Skip to content
Part 36 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Malam Yahuza ya yi matukar farin ciki da ganina ya yi mana karatu mai gamsarwa ya yi mana kuma nasiha kan yan uwantaka irin na musulunci tare da bayani kan wanene musulmi? Lokaci mai tsawo ya dauka yana bayani akan siffofin musulmi na kwarai da Manzon rahama (S.A.W) a kai daga cikinsu akwai kubutar musulmi dan uwanka daga sharrin harshenka ya gama, ya yi mana addu’a muka shafa na dawo gida.

Na soma zuwa makaranta a kunya ce a darare sai dai ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai na wartsake har ma karatun nawa ya zamo daga cikin abubuwan da suke ragemin damuwata su nutsar min da zuciyata musamman ma da yake yayi dalilin da na koma yin karatun Alkur’ani mai girma sosai da sosai wanda da na daina yi saboda damuwa da rudewa in ba haka ba ai na dade ina jin malamai suna fadin cewar shi Alkur’ani waraka ne ga duk wata cuta ciki kuwa har da na zuciya.

Daga komawata makarantar Islamiyya sai mu’amala mai karfi ta kullu tsakanina da malam Yahuza, saboda kullum idonshi yana kaina na zo makaranta ko ban zo ba.

Ki koma makarantar oko don ki samu damar mallakar takardarki ta karatun college, na ce a’a malam ai ni bokon nan ba wani damuna yayi ba. Ya yi murushi to ko bai dameki ba kin riga kin yi shi takardar da za ki mallaka ta zame miki shedar wahalar ki, kar ma ki yi wasa da ita, alhalin ilimin yanzu ya ta’allaka ne a kan abinda aka gani a rubuce don haka ki koma ki yi karatunki karki yi wasa da lokacinki, shi lokaci da kike gani ba a wasa da shi tsada ke gareshi, baki ji abin da wani bature mai hikima ya fada ba? Ya ce “A man who dares to waste an hour of time was not discovered the value of life.

Mamaki ne ya kamani jin da nayi malam Yahuza yana rangada lafiyaiyen turanci da bakinshi bayan na dauka arabiya ko larabci kawai ya iya.

Shirun da nayi ya sashi tambayata ko kinfi gane dai ki jira mijin aurenki ya zo ki yi auren ki kawai?

Shiru nayi ban amsa ba iyaka dai kaina a sunkuye ban kalleshi ba, amma nasan murmushi yayi kafin ya ce min, daina zaman jiran miji Maryam saka al’amura masu yawa a gabanki sai ki ga ma yafi saurin zuwa gareki tunda shima ya san bashi kadai kike jira ba kin gane? Na ce mishi to.

Kalamai da nasihohin da malam Yahuza ya yi ta yi min su ne suka karfafa min zuciyata da ta riga ta karaya da al’amuran rayuwa har na rinka ji da ganin tamkar bani da wata mas’ala ko damuwa a tare dan in dai ba ta rashin lafiyar babana ba ne. Makarantar koyar da sana’o’in mata ta Markas wacce Mansur ya taba bani labari na shiga da taimakon malamina malam Yahuza shi ya karbomin form din na cike ya mayar ya kuma biya kudin form din gashi kuma anyi sa’a kyau ta ce form din kadai ake saya, ajin dinki na shiga shi ne a raina tun sanda Mansur ya ce min ya fi sha’awata da yin dinkin.

Na fara zuwa Markas mas’alolin da na fuskanta ba su wuce na wahalar tafiyar kafar da nake yi da kuma dawowa gida da nake yi ban samu abincin da zanci ba sai na nemawa kaina hakan kuma na jira. Na wayi gari rannan ina gida banje wurin koyon sana’ ata wato Markas a dalilin ranar da Jumaa ce, ranar Juma’a kuma ranar hutu ce a garemu, ina kwance kan gado na na hutawa bayan na kamala wanke mana kayanmu ni da babana sai kawai naji Sallau yana cewa uwarshi, kai an auná arziki yau dai an daura auren Asabe magana ta kare.

Sauri nayi na kara maida hankalina wajen jin maganar tasu tare da tunanin Asabe tayi sa’a itama ta samu tayi aure duk da cikin shegen da tayi ta haihu ni ce dai… kan in karasa tunanin zuciyar tawa sai naji baba Lantana ta ja wani mummunan tsaki tare da fadin, to wani kokari kayi a hakan? Ina ce takardar filina da ya karba kawai nace ka karbo min a matsayin sadakin auren nata ka kasa ka karbomin nera goma. Ya ce, uhun baba kenan ba ki ma san yanda akayi ya bada nera goman bane abinda ja yayi ya tsaya a kan nera bakwai zai bayar sai da malamin da zai daura auren ya ce mishi bai kai rubu’u dinar din da shari’a ta yarda a karba a matsayin sadaki ba shi ne ya bada goamn, ni dai tunda Asabe ta samu mijin aure zata isa gidan mijinta yau danta kuma ya samu uba ba zai yi ta watangaririya a hanya bai san ubanshi ko danginsu ba ai shi kenan magana ta kare a wurina.

Duk da ganewar da nayi Alhaji Nalami Asabe ta aure kalaman da Sallau ya yi sun sani girmamashi tare da auren da Asaben tayi saboda na gane aure daraja ke gareshi Sallau kuma na gane natsattsen yaro mai kuma hankali tsayaiyar tarbiya ce kawai bai samu ba.

Na fara zuwa wajen koyon sana’a ta a Markas babu dadewa’sai kuma malam Yahuza ya sake yi min magana kan wata babbar makaranta ta ilimin addini mai zurfi da aka bude duk da irin kudaden da ya yi min bayanin za a kashe kafi in so ma karatun na shige ta saboda yaya Dija ta amince da shigar tawa ta kuma bayar da duk wani abinda aka nema shi kuma malam Yahuza sai ya taimaka min da manyan litattafai masu tsada a matsayin aro kafin ta samu ta saya min nawa in mayar mishi da nashi tunda shima ba daina karatun ya yi ba tunda shi littafi abin ajiyewar dalibi ne.

A wannan lokacin sai na zama kusan kullum ina da abin yi mafi yawancin lokacin ma nakan fita da safe ne in dawo da yamma saboda zan tashi daga nan in nufi can don ma dai kawai babana yana raina kowane lokaci.

A wannan lokacin baba Lantanaa wuni take yi tana yiwa babana gorin auren da Asabe tayi da na hada ‘yarka da shi kuka ki ai gashi ni na bashi tawa tana kuma zaunen abin ta tsaf cikin rufin asiri da kwanciyar hankali ga mutunci shi aure ai darajarshi yawa ne da ita ba kowane yake samun darajar yin shi ba.

Ina jinsu bana cewa komi, iyaka dai na sani na kuma yarda da kalaman nata duka iyaka dai can cikin zuciyata a yanzu bani da damuwa mai yawa kan maganar yin auren nawa na yarda na kuma gamsu da cewar dak ullum malam Yahuza yake yi na komai lokaci ne kowa kuma yana da nashi lokacin, Nalami kuwa in dai shi zan aura to ina ganin kamar gara in yi rayuwata kawai a haka ya fiyemin don haka ko kadan bana jin zafin kalaman nata.

Ina zaune a dakina bayan na idar da sallar magariba takardun da zan tafi da su wajen malam Yahuza nake hadawa saboda muraja’ar da yake yi min kan wasu darussan masu dan nauyi da nake bukatar fahimta mai kyau a kansu, har zan yafa hijabina in fita sai kawai naji yaro ya shigo yana cewa wai ana sallama da Maryam a waje. Na daga ido na kalli agogo cikin zuciyata na ce kar dai Halliru ne ya zo a wannan lokacin. Halliru shi ne sabon saurayina da Yakumbo ialima ta turo min a dalilin ya ce mata ta duba mishi budurwa mai hankali da iya kwalliya kasancgwar shi dan mijinta da ta rike ya sa ta ce bai dace da kowaccc budurvwa ba sai ni, ni kuwa a wannan lokacin bani da wani zabi na kaina, ko in zaba ince ga irin saurayin da nake so ko ga irin mijin da zan aura, aurcen kawai nake so wanda duk yazo kuma a shirye nake zan aure shi, in dai huta babana ma ya huta mu duka mu huta damunmu da ake yi ana bada bayanin mu a kan idona sai ka ji dattawan unguwar suna cewa ai nan kusa kusa duk ai babu sauran sa’arta kai kannenta na kusa ma babu duk sun gama yin aure sai ita kadai.

Na debi littafin nawa na rungume na jawo kofata na rufe na yiwa babana sallama na fito da nufin in mun gama maganar da za mu yi sai kawai in wuce na kuma san ganina tare da litattafan a hannuna zai kara sashi tafiya da wuri tunda yasan ina da abin yi.

Ina fita waje maimakon in ga Halliru, Mubarak na gani a tsaye, wani irin lalataccen kallo ya yi min da ya sanya gabana faduwa cikin zuciyata na yi maza na ce, ban yafe maka ba zuwa kofar gidanmu da kayi ka fadar min da gaba.

Shima malamin naki yana nema ya rikide ne ya zama saurayinki? Da sauri na daga ido na kalleshi cikin tsananin mamaki abinda ban taba zaton wani zai yi tunanin hakan ba don babu wata alama da take nuni da hakan.

Idan kika kuskura na gane da wani abu a tsakaninki zaki bar karatun naki gaba daya ki koma zaman gida in kuma kina ganin kamar wasa nake yi to bari in gane hakan, ki gani kina nufin don yana koyar da ke karatu a da sai kuma a yanzu ki rinka kwasar litattafai kina zuwa wurinshi kuna zama ku biyu?

A kidime nace mishi, ba fa mu biyu bane? Ya yi maza ya katseni ko ku dubu ne ban yarda ba kar in sake gani ko jin kin fita daga gida bayan sallar magariba, na gaya miki.

Kuka na soma yi mishi saboda bakin cikin abinda yake yi min, takuraw ar ta kai duk inda ta kai, komai nake yi ya sani ko baya nan nayi in ya dawo zai ji labari.

Cikin karfin hali na daure zuciya ta na ce mishi, to wai ni ina ruwanka da ni ne? Ina abinda ya shafeka da abinda nake yi, kullum sai ka shiga harkata, kullum sai ka takurawa rayuwa ta.

Ban san dalili ba rannan sai na kasa zuwa wurin muraja’ar da Malam Yahuza ke yi min, maimakon washegari ma inje ban iya ba, sai kawai na hakura da muraja’ ar na koma maida hankalina sosai a aji wajen fahimtar dukkan darussan da ake yi mana.

Kullum dai burina bai wuce in samu lokaci in tatawa Mubarak rashin mutuncin da zai sa ya fita harkata kwata-kwata ba amma in na ganshi sai in kasa saboda kwarjininshi da yake yi min nauyi a idona.

Gabatowar watan azumin ramadan mai girma ya sa aka shirya mana jarrabawar da a bayanshi muka samu hutun makaranta har sai bayan salla mu koma, farin ciki sosai nayi a wannan lokacin a dalilin jarrabawa ta tayi kyau banda haka zan dan samu hutun wahalar da nake yi ta zuwa makaranta da kafa in dawo da kafa, Sannan zan dan fuskanci wani abinda nake kuma dokin yi shi ne dinki don na dan fara iyawa har yaya Dija ta gamsu da labarina bayan dinkin ‘ya’yanta dana dade ina yi musu ta hada min har da nata nayi a dalilin hakan kuma ta ma karbar min na kawayenta da abokan zamanta.

Ki natsu sosai ki yi musu mai kyau don sai ya zamo tamkar tallan iyawarki kikayi, nace mata to.

A wannan lokacin hutun makaranta da dokin dinkin azumi da nake yi ne ya ragemin damuwa ko bacin ran da na samu kaina a ciki raina dalilin turowar da Halliru ya yi a ka karbe mishi kayanshi, shi ko kayan na gani ina so kamar yanda wasu suke fada da da ya kawo gidan mu haka kawai ban san hawa ba ban san sauka ba wadanda suka kawo kayan suka zo suka ce a yi hakuri a basu bisa wasu dalilai da suka ce wai su ne sukayi dalilin in fasa auren nashi a wannan lokacin.

Yakumbo Halima dai ta ce min wai yayi mata bayani da cewar ya fasa auren ne a dalilin akwai wani dodo dake biye da ni mai tsoratar da mutane matukar kuma ba a tsaya an rabani da wannan dodon ba to aure na zai yi wuya.

Bayanin nashi ya yi tasiri mai karfi a zuciyar Yakumbo don salati ta rinka yi tana fadin, wai dama tuni ta dade tana tunanin watakila aljani ne da ni wanda ya hanani yin aure.

Ni kam tattara maganar nayi na ajiye a gefe ban yarda ba ban kuma karyata ba don ban san komai a kan irin wadannan alamuran ba, abu guda daya dana sani na kuma yarda na tsaya a kan shine gaba daya mu mutane da kuma aljanu dukkanmu bayi ne na Ubangiji babu mai ikon cutar da wani a tsakani sai da abin da Ubangiji ya yarda ya kuma kaddara fil azal wannan din zai cutu da shi, wannan shi ne bayanin da kullum malamin mu na tauhidi yake yi mana da sai kuma na yarda sai na samu natsuwa da kwanciyar hankalin dana fuskanci al’amurana na dai san kawai na koyi yin addu’a.

Sai dai kuma tawakkalin da sanin da nayi cewar babu mai yi ko hanawa sai Ubangiji bai hana zuciyata kuntata ba a dalilin aure nake so auren kawai nake so, SO nake in ganni nima a zaune a nawa dakin ina zaune ina aurena ga Asabe tunda ta yi aurenta tana dakinta ban sake ganinta ba, kullum kuma sai uwarta ta yada magana a tsakar gida ta ce, yin aure ai rufin asiri ne Asabe asirinta ya rufu tana can dakinta cikin rufin asiri, ubangiji ya sanwaka ace yar mutum tayi ta galantoyi a gaban shi, yana kallonta kowa ya zo ya yi kamar zai aureta in ya taya ta sallama yaga araha sai kawai ya yi dani ya tafi. Tir, ta ja tsaki fa ci gaba da harkokinta.

Cikin zuciyata dai na kan yi mamakin al’amarinta saboda a farkon abinda ya faru da Asabe na dauka zata fita hanyar irin wadannan abubuwan sai ya zamo ko a jikinta ba ta ma tuna nata sai dai na wani dama bai karasa natan lalacewa ba.

<< Halin Rayuwa 35Halin Rayuwa 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.