Skip to content
Part 14 of 27 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ramla kwance a kan cinyata ina shafa kanta don ta yi barci a lokacin da ya shigo dakin.

“Sannu uwar hudu. Wai don Allah duk iskar fankar nan ta miki kadan sai kin hada da mahuci?”

Cikin yanayin mamaki ya yi tambayar.

Dariya na yi kafin in yi masa hararar wasa “Wai saboda tsaro, ka ga ko an dauke wuta ba zan sha wahalar tashi zuwa neman mahuci ba ga shi a kusa da ni.”

“Anya masu scanning din nan kuwa suna gani me kyau? Gaskiya cikin nan naki ba yaro daya ba ne.”

Dariya na kuma yi hade da shafa cikin “To ai dai scanning din nan ba sau daya mu ka yi ba. Kuma dai duk abu daya yake bayarwa.”

“To gaskiya kina da girman ciki, sai ka ce za ki haihu yanzu, ko Maman Khalil ma mamakin girman cikinki take yi. A tarihi dai ke ce mace ta farko da cikin farinta ya yi girma kamar daro”

Mahucin kusa da ni na dauka tare da kai masa jifa.

Ya yi saurin kaucewa yana dariya

“Abun da za ka fada kenan ko?” Na karashe maganar ina harararsa.

Kafin ya yi magana na dora

“Kuma fa ina jin nauyinsa sosai, kai ne ma ka ki barina in je gida ka ga dana huta da wasu hidimomin, tun da na yi aure  ma fa zuwana daya, su kuma sun ki su zo mun.” Cikin yanayin shagwaba na yi maganar.

“Da wannan cikin za ki gidan, kuma duka watanki nawa da auran? Sau nawa kike so ki je gidan a shekara?”

“Ni ban ki ba ma kullum in je”

Dariya ya yi sosai, kafin ya ce “Ina jin yunwa ina son yin wanka wanne zan fara ne?”

“Ka ci abincin sai ka yi wankan idan ka dan huta”

“An gama” ya fada hade da cire rigarsa

“Yaushe rabon da ki cire min kaya ma wai?”

Dariya na yi mai sauti kafin in ce “Ko jiya na cire ma fa, yau kuma gaskiya na ji dadin zama ba zan iya tashi ba.”

“Ko kuma don yarki na kan cinyarki ba.” ya yi maganar cikin tabe baki, lokacin daya kuma ya zauna hade da bude flask din abincin

Sababben ne dai, wato tuwo, amma yau miyar ganye na mishi, kuma sosai ya ji dadin abincin saboda yadda yake cinsa hankali kwance.

Kodayake shi dai indai abinci na gargajiya ne zai ci shi sosai, kwaben zamani ne bai so.

“Ka gama don Allah mu je chemist din Bilya, yarinyata jikinta ba dadi”

“Ke ma kin zama Sakeena kenan, da kin ga yaro ya yi shiru sai ku ce ba lafiya. Wannan ma kin fi Maman Khalil. “

Gajeruwar dariya na yi “To ai alamun ciwon ne”

Shiru ya yi kafin ya ce “Dakinki kamar pharmacy Ko ina duk magunguna, wai yarinya daya ce fa ranar da suka zama biyar, kila sai dai ma’aikatar hada magunguna”

Na kuma yin siririyar dariya “lallai ka sanya min ido da yawa, ashe duk kana lura da ni”

“Sosai ma kuwa, ko bacci kike hankalinki a kan Ramla, ranar ina kallonki cikin dare da ba ta da lafiya tana bacci har da aje kunnenki a saitin hancinta, na san numfashinta kike ne ma”

Dariya na kuma yi sosai “Wai don Allah ka ganni?”

Ya dan murmusa kadan “Eh mana, na yi shiru ne kawai, ki daina zafafa soyayya mutuwa ake gudu, tun da dai ta rataya a kan kowa. Ki ki tafi ko ta tafi.

Yunkurawa na yi da kyar na tashi, hade da daga Ramla na aje a kan kujera “Idan ta zo babu yadda na iya amma kam tabbas zan ji jiki, kuma ma sha Allah ba yanzu ba, sai na lullube Ramla na kai ta daki, kai har sai na dauki yaranta sha Allah.”

“Allah ya yarda, ni dai na fada miki ne, ki dan rika ragewa. Ana boye son yaro a barwa zuciya saboda irin wannan son naki sai ya raba kan yara, kiri-kiri kike nunawa.”

“Ikon Allah! Ni fa ban san ya kake so in yi ba, ina jin ko yarinyar da zan haifa ba zan so ta kamar Ramla ba, ina son yarinyar nan kamar raina wallahi. Allah ne ya dora mun hakan, ba munafurci na kishi ba ko neman gindin zama, wallahi son tsakani ga Allah nake wa Ramla”

“Na sani, kuma ina kallon tsantsar kaunarta a idonki, Allah ya saka miki da mafificin alkairi”

“Amin” na fada a daidai lokacin da nake shigewa bedroom.

Shi ya dauki Ramla a lokacin da muke zuwa chemist din.

A can din ma dai Bilya ce mana ya yi zazzabi ne kawai, kuma ya sauka, paracetamol kawai ya bamu.

A hanyamu ta dawowa ce na ga mai’awara aiko na sayo mana ni da Maman Khalil. Sosai ta ji dadi a lokacin dana kai mata.

Tun da na yi sallahr asuba ban koma ba, kokarin hada mishi break nake yi, don tun dare ya ce min da wuri zai fita.

Misalin 7:30am kuwa muka fito tare da shi, hannuna rike da jakarsa ta zuwa aiki.

Yayin da ya sha kwalliyarsa cikin blue shadda, hatta hular kansa blue ce, ya fita kamar wani matashin saurayi ko don yau bai sanya babbar riga  ba ne oho, amma bana gajiya da kallonsa kwalliyarsa ta yau ta boye shekarunsa.

A daidai lokacin kuma Maman Khalil ta fito cikin shirinta na wani blue boyel na mata kamar hadin baki, dinkin doguwar riga aka yi mata sosai dinkin ya karbi jikinta, Cas da ita kamar ba ta haifi yara uku ba.

Ina kallon yadda yake ta satar kallonta, take na ji kishi ya kamani dole na yi kokarin dannewa kamar yadda ita ma take yi, don na san ganinmu tare ita ma kishin nata ya motsa.

Yanzu kam Kar nake kallonta, tun da na ji sirrinta

Da ni ta fara gaisawa kafin ta koma kansa

“Barka da safiya Abban yara”

Cikin murmushi ya amsa “Barkanki dai Maman Yara, na shiga ai kina wanka.”

“Eh ina sauri ne zan fita yau, muna da baki”

Ya leka cikin mota inda su Khalil suke, ban ji me yake fada masu ba, daga karshe dai ya dago kai  hade da tattara hankalinsa a kan Maman Khalil dalilin maganar da take masa.

“Kun yi waya da Inna ne da safen nan? Ni na kira wayar ba ta shiga ba.”

“Ni ban kira ba ma, tun jiya dai da dare Abdul ya ce min akwai sauki.”

“Eh ni ma Rukayya ta ce akwai sauki sosai, amma ya kamata aje a dubota”

“Tun jiya na yanke wannan shawarar, zuwa yaushe kenan?”

“Sai mu je ranar Alhamis tun da akwai hutun mid time break, sai mu dawo juma’a”

“To shi kenan Allah ya kai mu”

“Amin” ta fada hade da shigewa motarta ta fice cikin kwarewar tuki.

Sai yanzu hankalinsa ya dawo kaina, tun da muka fito hankalinsa kaf a kanta, amma kuma wai a hakan ita ma complain take yi.

Da kyar na danne mugun kishin da yake taso min, na rakashi zuwa gurin

motarsa shi ma ya tafi.

Bayan na dawo daki kuwa mamaki ne ya kama ni, to wai ni ma yaushe za a rika abubuwa da ni ne?

Da alama mahaifiyarsa ce ba lafiya, amma ban sani ba, shi bai fada min  ba, kuma daga can ma babu wanda ya fada mij.

Ni kamar basu sanyani cikin danginsu ba.

“Amma ba komai akwai lokacin da wannan din ma zai wuce, zan yi kokarin samun fada, ai yanzu aka soma wasan.”

Na rarrashi kaina, saboda raina ya baci sosai da  abin da suka min.

Kuma ba zan yi mishi magana ba, ina yi zai ce na cika korafi.

Da yamma daman ba a dakina yake ba, sai bayan isha ya shigo, bai kuma jima ba ya fita, wai bacci yake ji, zai je ya kwanta.

Na ce Allah ya tashemu lafiya, na rungumi yarinyata ni ma mu ka kwanta.

Ranar Laraba da safe ne Maman Khalil ke ce min zasu tafi da Ramla, wai Inna ta ce tana son ganinta.

Dalilin da ya sa kenan na warware mata kitsonta duk da bai tsufa ba, na canja mata wani kanana me kyau.

Kunshi kuwa ba dama in yi wani tun da wancan bai gama fita ba.

Sannan na fadawa Baban Khalil ina son ka ji guda hudu idan ba damuwa.

Wajen karfe biyu na rana kuwa sai ga kajin, na yi dambun nama da biyu sannan na yi pepesoup din biyu.

Har ga Allah daga shi har Maman Khalil haushinsu nake ji, a kan me ba za su fada min cewa Inna ba lafiya ba.

Na ma fi jin haushinsa, idan ya dauke ni mata da gaske ai ya fada min mahaifiyarsa ba lafiya.

Sannan idan abun na kai da kitso ne ai ya kamata ni ma a tafi da ni, amma hakan goga min bakin jini za su yi ai.

Duk da dai na kira Innar na yi mata sannu, amma zuwan ma ai yana da muhimmanci.

Da dare haka Ramla ta matsa wai dole sai na yi mata lalle a hannu, ga bacci ina ji amma haka na daure na zauna ina mata lallen.

A daidai lokacin ne kuma ya shigo yi min sai da safe.

Sai na ji wani haushinsa ya kara kamani, kasa boye bacin raina na yi,  da kyar na amsa mishi sallama.

“Kunshi kuke yi ne? “

Ban amsa ba.

Hakan ya sa ya kalli Ramla “Babyna ana miki kunshi ne.”

Kai ta daga ba tare da ta ce komai ba, Sam magana ba ta dameta ba. Ita ma kamar Affan take, indai ka ji surutunta to da ni ce, ni din ma watarana shiru take min.

“Yan matana, ya na ga yau kamar an taba min ke?”

Ban ce komai ba, sai ma leda da na dakko ina saka hannun Ramla a ciki.

Shi ma bai kara magana ba, guri ya nema ya zauna, har na karasa mata na dayan hannun, sannan na ce mu je ki kwanta.

Rigima ta sanya ita dole sai  an yi a kafa, iya lallashin ta ki yin shiru rikici take ji da alama yau, shi ma ya yi bakin kokarinsa amma ta ki, dole ita sai an yi mata lallen a kafa.

Dole na dauketa na dora a baya, ina neman zane ne, na ji an dauketa a bayana

“kina hauka ne, da wannan katon cikin za ki goyata?”

“To ba shiru za ta yi ba idan ba goya tan na yi ba” cikin dakusasshiyar murya nake maganar don sosai nake jin haushinsa.

“Kin riga kin shagwaba yarinyar nan ya yi yawa, haka nan ma sai ki kama goyata, yanzu kuma ba da ba ne, ba ni zanen.”

Ram ya goyata a bayanshi, duk yadda raina yake bace, na kasa danne dariyata, musamman dana kallesa yana ta zagaye falo da ita, kawai sai na tuntsire da dariya mai sauti.

” Hmmm! Ai ke kam Sa ce, ba ki dariya sai ta baci. “

Na kuma tuntsirewa da dariya, hade da dakko wayata ina mishi hoto.

Buga kofa ne ya dakatar da ni, shi ne ya bude kofar.

Rike da haba ta shigo tana fadin “Ashe haka kuke shagali a dakin shi ne ba ku kirana in gani”

Na tuntsire da dariya, kafin in ce “Ai hanawa yake a kira ki” Ina sane na fadi haka shi yaki ai dan zamba ne, kamar yadda ta fada. yau ne karon farko da ya goya Ramla amma gara in fada mata dama yana yi, duk da yarta ce na tabbata sai ta ji wani abu.

“Wai kunshi aka yi da daren nan?” ta canja salon hirar

“Eh, ta damu wai sai an yi, don ba a yi na kafa ba ne fa ta sanya rigima”

Ta kuma rike Haba tana kallon Ramla da ke goye a bayan tsohonta.

“Ai yarinyar nan tana yadda ta ga dama, Allah kin shagwabata, da can ina ma ta san wani abu lalle.”

Dariya kawai na yi, ba tare da na ce komai ba.

“kin yi ragowar baking powder ne ki ba ni”

“Eh.” na fada lokaci daya kuma na mike zuwa kitchen don dakko mata.

Ina mika mata ta fice, duk da bai yi magana ba, amma na san tabbas shigar Maman Khalil ta tafi da shi.

Wando ne baki mai kama jiki ta sanya,  tsawonsa bai wuce gwiwa ba, jar riga wacce hannunta ya tsaya rabin cinyar hannu, ba ta kamata ba sosai amma kuma ta fito mata da dirinta, bakar hular da ta dora a kanta ma ta kawata mata kwalliyarta.

Sam bana son ganin giccinta idan ina tare da mijina, don muddin za ta gitta muna tare da shi ta kan janye hankalinsa zuwa wajenta gabadaya.

Shiru ya ratsa wajen bayan tafiyarta.

“Kin ki fada min laifina ko?” ya katse shirun namu

A yanzu dai ba zan iya fada ba, Maman Khalil ta kuma dagula min komai.

Ganin ban yi magana ba, ya sa ya kwantar da Ramla  da ta yi bacci, sannan ya ce “To mu kwana lafiya.”

“Allah ya sa” na fada a lokacin da yake fita

Kamar ransa a bace, amma ban damu ba, matar Sonshi za ta wanke mishi shi tas.

<< Hasashena 13Hasashena 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×