? Za ki buge ni ne? Ban ce mata komai ba na wuce na nufi dakinmu.

Sallau ya ce uhun baba kenan ai ba ki yarda ba ne da kin yarda…kan ya karasa ta sunkuci itacen da tazo da shi din ta shiga rafka mishi tare da fadin zo ka bar gidan nan zo ka tafi.

Ai babu inda zanje baba in dai ba baba da kanshi ne ya koren ba ban taba samun inda na zauna lokaci mai tsawo a rayuwata ba sai da na zo hannunshi in har kuwa ki na so in tafi to ki kwatantamin inda zan samu dangin ubana tunda kin ce wai ya mutu su kam in kika nunamin su to ba zan sake zuwa inda kike ba sai don gaisuwa amma haka kawai ba za ki kora ni in shiga duniya ba.

Na fito daga wanka na kalli Asabe na tabbatar jikinta yayi matukar sanyi kan abinda ya faru tsakanina da ita jiya da yau nace mata haka a yanda kike na fama da abinda kike fama da shi kice zaki buge ni ina budurwa gal a leda? Ai ke ma kin san karya kike yi ubana ai ya rufa muku asiri dukan ku.

Daga ita har baba Lantanan babu wacec ta tanka min iyaka dai na ganta tayi wanka ta shirya ta fita ta bar gidan ta tafi, nima na shirya na nufi gidan yaya Dija na gaya mata halin da jikin babanmu ke ciki sai dai ban zauna ba na dawo gida.

Ina shigowa na samu baba Lantana tana rabon abinci nayi maza na kwaso kwanuka guda biyu na ce mata ga nawa ga na babana, tayi kamar ba zata zuba ba ban san tunanin da tayi ba sai kuma naga ta dan minmindira mana a zuciyata nace oho na dauka na tafi na kaiwa babana ya ci ya rage sannan naci, ban wani dade da dawowa ba sai ga yaya Dija ta iso babana ya yi ta fada kan zuwan da nayi na gaya mata.

Ta ce to baba za ka yi ta ciwo ne ban sani ba? Ya ce to wannan ciwo da ya riga ya zama jiki ai ba kullum ya tashi ne za a je a fada ba tunda dai itama ya riga ya yi bayanin shi cewar ba a warkewa shi abokin tafiya ne, nayi maza na ce a’a baba ba fa haka ake nufi ba ai kca da hanyar tafiyar shi bai kuma zama dole don kana da shi a ce shi ne abokin tafiya ba ai ana jin saukin shi. Ya ce uhun fata dai ai bai wuce na rokon ubangiji ya bamu sa’a ba rmuka ce amin.

Ta gama abinda zata yi ta fita zata tafi na bita ina yi mata rakiya ina bata labarin abin da ya faru tsakanina da su Asabe da uwarta sai dai babu alamar natsuwartı tana tare da ita saboda yanda na ga tana ta faman har dewa har tana buga tuntube.

Yanzu nan har yanzu wadannan mayun yaran basu daina wadannan wakokin nasu na sharri ba? Na ce mata eh, tyo amma shi ne kike fita? Na yi murmush na ce to vaya zanyi? Ai ya zama min dole in fi ta ta ce haka ze hausawa suka ce wai watan kwaram daya ne in ya mutu sai na wnai ya kama amma mu namu watan kwaran din bai zamo guda daya tunda yau waien kwane sittin ne har da bakwai har yanzu bai mutu ba, bance mata komai ba shiru kawai nayi har ta gama maganganunta muka yi sallama na juyo gida.

Da daddare ina zaune a dakina ni kadai saboda tunda Asabe ta fita ta bar gida bata sake dawowa ba, shirin tafiyarmu asibiti nake yi gobe saboda umarnin da yaya Dija ta bani kenan ta kuma kawo mana kudin zuwa asibiti. Ina cikin kammala abubuwan tunda nasan sai munyi sammako sosai ne zamu iya ganin likitan a kan lokaci sai ga Sallau ya daga labulen kofar dakin tare da ya min magana a hankali, sannu Mero. Na daga kai na kalleshi, yauwa sannu Sallau, ya ya mai jikin? Na ce mishi da sauki. Ya sake rage muryar tashi ta kara yin kasa kafin ya ce min da wata shawara nazo da ita ban sani ba ko zata samu karbuwa a wurinki.

<< Halin Rayuwa 27Halin Rayuwa 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×