Ina jin Babana yana gaya mata cewa in ban da kananan ‘ya’ yannan da a ka ambata ba zai yi ba, don mata ba wani kirki ne da su ba, suna samun kan namiji to su kuma sai rashin imaninsu ya tashi.
Delu ta ce ina za a yi haka Mallam ita da take neman yanda za a yi ta zauna a kan ‘ya’yanta? To a dai gaya mata in ta samu yadda take so ban yarda ta zalunce shi ba, in kuwa tayi haka ita da Ubangiji da sauri ta ce zan gaya mata Mallam, ai don ma ba ka santa ba ne.
A kan idona Babana ya rinka yin rubutu a jikin allon karfen shi yana wankewa sai a bayan idonshi in ga Babah Lantana ta kafa kai ta kwankwade shi tas.
Ni ina kallo ko Yaya Dijah ban taba gayawa ba, balle wani can daban saboda kullum naje gidanta ta ganni sai tayi kuka ‘yar magana ba mai tsanani ba in na gaya mata itama tayi ta kuka don haka na koyi kame bakina.
Ban kuma tabbatar jagwalgwalo da aikin da yake yi wa kanshi ya kama shi ba sai a ranar da nake sharar tsakar gida da safe yayin da shi kuma yake cikin dakin a kwance a kan gado.
Naga an yiwo fito da wani hoto babba waje, gilas dinshi ya tarwatse.
Da sauri na nufi inda hoton ya fadi cikin tsananin tsoro da fargabar kar abinda nake zaton ya tabbata, ina daga hoton gabana ya fadi, jikina ya dauki rawa ‘shi ne hoton Innata da zamanshi a dakin ya dade yana tukurawa rayuwar Babah Lantana bata samu yancin yin yanda take so da shi ba, sai yau.
Ina cikin tunanin Baba bai san ta cire mishi hoton shi ba sai na jiwo ta tana ce mishi ni fa na cire wannan jarababben hotonn da a ka kakaba min a daki.
Shekara da shekaru tana can a kwance har kashinta yayi fari amma ka ajiyewa mutane ita a wuri tana nema ta rinka yi musu fatalwa, wannan in banda ni din ni ce ai da bata bar ni na zauna a dakin ba, to kullum na hada ido da ita sai na zare mata nawa nima in kuma ce mata kurwata kur taci kanta tasha bakinruwa.
Ban ji ya ce mata komai ba, to balle kuma ni na dai sunkuya kawai na dauke hoton na kuma tsince gilasan da suka fashen har suma ban zubar ba, kulle su nayi a wani tsumma naje na adana su a cikin kayana na zauna nayi kuka sai da na gaji na share hawaye.
Tunda Babah Lantana ta samo kan Babana ta kara bayyanar da kiyayyar da ke tsakaninta da Babah Sumaye da mijinta, tun farkon zuwanta dai dama bata yarda tayi wata mu’amallah da su ba, sannan duk wani lokacin da wata magana ta taso da ta shafe su za ki ji tana yawan aibanta su ko ta kira kirkinsu da Babana ke fadi da kirkin munafukai.
Nan take kuma ta shiga rattabo mishi aibobinsu, a yanzu ta kaima ta raba Babana da Baba Baidu cin abincin da suke yi da daddare ban dai san yanda a ka yi ba gani kawai nayi sun daina. A bakin Babah Sumaye kuma naji tana ta fadin, ai mace shu’uma ce in ka gamu da ja’ ira tosai dai addu’a kawai, amma in ba haka ba yaushe? Yaushe za a zaci za a yi haka?
A wannan lokacin ta kai ma ko makarantata ta boko bana samun zuwa a kan lokaci, karatuna na Alkur’ani kuwa tuni tasa kafa ta shure shi ko a gida ta ganni ina karatun Alkur’ani zata shiga zage-zage tana fadin ai Ubangiji ya riga yayı magana a kan irinku masu yi don ace su ya tashi ni ki bani wuri, munafuka kawai.
Ni da na rayu da Innata ina wanka safe da yamma har bayan ta ma a haka nake ina tashi nayi ayyukana na safe zan yi wanka kafin in tafi makaranta in na gama komai zan kwanta ma zan sake yi kafin zuwan Babah Lantana gidanmu na dauka ka’idar rayuwa ne yin hakan.
A yanzu duk na daina saboda babu halin ta ganni nayi wanka ko zan yi sai ta ce wai kishi da ita nake yi ranan har tana zaunar da ni tana yi min bayanin da ki ke ganina ina wanka safe da yamma ba ra’ayina ba ne yin hakan fitinar ubanki ce ta kan sa ni, in ban da haka babu abin da zai sa in yi ta jika jikina da da ki ke kwaikwayona ke a wane dalili ki ke yin naki?
Irin wadannan kalaman nata suka sanya ni na zamo sai in yi kwana uku hudu ban yi wanka ba, balle ayi maganar wanki ga shi a yanzu tsanin da ke tsakanin gidanmu da na su Babah Sumaye ya rikida ya zama wari tunda takai ma har Babana ya kafa min dokar shiga gidan.
A wannan lokacin kuncin da nake ciki ya kai in da yakai kusan kowane lokaci a cikin yunwa nake yawo ga kazantar jiki da na kaya gaba daya na hade na zama babu kyan gani.
Tuni Asabe ta dawo gidanmu a zama, sai dai ta dawo ne a matsayin ‘yar da Yayarta ta rasu ta bari ba a matsayin ita ta haifeta ba ni da Asabe kai daya muke a tsawo sai dai ta dan fi ni kauri kadan saboda ta girme ni idonta a bude yake kwarai saboda za ka ji manya-manyan maganganu a bakinta.
A wancan lokacin da ban san komai ba game da al’ada saboda kuruciyata ita bata jin kunyarta a wurinta na fara ganin ta saboda bata damu da kintsa kanta tayi ta gama wani na kusa da ita bai sani ba.
Tunda Asabe ta dawo gidanmu da zama al’amura suka kara tsananta a gare ni dakina da da nake yawan zama a cikinshi saboda kuntatar da nake yi a tsakar gidan yanzu ba ni da halin yin hakan in ji dadi saboda ni da ita ne a ciki, gadonmu ma daya dan kankanin motsi zan yi ta rufe ni da duka babu mai cewa ya isa balle aje ga tambayar dalilin dukan.
Ni kuwa a kwance muke a gado da daddare to matse ni take yi a jikin bango da kuma zan ji tsananin yakai tsanani in dan yi motsi sai kawai tayi min gula da gwiwar hannunta. In nayi kuka Babah Lantana ta fito ta kare min tanadi tana fadin ai duk bakin cikinki ba ki isa ki kori Asabe daga gidannan ba ina zamnan ubanki ne, ita kuma tana zamana yauwa in takamar ki maraici itanma marainiyar ce ta uwa da uba, bata da kowa sai ni din nan da ki ke gani.
Don haka babu in da zata yauwa yarinya ‘yar kankanuwa da ke sai bakin cikin tsiya tunda Asabe ta dawo gidannan ki ka dauki karan tsana ki ka dora mata me ta tsare miki ne haka?
Duk abinda ke faruwa kuma Babana yana ji amma sai ayi a gama bai ce komai ba, kamar baya nan a gidan.
Tunda Asabe ta dawo gidanmu Delu ta rage zirga-zirgan karbowa Baba Salamatu abubuwanta, sai Asaben ce mai karbowa kusan kullum sai ka ji ta karbo mata wani lakanin asirin saboda duk samun Babana da tayi bai ishe ta ba tana neman kari.
Rannan ina daga dakina a zaune ina hangen su Babah Lantana ce ta kama wani kifi mai rai ta shake shi, yayin da Asabe ke rike da wata ‘yar kankanuwar làya da taje ta karbo mata a hannu.
Yana bude baki sai kiyi maza ki jefa layar a ciki in ji Babah Lantana Asabe ta amsa da to.
Hakan kuwa a ka yi ta wahala tana isan kifin nan ya hangame bakinshi Asabe tayi maza ta jefa laya a ciki nan take kuma suka yi maza suka kama bakin nashi suka matse suka sa zaren lilo suka daure tamau. To dauki maza tun bai mutu ba kije da sauri ki jefa shi a cikin rafin nan na kasan layi yan uwanshi su cinye shi a haka.
Da sauri Asabe ta ce mata to, ta kuma suri ledan da suka jefa kifin tayi waje da shi don kai wa rafin da ta gaya mata.
A yanzu ta kai a ko a waje naga Babana ko na same shi a wajen tumatirinshi ba ya iya sake jiki yayi magana da ni balle yayi min wani taimako, don haka nima sai ban cika zuwa in da yake din ba.
Don haka a yanzu sai na zama kan dakalin gidanmu ne wurin zamana ko kuwa in yi zamana a cikin zauren gidanmu kan tsohuwar tabarmar Innata da nake shimfidawa.
Rannan na samu naje Makaranta daga can na saci jiki na wuce gidan Yaya Dijah a dalilin itama a yanzu bana tambayar zuwa gidanta a kyale ni saboda wai ita ce take kara koya min iya shegen da nake yi.
Ina zaune a dakin nata ina cin abincin da naje na debo a kicin dinta yayin da ita kuma take share hawayen da ke zuba a idonta a dalilin zancen da take yi min ashe abin da matar nan tayi wa Yakunbo Halima ke nan da taje gidanmu kan maganarkı?
Shiru nayi ban amsa ba, sai taci gaba da magana cikin tsananin kaduwa da mamaki tamfar a lokacin ta fara jin zancen, wai ta kawowa Yakunbo Halima diga da cebur ta ce mata taje kawai ta tono Innarmu a inda a ka binneta tazo ta rike ki tunda nata rikon bai yi ba an raina?
Na ce Eh nayi shiru ta gyada kai to babu damuwa ba zamu je mu tono ta ba amma kowa zai tafi inda taje din lokaci ne kawai wata rana kuma sai labari Baba ya bada ke ya ki? Ya hana ni ke ya hana su Yakunbo amma ya kasa hana wulakancin da a ke yi mana a kanki na kullum mutum ya ganki sai yayi kukan bakin ciki.
Ta dan yi shiru kafin zuwa can ta sake cewa ko da yake dai shima ba jin dadin zaman nan nasu yake yi ba, yana dai yin shiru ne kawai tunda gaba daya ya zube Baba mai tsabta amma duk ya zama wani iri ta soma kuka sosai.
Na mike na ce mata zan tafi, tayi maza ta bar kukan da take yi ta koma tambayata tun yanzu? Ki tsaya mana in taya ki tsifan kanki ayi miki kitso. Na.ce a’a in nayi kitso zata gane na biyo ta gidannan ta gayawa Baba.
Da sauri Yaya Dijah ta zaro ido tana kallona Baban ya hana ki zuwa wurina ne? Na yi maza na ce mata a’a amma ai ban ce mishi zan zo ba daga Makaranta ne kawai na biyo, da wannan bayanin ne ta dan samu natsuwar zuciyarta ta tashi taje ta kawo kudi ta bani nasa hannu na karba na juya zan tafi tana bina tana yi min magana ki adana su kina kashewa a hankali kar kuma ki rinka zama da datti, gobe gari yana wayewa ki tsefe kanki kije kiyi kitso na ce mata to na wuče na tafi.
A farkon zuwan Asabe gidanmu na sha ganin Babah Lantana tana feshe mata kanta da sheltox din da Babana ke kawowa gida saboda kashe sauraye da sauran kwari saboda kwarkwatar da take fama da su amma daga baya da suka yi sa’a tata kwarkwatar ta mutu saura kuma suka dawo kaina sai Asabe ta ce wai ba za ta rinka kwanciya da ni a gado daya ba don kar in Sanya mata kwarkwatata a kanta.
Babah Lantana ta ce kwarai kuwa ina ma ake haka me kwarkwata da mara ita su hau gado daya su kwanta? Don haka ta bani zabi tsakanin abu biyu ko dai in tsaya ta aske min gashin kaina tayi min malu saboda kwarkwatar da ke kan nawa tayi yawa ba zai yiwu a tsaya yin wahalar taba ko kuma in dawo kasa in rinka yin shimfida ina kwanciya.
Ita Asabe tana kwana a gado duk da ban bude bakina nayi zabin ba hukuncin da Babah Lantana ta zartar min ke nan dawo da ni kwanciyar kasa kan wata tsohuwar tabarma saboda na ki yarda in tsaya ta mayar min da kaina tal kwabo.
A wannan lokacin ko da gaske Babana ya daina Sona ne kamar yanda masu yaran suke gaya min? ko kuma a’a masifar da take balbale shi ta ita ne baya so yasa duk abinda zata yi yake zuba mata ido ban sani ba, duk abinda take yi bai cewa komai hakan kuma bai sa ya tsira daga masifar tata ta bar shi ya zauna lafiya ba.
Ko cinikinshi ya kawo mata kamar yanda ya saba in har bai kawo da yawa ba sai tayi mishi fada gashi babu halin ya ce mata a cikin kudin nan ayi abu kaza, sai ta ce a wane kudin? A irin hidimar gidan nan ne wani abu zai rinka raguwa a wadannan ‘yan kudin da ka ke kawowan.
Kullum sai ta tasa shi a gaba ya bata kudin cefane daga kudin aljihunshi amma kuma bata yin girkin kullum in tayi miya guda daya to bata sakewa ko da kuwa bata yi dadi ba sannan ko zata kwana uku to sai ta kare kafin a sake wata.
A wannan lokacin ne na samu kaina cikih wani irin hali da ya tabbatar min da maraicin uwata da nake ciki na rasa Inna na rasata kuma irin rashin da na kara ganewa cewa rashi ne na har abada bani kuma da mai yi min maganin halin da na samu kaina a ciki a dalilin rasatan da nayi.
Kullum dai Yaya Dijah da su Yakunbo Halima suna yawan gaya min cewar wata rana zai wuce sai dai in bada labari to amma yaushe ne wataranan zai zo? Wannan ita ce tambayar da kullum ta ke tsayawa a raina don gani nake kamar ba zai kare ba tunda kullum abin nata karuwa yake yi.
Ina makale a zauren gidanmu kuka nake yi saboda bakin cikin kalamin satan da Babah Lantana tayi wai ni na shiga dakinta na diban mata kudinta saboda kawai tayi min bincike cikin kayana taga kudina da nake boyewa ina tsakura a hankali ta kwashe wai nata ne alhalin Yaya Dijah da ‘yan uwan Innata ke ba ni.
Don haka wai in fito mata da duk sauran kudin nata ma da bata gani ba, bayan kuma ni ko shiga dakinta bana yi ta kuma san hakan.
Asabe tazo zata wuce ni da kwano a hannunta a rufe nayi zaton ai kanta a ka yi tana isowa inda nake sai kawai naga ta saki kwanon a kasa tayi maza ta kama ni tana fadin gata Babah ga ta nan na kama miki ita.
Sai kawai naga Babah Lantana ta shigo zauren ashe damà tana makale a kusa, hannu ta saka ta kama ni ta rike wani irin riko mai tsanani, ta shiga jana zuwa cikin gida ni kuma ina ta ihu saboda sanin da nayi cewar zan sha wahala ko daga jin irin kamun da tayi min.