Skip to content
Part 4 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Ba kina sallolinki a kan kari ba? Nayi maza na ce mishi eh babu, ba kya kuma sabon Ubangiji da gangan, na girgiza kai nuna lamar a’a, ya ce To in sha Allahu in kin yi addu’a ladan zai kai gareta ga kuma Yayarki da take zaune a dakin aurenta, tunda a ka yi aurenta ba’a taba jin wani abu na rashin jin dadin game da ita ba, kin gani? Cikin yardar Ubangiji addu’o’inku za su rinka kai wa gare ta.

Na sake kallon shi a hankali na ce mishi menene sabo Baba? Ya zuba min ido kafin ya gano ta inda zai Bullowa lamarin, irin su karya, gulma da shiga harkar da ba taka ba, da bijirewa iyaye ko zina da makamantansu kin gane?

Nayi maza na ce na gane, kusan kullum sai na lissafawa kaina laifuffukan da Babana ya lissafa min a matsayin zunubi ko sabo, don kar in aikata su saboda kar in aikata su su zama sanadin da addu’o’ina za su daina kaiwa ga Innata.

Kusan kullum na zauna tare da Babana muna hira zai yi min nasiha da cewar in kasance mai gaskiyaa kan al’amurana in kuma tsare mutuncina kar in yarda wani yayi min wayo duk abin da na gani naji ina so in gaya mishi ban da karbar abin hannun wani ita mace bata da wata daraja komai kyanta in har bata zama mai kamun kai da tsare mutuncin rayüwarta ba, in ce mishi to din ba tare da na san mé maganar tashi take nufi ba har na gane komai.

Rannan na idar da sallar Asuba ina ta doki da zumudin Babana ya shigo in ba shi labarin da ke cina a raina, yana shigowa na soma gaishe shi ba tare da na jira ya kai mazauninshi.

Cikin natsuwa na kalle shi na ce mishi Baba zan yi sadaka yau, ya kalle ni cikin natsuwa ya ce sadakan me kike son yi uwata? Na ce ko na meye ma Baba jiya da daddare nayi mafarkin Inna wai tazo gidannan na ganta lullube da fararen kaya tana kallona tana ta faman murmushi ni kuma sai tambayarta nake yi Inna dama ashe za ki iya zuwa wurinmu shi ne tunda kika tafi baki taba zuwa kin duba mu ba, ni da Babana?

Ina maganar tana kallona murimushinta kawai take yi ni kuma ina kokarin matsawa kusa da ita don in taba ta ina cewa Inna kiyi mini magana mana har zan taba tan sai kawai naga ta bace sai kuma kawai naga ra farka daga baccina.

Cikin natsuwa ya zuba min ido yana kallona lokaci mai tsawo bai kawar da idanuwan shi daga gare ni ba har na fara jin tsoro ko yayi fushi ne saboda maganarta da nayi mishi tunda ya sha ce min in an tunata ayi mata addu’a kawai basai an yi zancenta wani ba har zan buda baki in bashi hakuri tare da alkawarin ba zan sake yi mishi hirarta ba sai naji ya ce min jiyan da kika yi mafarkinta ai jiyan ta shekara.

Na yi maza na daga ido na kalle shi a firgice saboda razanar da nayi sai ya ce min kin gani in ba ki manta ba ta rasu ne ranar sha tara ga waran Jimada Thani, to yau ma ai shataran ne ko ashirin ga watan.

Na ce Haka ne Baba, lokaci mai tsawo ya dauka yana yi mata addu’a tare da sauran Jama’ar Musulmi da suka rigaye mu baki daya in kuma tamu cikawar tazo to Ubangiji ya azurtamu cikawa da kyau da Imani.

Nayi maza na ce amin Baba tsawon lokaci muna zaune shiru babu wanda ya sake furta wata magana sai na bude baki da nufin fadin abinda ke kai kawo cikin raina a hankali na soma yin maganar cikin yanayin girmamawa da tsoro don kar ya hana ni abin da nake nufin fadin tunda yasha gaya min cewar maimakon yawan ambaton Inna da yawan maganarta mu rinka yawan yi mata addu’a kawai.

Zuba min idon da yayi yana kallona shi ne ya kara tabbatar min da cewar ni yake sauraro, don haka cikin natsuwa da ladabi sai na buda baki nace mishi Baba tafiyar ta Inna ta fara nisa duk da a lissafi ne kawai Inna ke da shekara guda a yanzu in a kewa da kadaicinta ne mun kai wani matsayi da ba zai yiwu mu kwatanta ba. Duk da haka shekara gudan lissafin ma lokaci ne mai tsawo da yawa in ban da tafiyar tata bata dawowa ba ce da yanzu ta dawo ko kuma damun soma sa rai da dawowan nata.

Cikin natsuwa ya ce min eh, Maryam ai tafiya ta yi wata irin tafiya ce da dadewa bai sawa a dawo, da dadewa kansa a dawo ai da mu ma iyayenmu sun dade da dawowa.

Nayi maza na ce haka ne Baba, kamar in yi mishi wata maganar sai kuma naga to bari kawai in ja bakina in yi shiru.

A wannan lokacinne na shiga aji shida na Makarantar Primary na fara girma har Babana ya fara barina ina tafiya gidan Yaya Dijah ni kadai don yi mata wuni. Ina matukar son zuwa gidanta saboda yadda na lura na gane bata da wani wanda take so da kyautatawa irina.

Kullum naje gidanta to bata gajiya da tattalina da tarairayata komai na ce mai kyau ne cewa take yi in dauka tana ganin na kwana biyu ban je ba zata shiga aiko kanen mijinta suzo su ga lafiyata, in kuwa naje bayan aiken nata zan gamu da fushinta kan dadewan da nayi ban je ba, kullum a cikin yi min nasiha take tana ganin zani aikata kuskure zata yi maza ta gyara min. Yadda Yaya Dijah ke sona da ji da ni haka shima mijinta yana ganina zai fara murmushi ina Inna take? Zo maza ga Mamanki tazo.

Sanin da yayi kullum naje gidan Yaya Dijah zata tasa ni a gaba da aikace-aikace har da su hidimar girki wai kar in girma ban iya aikin mace a gidanta ba, yasa yana ganina zai je yayi sabon cefane ya kawo ko da kuwa ba a ranar suke bukatar cefanen ba sai ya ce in na girka in tafi mana dashi gida muyi amfani da shi ni da Baba.

Ina son Yaya Dijah da mijinta ina kuma matukar son ‘ya’yanta Inna da Abbati, ina son su irin son da ba zai kwatantu ba, saboda gani nake tamfar su din su kadai sune dangin da nake da su sai kuma nake kallonta kallo irin na uwa, ganinta nake tamfar ita ce madadin Innata da na rasa.

Dangin mijinta kuma ‘yan uwa saboda suna sonta kowane lokaci kaje’gian sunanan aurenta aure ne na soyayya, fahimta da kuma kyautatawwa juna, don haka gidanta gida ne na farin ciki da kwanciyar hankali, kudi masu yawa ne kawai ba su da su amma suna cikin rufin asiri.

Ni da Yaya Dijah kamannin da ke tsakaninmu ba wasu masu yawa ba ne, ba su wuce wadanda zaman ciki na kasancewa shakikai ke haddasawa ba, yayin da nake matukar kama da Innarmu ita kuma kama da Babanmu take yi.

Haka nan ko a halayenmu mun bambanta mace ce mai matukar hakuri bata kuma da kwaramniya.

A wannan lokacin saboda na riga na fara yin wayo na fara fahimtar me nake ciki sai na zama babu abin da nake so nake fata da buri irin in ganni nayi haddar Alkur’ani mai girma a dalilin kullum sai Malaminmu na Alkur’ani yayi mana bayani kan falala, girma da kuma darajar mahaddata Alkur’ani a ranar alkiyama su da yayensu.

Sai na zamo ina matukar kwadayin nima iyayena musamman ma Innata da nake rayuwa cikin tsananin kewarta da begenta su samu irin wannan matsayin a gobe kiyama.

Kowane lokaci a cikin taka tsan-tsan nake na kauce wa aikata laifi musamman yin karya da duk wani abin da Mallaminmu ya ambata cewar laifi ne don in samu in zama ‘ya ta kwarai saboda ya ce mana ya’ya na kwarai suna daga cikin sadakatul jariya da mutum ke bari a duniya wanda ladansu ba su yankewa a gare shi.

Rannan ina tare da Babana a cikin gidanmu da daddare a kishingide yake a kan tabarma yayin da yake jan carbinshi a hankali cikin natsuwa idanuwanshi a kaina suke tare da natsuwar shi saboda sauraron haddar da nake kawowa na suratul ‘ANKABUT”.

Sai da na kai karshe na sake kallonshi cikin natsuwa kan in gaya mishi abinda nake nufin gaya mishin sai ya ce min kina da murya ta karatun Alkur’ani Maryamu, kar ki yarda ki daina, kar ki yarda kiyi wasa ta basirarki na ce mishi to Baba, kan in yi wata magana sai ya sake bani umarmi na in maimaita surar, ya ji ta dá kyau.

Sau biyu na maimaita sannan yayi murmushi ya ce a’a lalle hadda ta zauna sai kiyi ta tilawa kar ki yarda kina yin sake don shi Alkur’ani kana barinshi sai shima yayi nesa da kai, don haka ki dage da tilawarshi. nayi maza na ce to Baba. Yi mana addu’a, na sake cewa to nayi muka shafa sannan muka je muka kwanta.

Rannan da safe muna aikace-aikacenmu a gida ni da Babana kafin ya fita kasuwarshi nima in tafi Islamiyyata tunda ranar ta Asabar sai naji ya ce min ni Mero ba ki iya komai ba ne cikin girke-girken da ki ke cewa ‘yar uwarki tana nuna miki?

Na yi maza na bar abinda nake yi na kalle shi cikin natsuwa da zumudi na ce mişhi Baba duk abincin da nake zuwa da shi gidan nan fa ni nake yi Yaya Dijah zama kawai take yi tana kallo in taga zan yi wani abu ba daidai ba ta gyara min.

Shiru yayi yana kallon wuri guda nuna alamar a cikin tunani yake, na bar abinda nake yi na sake kallonshi tare da tambayarshi mene ya faru Baba? Kaji miyar bata yi dadi ba ne?

Yayi maza ya gyada kai uh’uh ba haka ba ne Mero tunani dai nake yi na in har ke ce da gaske ki ke yiwo mana wannan girkin to ai gara in hutar da wadannan yan uwa namu da suke ta faman dawainiya damu shekara guda har da wasu watanni tunda mahaifiyarku ta rasu ba su taba hutawa da hidimarmu ba.

Don haka in har za ki iya to sai in sauke musu nauyin girkinmu su rinka yin nasu kawai in rinka kawo cefanenmu kina yi mana.

Nayi maza na ce eh Baba gara kawai muyi hakan can cikin zuciyata murna nake yi da zumudi saboda babu abin da nake so nake kuma sha’awa irin in ganni ina girki ni kadai ba tare da ana nuna min ba wai ni a dole na iya.

Wannan maganar da muka yi da Babana bata wani dade ba don ko kwana bakwai bata yi ba,  naje karbo cefane kamar kullum yanda na saba ni ke zuwa wurin shi in karbo cefanen kayan miya gami da su manja ko man gyada da maggi in kai ma Babah Sumaye shikuma Baba Hodijo yayi abin da ya saura tare da hatsi.

Ina tsaye ina jiran ta gama hada min in dauka in kawo mata sai kawai naga ya miko min ledoji guda biyu, ungo ki kai mata daya ke kuma ki girka mana daya.

Gabana ya yanke ya fadi tamfar dai’ ba ni ce na ce mishi na iya girkin ba. Zaro idanuwa nayi ina kallonshi yayin da shi kuma ya ci gaba da yi min bayani, na riga na yi wa Mallam Hodijo bayanin komai, don haka kaiwa ita uwar taki kunshi daya ki rike daya.

Kije ki girka mana abinda ki ka san shi ki ka fi iyawa kin gane ko? Na ce mishi to Baba, na kamo hanya ina dawowa gabana sai faduwa yake yi ban taba yin girki ni kadai babu wani babba a wuri ba hasalima kafin rasuwar Innata bana shiga kicin da sunan ya yi girki ko da kuwa na wasa ne.

Babah Sumaye ta zubawa cefanen ido tana kallo yanzu nan bawan Allahn nan da gaske yake yi sai ya raba girkin nan? Ta dan gyada kai tare da fadin to ai shi kenan tunda haka ya gani dai, amma menene’? Ai mun riga mun zama dan abincin da a ke sa mishi guda nawa yake?

Ban da haka ma kullumn fa cefanen nan a wurinshi ake karbo shi amma ya ce wai dawainiyar da ake yin tayi yawa, ni dai nafi zaton ko subutan bakin da nayi na ce a gaya mishi ga wata bazawara na saman mishi ne duk ya kawo hakan.

Ni kuma ba nayi hakan ne don na gaji a sa mishi tuwo ba a’a ko kadan ba haka ba ne nayi mishi tallan bazawarar ne don ganin hankalinta da natsuwarta shi kuma yana ta zaune a haka yau kusan shekara daya da rabi da rasuwar Ramatu, wanda wasu da kyar suke jira ayi arba’in sai kawai ka ji sun daura aurensu.

Yadda dama ban san anyi wannan magana da Babah Sumaye ta rattaba min ba haka a yanzun ma da ta rattaba min ban nuna naji ko na gane inda Zancen nata ya nufa ba, balle in furta wata kalma.

Sa hannu kawai nayi na dauki leda guda daya na juyå da nufin fita daga gidan saboda nima ban san dalili ba sai naji maganar ta dan sosa min zuciya ina fita daga gidan dai ina jinta tana cewa bai fahimce ni ba ne, ban gaya mishi hakan don ban damu da rashin da aka yi ba sai dai don sanin da nayi cewar yadda duk muka kai da son Ramatu to babu yadda za muyi tunda ta riga tayi tafiyar da babu dawowa a cikinta sai dai kawai muyi ta binta da addu’a.

Ina shiga gida na juye kayan cefane na kama wankewa sai da na gama tsaf naja na tsaya ina kallon kicin din wanda rabon da a girka wani abinci mai muhimmanci a ciki har an manta, sai a lokacin ne kuma naji na dibibice na rude na rasa ta ina ne ma zan faro?

Na zubawa murhun ido ina tuñanin yadda ma za a yi in hada itacen su kama su zama wutar da zata kama ta girka abincin da zai nuna ya zama tuwon da za a ci.

Tsawon lokaci ina tsaye a wurin nan ina tunanin ta inda zan faro sai ga Jumare ta shigó da saurinta. Babah Sumaye ce ta ce in zo in ga abinda kike ciki da cefanen da ku ka zo da shi in taya ki girkin da za ki yi.

Nayi maza na ce mata gashi nan saboda taimakon nata yazo min ne a daidai lokacin da nake bukatarshi.

Duk da taimakon da Jumare ta kawo min da aiken da Babah Sumaye tayi-tayi na ayi kaza kar ayi kaza abincin da muka girkan yawanshi ba kadan ba ne, dandanonshi kuma ba wani mai gamsarwa ba ne ko in da aiken nata da zuwan Jumaren wane irin kwaba zan yi? Oho.

Duk da min karbi girkin abincinmu Babana bai daina bada kayan miya a gidan Baba Hodijo ba babu kuma wani abinda ya canza a tsakani ni kam ma dai ban daina zuwa karban abincina ba ina shiga gidan Babah Sumaye zata ce min ga abinci can in za ki ci jeki ki diba in ce mata to dama kuma hakan take yi min.

Haka nan duk wani abu na kulawa da take yi min bai sauya ba, ina dawowa daga Makaranta wurinta nake fara zuwa in tube kayana in canza da wanda ke nan a wanke a goge in ci abinci in yi wanka in yi sallah in yi shirin tafiya Makarantar allo bayan na karbo cefane na kawo.

Zan iya cewa kwanon Babana ne kawai aka cire shi ne kuma mai cin abincin da nake kwabawa da sunan girki sai ko yaran da nake turawa a cikin gidan wadanda rasa uwata da nayi ya koya min lura da sa ido wajen sanin ‘ya’yan da ba su da uwa a dalilin suma mutuwa ta daukan musu ita kamar yadda ta daukan min tawa ko kuma a’a sakin uwar tasu aka yi aka bar su watse a tsakar gida.

Duk.munin abin da na girka Babana bai cewa komai, bayan sannu da kokari sai yayi bisimillah yayi komai uku yayi hamdala ya ce in kawar ko in nemi wadanda zan ba, in ce mishi to in je in kawo mishi ruwa.

Zuwan da nayi gidan Yaya Dijah ne na bata labarin dukkan abubuwan da suka faru har da bayanin da Babah Sumaye tayi ina ji, shiru yaya Dijan tayi cikin wani yanayi na nuna tsananin tausayi ta ce uh’uhummn, Baba ina jin tausayinshi in na tuna Inna na tuna halin da na samu kaina a ciki a dalilin rasata da muka yi.

<< Halin Rayuwa 3Halin Rayuwa 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.