Skip to content
Part 50 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Dadin abin shi ne babu ta inda abinci bai yi ta shigowa ba daga gidansu Mubarak ma katuwar kula aka kawo cike da farfesun kayan ciki ga kuma tuwo miyar kuka nima a cikin gidanmu nayi mishi burabuskon gero da miyar kuka da naman kaji a ciki na kuma zubawa kowa har da baba Lantana da ta k tsayawa ta yi girkin.

Anyi sallari sha’i sanda naji zuwan Alhaji Muhammadu ya zo yiwa wan babana barka da zuwa va kuma dade a wurin suna hira kafin ya yi musu sallama ya tafi. Gaba daya ‘yan hira suka watse aka bar babana da dan uwanshi saboda kafafuwa sun fara daukewa alamar dare ya fara nisa gashi kuma lokaci ne na sanyi amma duk da haka baba Abba Gana ya shiga gida ya ki shiga.

Wai shi zauren ma ya isheshi don haka a nan sukaci gaba da zamansu nima nayi maza na hura wuta cikin kasko na kai musu. A haka suka kwana suna hira ba na zaton sun samu runtsawa don sau biyu ina farkawa cikin dare ina jin zancensu sai dai bana gane me suke fadi saboda barbarcinsu suke yi.

Washegari da safe daga gidan yaya Dija aka kawo lafiyayyen abin karyawa wanda basu da cikin gidanmu ba kawai har gidan su baba Sumaye sai da aka kai musu. Ina zaune a gefe sai taya babana murmushin da yakeyi nakeyi saboda jin dadin ganin dan uwa da yayi a zuciyata kuma ina tunanin yanda muke ni da yaya Dija haka su ma suke uwa daya uba daya sai dai kawai su maza ne mu kuma mata, ina wannan tunanin ina kuma kwatanta girman al’amarin da ke tsakaninsu sai na ji yaya Ibrahim yana ce mishi, baba ai sai kawai ka tsaya a yi daurin aure kafin ka tafi tunda ita Yacuwunan ai kwanan nan ne za a daura auren nata.

Da sauri ya ce a’a a’a a’a ba za ta tsaya a nan ta daura aurenta ba zata kai ta can gida dangi ma ta ganta mijinta tana sonta ta bita can gida ma zata bata in bata Sonta ta zauna ta bata miji a cen shi kenan miji kam tana karewa ne?

Duk da irin yanayin da yayi maganar a ciki kowa ya gane abinda yake nuff gaba daya sukayi tsuru tsuru ana kallonshi an rasa mai karfin halin da zai musu maganar tashi ni kuwa ko a jikina ban damu ba don ya ce zai tafi da ni tunda dai babana ya yarda wanshi ne uwa daya uba daya kowa ya gansu tare kuma sai ya yi magana a kan kamanninsu dan uwan babana ne ban damu ba duk yanda yaga dama ya yi dani musamman ma kuma da yace zai kaiwa dangi ni don su kara yarda da cewar shi din ya ga Abubakar yana nan a raye har ga sheda nan ya zo da ita.

Na yarda mai kama da shi karo na farko da na ji wani ya ce wai ina kama da babana. Yaya Ibrahim ya shiga yi mishi kalamai da bayanai na nuna mishi wai ai tunda ya riga ya zo sun ganshi sunji bayanin komai to yana tafiya za su je don haka ba sai ya tafi da ni ba daga zarar an gama bikin zai gayawa angno ya kawo musu ni ko ma mu taho tare dukanmu ai kaga uban angon baba shi baya nan ne ya yi tafiya. Baba Abba Gana ya kalli yaya Ibrahim cikin natsuwa ya tambayeshi, a’a Ibrahimu zata hanata tafiya da abinta ne? Yayi maza ya ce a’a baba ba haka bane.

Ya gyada kai tare da fadin, to insha Allahu zata je da ‘yan uwana. Ya sake bude baki cikin natsuwa ya ce mishi, to ko zaka daga tafiyar daga gobe ka kai jibi don mu yi shiri mu maida kai gidan.

*****

Haka nan ba yanda nayi zaton ganin Gaidan din na ganta ba gari ne babba da ya ci gaba a kan al’amura da yawa musamman ma masarautarsu haka nan zamantaaekwar garin akwai sha’awa a ciki mutane ne masu kula da lamuran addini. Babana yan uwa ne da shi sosai abin har abin mamaki yanda ya iya tsallake yan uwa da dangi masu yawa haka yayi tafiyarshi ba tare da ya taba waiwayarsu ba.

Sai dai banfi kwana uku da zuwa garin ba na soma jin labarai iri iri na abinda ya yi dalilin da ya sa babana ya tsallakesu ya yi tafiyarsu, labaran dai iri-iri ne kowa kuma da irin abinda yake fada sai dai wanda nafi kamawa shine wanda matar baba Abba Gana ta bani da kanta wato Kabudi sunan da na ji suna kiranta.

Kenan ita ce ta shedamin cewar su su babana su biyu ne wurin uwarsu daga shi sai Abba Gana saboda ita uwar tasu ta rasu da wuri hasalima bayan haihuwar baban nawa da kadan ne ta rasu, sun fara maraicin mahaifiyarsu baa wani dade ba sai na uba ma ya same su don haka sai rikon nasu ya koma hannun kanin mahaifinsu wanda ko kadan bai kula ya tsare zumuncin dake tsakaninshi da dan uwanshi da ya rasa ba banda gadonsu da ya cinye tun basu isa komai ba sai kuma suka taso a hannun nashi cikin wahala mai yawa.

Shekara da shekaru dai su ne masu noma mishi gonakinshi da suka taso kuma yaga sun isa munalin aure har wani tsohon aminin babansu da ya rike zumunci ya baiwa Baba Abba Gana auren ‘yarshi shi sai ya nuna yarshi da ta soma tasowa yace in ta isa aure ta babana ne tana isa auren kuma sai dan mai kudin garin ya zo ya ce yana sonta sai kawai ya dauketa ya bashi ya ce babana ya yi hakuri ga kanwarta nan in ta isa auren zai bashi.

Itama da ta isa auren sai ya dauketa ya sake baiwa wani da ya zo daga waje ya bashi kudi bai lura da cewar shekara da shekaru babana ke nomoe mishi gonakinshi ba, ana cikin haka ne ya sake cewa an satar mishi kudinshi da yake binnewa a gonarshi a gindin bishiya babu kuma wanda zai yi mishi wannan satar in banda babana don yafi kowa sanin gonar.

A dalilin haka ne ya yi mishi wulakanci a bainar jama’a, tare da fadin wai tuni dama shi ya gane duk sace-sacen da ake yi a nan gidan dama makwabta ba kowa ba ne ila shi kam haka ya kwace mishi ‘yan kadarorin shi da ya yi aikin kodago ya dan adana kwanaki biyu ne kawai da faruwar hakan da safe ya dauki garmarshi ya fi ta kamar yanda ya sabayi kullum sai aka ga shiru bai dawo ba aka bishi gonar ba a sameshi ba sai garmar tashi aka gani a ajiye a kan daukota aka dawo da ita gidan tund aga ranar babu wanda ya sake sa Bukar a idonshi sai ko wannan ganin da dan uwanshi yaje ya yi mishi.

Sunyi nema sun yi nema har suka gaji ‘yan kwanaki kadan da tafiyar tashi sai ya baiyana kowa ya gane ba shi ne mai yin dauke dauken nan ba dan kanin baban nasu ne da suke kai daya da shi don ko da ya bar gidan ba a daina ba banda haka ma sai kawai aka kama shi da akuyar mutane ya yanka ta ya durata a buhu, hankalin babban nasa bai yi mummunar tashi ba sai da ya ga damuna tazo ya rasa mai nome mishi gonarshi ga kuma dan nashi da surkayen nashi suna kallo lokacin ne ya yi nadama mai tsanani ya yi kuka har ya gaji ya nemi Bukar har ya zama abin tausayi a kan neman nashi ko zuwa akayi aka bashi labarin cewar anga wani mai kama da shi a wuri kaza saiya debo kudin mota ya ce a tafi a gani ko shi ne sai aje a dawo a ce mishi ba shi bane, sula yi nema har suka debe tsammani, suka hakura sai a ‘yan shekarun nan da yan uwan Malam suka yi ta rasuwa sai hankalinshi ya sake tashi ya sake yin niyayr zai sake neman Bukar ko zaiyi dace in har yana raye su ga juna kafin rai ya yi halinsa.

Shekaru biyar kenan yanzu tunda ya koma bai da wani aiki sai na rokon Ubangiji ya sadashi da dan uwanshi in har yana raye in kuwa baya raye to ya nuna mishi wata alama da zai gane hakan don ya samu natsuwar da zai hakura to a cikin hakan ne ya samu labarin anga wani mai kama da shi a can kasar kudu ya shirya ya tafi ya yi iyakar neman da zai yi har ya gaji ya dawo bai sameshi ba wannan fitar da ya yi dai na wannan karon shi ne fita ta uku ko hudu da ya yi sai kuma gashi ya dawo cikin nasara.

Cikin natsuwa nace mata, shi kanin baban nasu ya dade da rasuwar ne Ya Kabidi? Bana shekararshi tara

kenan, cikin shekaru taran nan kuwa ba karamin zuba akayi ba a gidan kin ga wancan dakin da wanene da

wance a ciki wannan ma da su wanene in takaice miki dai a yanzu daga babanki ne sai dan uwanshi goni su ne manya a gidan shi kuwa goni shi ne dan karami baban nasu kanin wancan da suka taso tare da Bukar.

Tausayin al’amarin ya kamani can cikin zuciyata na yi tunanin duk yanda abu ya kai da zai tsakaninka da dan uwanka to yafiya ituce maganin al’amarin tunda in ma baka yi hakan ba watarana sai a wayi agri ba wani a cikinku, sannu a hankali kuma sai dukkan ku ma ku kai ga karewa.

Babana dangi ne da shi masu yawa ku san kullum sai baba Abba Gana ya bada umarnin a kaini wajen wasu da ya dace su ganni duk da na gane abu mai zati aka yiwa babana wanda ya yi dalilin barinshi gida babu ma dai irin satar da aka dala mishi don kuws na sah jm manya su na  fadin wai ita satar dan halal ma baya yinta to amma duk da baka sai na rinka ganin tamkar da bai yi fushi mai tsanani ba haka da yayi ya tafin ya samu kamar wasu shekaru da basu tsananta ba da sai ya waiwayi dangi musamman ma da yake a can in da ya tafin shima ya samu rubonshi na aure.

Baba Goni shima mutumin kirk ne amma da ganin tsarin zarman nasa da baba Abba Gana kasan ba karanmin hakuri yakeyi da shi ba. Wata irin kulawa baba Abba yake yi min amman duk da haka bai hana sanda na kwana bakwai a gari naji hankalina ya kona gida ba kewar mutacn da us baro ta fara damuna babana, yaya Dija da iyalanta sannn ahankali sai naji shima Mubarak ina son ganinshi ban kuma ji hankalina ya tashi na gane har a vanzu da kulım nake kin auren Mubarak ba kararmin son shi nake yi ba.

Don kuwa a ranar da na ji kishin kishin wurin Yatakabudi cewar baba Abba Gana ya ce ba zai sake barina in koma gida ba zai rike ni ne kawai ya aurar da ni a nan don da hakan ne kawai yake ganin zai karfafa zumunci tsakaninmu da yan uwanmu da mu da su ba wan shakuwa muka yi ba tunda in ya aurar da ni a nan to ko su basu raye zumunci zai dore a tsakaninsu yaya Dija zasu rinka zuwa ko ba don kowa ba don ni su ma nasu ya’yan tunda gani a cikinsu zasu kula da zumuncin dake tsakaninmu da su yaya Dija.

Kasa bacci nayi kwana nayi rannan ina tunanin duk da tunanin nashi tunari ne mai kyau ama anya zan iya zama da wani mijin kuwa matukar ba Mubarak ba ne? Duk wani mutumin da ya taba zuwa wurina kan maganar aurena na amince wani dalili yana hana auren nake mancewa da shi inji garama da ba a yi auren ba ya fiye min in gamu da shima ban yi komai ba saboda bani da wata danuwa game al’amarin shi amma banda Mubarak.

Mubarak ne mutum daya da zuciyata ta kasa daina kishinshi na kasa daina jin zafinshi na kasa fita cikin harkokinshi in daina son jin abinda yake ciki, na kan dai daure in kawar da kai game da shi har in bude baki ince mishi ya fita harkata amma a zahiri ne kawai hakan yake faruwa yana gwada zai fita harkar tawa sai inji nayi matukar takura, dan sa’an da nayi ma shi ne shi din ba wani jarumi bane kan lamarin fita harkar tawa da ban san yanda na rinka ji ba a raina.

Kwana biyu bayan maganar da Yakabudi tayi min naje dakin baba Abba Gana da safe don gaisheshi kamar yanda da ma kullum nake yi tun zuwana gidan sai ya zaunar da ni yana yi min bayani game da muhimnmancin yin auren zumunci a wurina ga dan uwanki nan da na yiwa Bukar takwara da shi don shi ne dan da Kabudi ta fara haifa bayan barin shi gidan sai in hadaki da shi dan uwanki ne amma ba zan yi hakan ba sai na baiwa mutumin da aka gaya min cewar yana sonki lokaci na kwanaki ashirin da biyu in har ya biyoki kafin cikar wadannan kwanakin to shi kenan ke din rabon shi ce, in kuwa bai zo ba sai bayan cikarsu ko da da karin kwana biyu ne to ba zai saurareshi ba.

Hankalina a kwance na ce mishi to baba saboda ni da kaina na gamsu da adalcin da ya yi na bada wa’adin kwanaki ashirin da daya duk da dai a lokacin ina da waje kwanaki tare ne a gidan ‘yan uwan babana sun nuna min gata na zumunci sun martaba zamaa a cikinsu sun kamama bakuntata irin karramawar da har na rinka yin mamaki sai dai duk da haka zuciyata tafi son in koma gida kusa da babana da yar uwata yaya Dija da iyalinta in so kuma shi ne samu to zanso ace na wayi gari a gidan Mubarak a matsayin ni din matrshi don haka sai nayi ta addu’a ya iso Gaidan kafin cilar kwanakin da baba Abba Gana ya dibar mishi na kwanaki ashirin da daya.

<< Halin Rayuwa 49Halin Rayuwa 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×