Allah Ne kadai Ya kawo shi gidan Laujen lafiya shi kanshi bai San yadda aka yi yazo ba sai dai kawai ya ganshi a kofar gidan yana muzurai.
mizurai.Musamman yadda ya rika keto over taking mutane suna ta darewa suna bashi hanya saboda gudun da yake shekawa.
Ya fito daga motar yana rufe kyauren da karfi ya kutsa kanshi cikin gidan inda ya iske Laujen da baki wasu manyan mutane ne da Nigeria ke damawa dasu yau gasu a gaban lauyayyen tsohon me baki da tukar goro wanda ke amsa suna Lauje a zahiri kuma yafi shaidan iya shaidana. . .