Take tai tsuru tsuru kafin taji duk ta muzanta saboda tsawar da yayi mata tasa hankalin mutane da yawa ya dawo kansu,
“Ke wace irin wawuya ce da zaki zo inda ba a gayyatokiba ko baki son turakar waye ba da zaki kwaso wani tsumman jikinki kina tsami ki zo kice zaki zauna sai kin mana asarar wannan damar da muka dade muna nema kafin musamu to middin ya daina zuwa nan sai na kulle ki wawuya ƙazama maza ki barnan tun kafin nasa a fitar da ke ” cewar manager wajan wacce macece
“ wai akan wannan sakaran kuke neman wulaƙantani. . .