Ranar da na cika kwana goma sha hudu wato sati biyu cif da zuwa garin Gaidan sai ga Mubarak ya iso babu wanda ya yi zaton ganinshi a lokacin har nima farin ciki irin wanda nayi bai raisaltuwa sai dai ban bari an gane ba.
Su biyu ne suka zo abinda naji ana gayawa Yakabudi kenan sai nayi zaton ko shi da Amiru ne, sai da na shigga dakin da aka saukesu na gansu eai naga ashe ba Amiru bane, ran amarya ya dade, inji abokin nashi.
Mubarak ya harareshi, kai nan har wani kulata zakayi? Ya yi dariya to ba zan kulata ba me ya kawoni?
lta amaryar ma ance maka ta na yin laifi ne? To ai shi kenan tunda a wurinku ba ta yin laifi.
Na gaida abokin nashi cikin mutunci da girmamawa a hankali Mubarak ya tambayeni, kin ganeshi kuwa? Na gyada kai muna alamar eh, ya sake kallona a ina kika sanshi da kikace kin ganeshi, na yi murmushi kawai nayi shiru, gayamin sunanshi in har kin gane shin da gaske, ban fadi sunan ba saboda in girmamashi sai na ce mishi na taba ganinku tare da sallah ka ce min daga Kaduna yake.
Ya yi murmshi ya ce, a to ai tace maka ta ganeni kai kafi so sai ta ambeci sunana gatsal ita kuma mai kunya ce, to ni shikenan yi ta zugata.
Na matsa kusa da kwanukan abincin da na samu an kai musu na soma budewa yallabai ai baku ci abincin ba, bai kalleni ba ya ce, to abinci muka zo ci sunje sun dauko min mata ba da sanina ba sun kawo min ita nan ni banyi musu muzurai kan abin da suka yi min ba sai su ne kuma wai za su yi min? Cikin natsuwa na ce mishi, to kayi hakuri si kasan iyaye ne.
A hankaii ya dago ya kalleni har da shi ma wannan gorin a cilkin iyayen ya kare? Jin yanda yayi maganar a kanshi ya sani yin maza na ce msihi, shima fa kanin babana ne. Ya yi kamar bai sani ba, au haba? Ai na dauka shima yana cikin maneman naki ne? Abdulhamid ya yi murmushi tare da fadin, kai kam Ahamad Ubangiji ya shiryeka surikin naka kake cewa yama cilkin manema.
Mubarak ya murtuke fuska ya ce, to menene don ya nema ba ‘ya’ya maza suke da Babanta ba ta haramta ne a wajenshi? Ai ni wannan mutumin ban yarda da shi ba, don bai yi min kama da wanda zan yi surkuta da shi ba baka ga ko kadan bai yi murnar zuwan namu ba? Na kau da kai daga zancen nashi saboda ganewar da nayi bai san komai maganganunshi ne dai kawai na zato da kishi da ya saba da su na soma zuba abincin da aka kawo musun na mika mishi ya karba ya ajiye a gaban Abdulhamid kafin ya sake karbar wanda na sake zubawa ya ajiye a gabanshi.
Suna gama cina bincin Abdulhamid ya mike, kai nifa zan sha iska a waje daga nan inga yanayin wurin, bai jira amsar da Mubarak din zai bashi ba ya ficewarshi. Cikin nutsuwa na kalli Mubarak na ce mishi, ashe ka dawo? Ya ji dadin irin karbar da nayi musu da watakila bai zaci hakan don haka cikin murmushi ya ce min, na dawo na zo ban sameki ba na ce darma ana yin haka n mace tayi tafiya mai tsawo irin wannan babu izinin mijinta ba a gaya musu an riga an bani ke ba ne? Gashi anzo suna cewa wai ba za ki bini ba ni kuna na zo ne da niyyar tafiya da ke ban gane abinda suke ba fa ko kin san da wani abu ne? Na ce mishi a’a sai dai a’a da nace bai hanani gaya mishi bayanin da Baba Abba Goni ya yi min na ce to amma ai kazo kafin cikar lokacin da ya diban.
Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, ke dai kawai ki danyi gaban ki jiramu a kan hanyar can ta shigowa unguwar in muka fito sai kawai mu daukeki mu yi tatiyarmu don in ba haka ina ganin wadannan ba rabuwa da su lafiya zan yi ba.
Na yi murmushi na ce, haba yallabai ranka ya dade ai kaima ba zaka so in yi irin wannan sallamar da su ba in ka bisu a hankali sai ku daidaita shi baba Abba Gana ai al’amuranshi masu sauki ne gashi kuma mutumin kirki ne sosai. Hira sosai mukayi da Mubarak irin wanda ko da bamu taba yin irinshi ba ko kuma mun dade har na mance rabon da mu yi irinshi, nayi mishi kalamai masu saka ya samu natsuwaa tare da shi.
In dai sake komawa wuinshi kenan da maganar? Nace mishi eh, to babu laifi bari in kira Abdulhamid muje inda tuntuni haka kikeyi min Mero ai da babu dalilin da zaisa in yi ta sakin baki ina daddankara miki bakaken maganganu, to in nazo da damuwa sai kice sai kin karamin to in ban gaya miki bakin ki ji kema inda dadi ba yaya zanyi? Ban tanka mishi ba na wuce na tafi don su samu damar sake ganin baba Abba Gana.
Sai bayan sallar la’asar ya sake aikowa a kirani a jikin motar da suka zo a ciki na sameshi, to mun daidaita da su Maryam duk da dai ba haka naso ba to amma tunda mun ajiye matsayar da muka yarda da ita shi kenan magana ta kare, ya ce a nan zan yi daurin aure a nan zai yi biki saboda ba zai yiwu a ce za a dibi jama’a a je can ba lokacin biki kuma da kyar ya yarda da kwanaki talatin da biyar nan gaba sati biyar kenan sannan wai a nan za a bariki. Na ce to ai kamar yanzu ne sai kaga lokacin yazo, ya ce to yi min wata magana komai kankantarta da zai sa in ji damuwar da ke zuciyata tayi min sauki don bana son tafiyar da zanyi in barki.
Cikin natsuwa na sunkuyar da kaina kasa don in tabbatar bai tafi da wata damuwa ba sai na ce mishi, ai ko ka tafi ka barni a nan din ba wani abu bane babu wani abin da zai faru a bayan naka sai alheri, ya ce to babu laifi.
Sai bayan tafiyar su Mubarak din ne na gane banda dinbin tsarabar da ya kawo musu har da kyautar manyan kudi ya yi musu ga kuma lissafe-lissafen da Yakabudi tayi mishi nasu a wurinsu ana bada kudin yin lalle da kuma na turare ya tambayi yawan su ta fada, suma ya bayar.
Sallama mukayi da Mubarak ba tare da ya gaya min cewar zai dawo ba amma sati biya bayan tafiyar tasu sai gashi ya zo shi da Amiru wani sati biyun ma, bayan nan ya sake dawowa a lokacin nan kuwa baifi kwanaki biyar sulkz saura a fara bikin ba.
A ciki wadannan kwanakin kuwa babu abin da Yakubudi bata yi min ba wanda suke yi wa amarensu ko da yake ma kamar karasawa ne don tafi kwanaki talatin tana min jike-jike, hayake-hayake, tsime-tsimw, goge-goge, gyare gyare, kullum kuma ta kan yi ne tare da yi min bayami wannan uban zirga-zirga da wannan yaro yake yi ai gara a kara gyara mishi ke ya sameki..Kin san ance wai ko kana da kyau to ka kara da wanka kar ki yarda ki zauna bakya gyaran jikinki don shi namiji da kike kallonshi…. Ta danyi shiru kadan kafin ta ce, uhuyy ke yanzu yarinya ce ba za ki gane yadda alamarin yake ba tukunna.
Ana cikin haka kwanakin biki suka iso jama’a suka yi ta haduwa fiye da duk yanda ake ko daga gida mutanan da sulka zo bikin ko kadan banyi zaton ganinsu ba, Umman Mubarak, Yakumbo Halima, baba Sumaye, baba Lami, manyan dattawa, sannan yan matasa yaran mata kuwa akwai anti Asiya aminiyar yaya Dija da malamata malama Basma akwai yar anti Safara, ga wasu mata su uku da suka gabatar min da kansu a matsayinsu na angwaye alamar ko dai kanne ko kuma abokan wasan Mubarak sai dai ban san ta ina ba maza kam babu adadi don kuwa naji ana ta maganar yawan masu abokan Mubarak da yawa sun zo daurin auren ga samarin unguwa irinsu, Isiyaku su ma ba a barsu a baya ba don kuwa shi mai mu’amala da na kasa da shi ne abokan babana irinsu baba Baidu da baba Hodijo kasuwar timatir su ma ance mota guda suka zo abin dai gwanin dadi gwanin sha’awa.
Ina kwance a dakin da nake zaman lalle ina lullube da kaina na ji an shigo an zo an durkusa a jikina a hankali na bude ido don ganin waye hakan? Inna na gani da sauri na saki wani lallausan murmushi yaya Dija ta zo ne? Ta ce a’a babanmu ne ya zo da mu ni da Abba, sannunku da zuwa na mike na zauna ina nuna mata kwanukan da na san akwai abinci a ciki don taci tagir giza kai nuna alamar ta koshi.
Biki Baba Abba Gana ya yi irin wanda yake yiwa ya’yan da ya haifa a cikin shi koma ince fiye da haka dan kuwa yayi hidima ya ciyar da jama’a abin ba a magana, bayan nan kowa daga jama’a ne aka yi daurin auren bai yarda an dauki amarya kamar yanda abokan Mubarak suka so su yi ba sai ya ce tafiyar tayi nisa baza a dibi mutane masu yawaa yi irin wanan tafiyar da su ba a cikin dare.
Don haka aka bari sai washegari a wannan lokacin ango baya zuwa wurin daurin aurenshi don haka Mubarak bai zo Gaidan ba yana Kaduna wurin harkokinshi.
Washegari ana gama karyawa aka yi ta shiri ana fita don shiga motocinda zasu dibi jama’a ganin da Baba Abba yayi kaiyade masu zuwan zai iya kawo bacin rai yasa shi yin shiru yace su angwayen su debi adadin abinda suka ga zasu iya diba su kuwa su Amiru da Abdulhamid suka ce duk wacce take son tafiya kawai ta fito, mata kuwa sukace me za su yi ba tafiyar ba.
An fito da ni aka kaini wurin Abba Gana a lokacin nan kuwa yana tare da dan uwanshi Baba Goni alamar da tafiya ta zo ke nan kuka nakeyi sosai daga kuma cikin zuciyata kukan ke fitowa saboda tausayin abubuwa a yanzu kuma sa naga zaa tafi sai naji bana son tafiyar cikin dangin ubana.
Yakumbo Halima ta shigo dakin ga alama kuma kiranta akayi suka gaisa da baba Abba a cikin yanayi na mutunci da girmamawa, kece uwartasu? Tace eh Mallam suka dan yi hira kadan a cikin hirar tasu ta sake jaddada mishi ita da inna mu uwa da uba daya suke ita ta sha nono ta bar mata, to Ubangiji ya jikansu da Rahamarsa in tamu tazo kuma yasa mu cika da imani aka amsa amin amin, to mun gode fa mun gode mun gode yayi ta nanata godiyar tamkar dai wani abin akayi mishi sai da suka soma yi mishi sallama zasu tafi sai ya ce, to ungo ana Kabudi mika musu wannan sadakin da uban mijinta ya zo dashi ne wannan kuwa ni na bayar in kunje ku sai mata abinda kuka ga ya dace Yakumbo tasa hannu biyu ta karba tare sa yi mishi godiya me yawa.
Motar amarya itace motar da ta tashi a karshe kenan duk sauran motocin sunyi gaba kafin ita daga ni sai Yakabudi ne kuma a bayan motar ya yi da Amini da wani wanda ban sani ba suke gaba.
Kafceciyar wayar cellular da ke hannun Amiru tayi kara ya dauka tare da amsawa, ran ango ya dade ban ji abinda Mubarak ke gaya mishi ba na dai ji shi Amirun na ce mishi, gabadaya jama’a dai sun taso suna kan hanya amma mu gamu nan a kofar gida ba ma taso ba saboda shi wannan Baban na ta da kake bani labari ya ki bada ita.
Mutumin dake tukin ya yi murmushi, kai Alhaji Amiru kar ka se ango ya shide kai in banda Alhaji Adbulhamid ya dage ai da cewa ya yi wai shi ma zai biyo mu in yaso ko a Goabe ya tsaya shi nc ya ce sai daiya taho mu mu zauna.
Kai dai muna hanya amma mu biyo bayansu ne, ban san abinda yace ba naji Amirun ya sake ce mishi to amin.