Haka na rika amsar yan barka, musamman customers dina, Ana gobe suna yan Kano suka iso da yan Ruma, gida ya cika taf, musamman ranar suna, ban taba haihuwar da na tara mutane gami da samun abun arziki ba kamar haihuwar Aliyu Haidar. Tabbas ya zo min da goshi, Sai godiya kawai.
Raguna biyu Bashir ya yanka min, washegari aka suya hade da rabawa makota, da duk wanda yake da rabo, ranar lahadin gidan ya koma namu, saboda a ranar Jamila da Yusra kanwata suka tafi, yayin da Bashir ya dakko min wata yarinyar mace, za ta. . .