KADUNA
Rafin guza sai da aka fito daga masallaci kafin Lateefah ta tanbayi wani inane gidan su Namsiyya take ya nuna mata saboda sunan ba wani boyayye bane saboda shurar da tayi wajen son ƙarya da rayuwar hutu kuma daɗin daɗawa ita kaɗaice mai suna Namsiyya kaf faɗin unguwar, ɗaure fuska Lateefah ta ƙarayi lokacin da ta isa ƙofar gidan don rashin mutunci zatai masu da ruwa ruwansa sai taja masu kunne ta yadda zasu dinga shakkarta har suji tsoron ganinta, rashin mutunci ta zo da niyyar yimasu irin rashin mutuncin da ko sunan ta sukaji sai sun razana, sai. . .