Yau ma Maman Khalil ba ta yi min sallama ba ta wuce wurin aiki.
Na rika hasashen tana jin irin zafin da nake ji ne, ko kuma dai ta yi latti, zan jira ta dawo domin tantance zargina.
Mu ka sha baccinmu da Ramla, sai 12pm na shiga kitchen, jalouf din taliya na yi mana da ta ji busasshen kifi da ganyen ogu, Ramla na fara sanya ma wa, kafin na watsa ruwa hade da yin alwalar sallar azhur.
Bayan na idar doguwar riga mara nauyi armless na sanya, kafin na zuba abinci ni ma. Cike da jin dadi nake. . .