Kuma nan Bashir ya ce mu shiga shi ne part dina.
Ban gama tsinkewa da lamarin ba, sai bayan da na shiga, an zuba komai na gyaran falo, very unique babu hayaniya, Irin cool falon nan dai na ƴan gayu. Kujeru leda ash colour mai haske, Sai stool da katuwar plasma. Idan ka dauke wannan babu komai a cikin a falon. Sai bangare daya da aka yi dinning area. Ta Kuma cikin dinning din ne kofar kitchen take.
Still a cikin falon daga kasan stairs din haurawa sama akwai corridor, wanda a nan ne dakin yara yake, dakuna ne guda. . .