Skip to content
Part 14 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Allah Ne kadai Ya kawo shi gidan Laujen lafiya shi kanshi bai San yadda aka yi yazo ba sai dai kawai ya ganshi a kofar gidan yana muzurai.

mizurai.Musamman yadda ya rika keto over taking mutane suna ta darewa suna bashi hanya saboda gudun da yake shekawa.

Ya fito daga motar yana rufe kyauren da karfi ya kutsa kanshi cikin gidan inda ya iske Laujen da baki wasu manyan mutane ne da Nigeria ke damawa dasu yau gasu a gaban lauyayyen tsohon me baki da tukar goro wanda ke amsa suna Lauje a zahiri kuma yafi shaidan iya shaidana.

Ya shiga daya daga cikin dakunan gidan masu cike da tarin kazanta har Lauje ya sallami bakin shi yayi mishi magana. “Kaga mutanen ka ko da kuka fayen Jin zancen su a cikin jaridu da kafafen yada laharai yau gasu ta cizo su dole an neme Ni? Ai Ni din Ruwan Jakara ne birni idan ba sha ni ba karkara ba za a gujeni ba.

Alhaji Aminu ya kunduma musu Ashar. “Ina Ruwa na dasu da kake min sharhi akansu?”Ina zaune lafiya cikin farin ciki na kana neman dagula min lissafi. Me aka yi ne kake fada min na ballo bahar maliya?

Lauje ya bude kwaryar dake gaban shi ya debo wani garin magani ya watsa a cikin kwaryar sai ga hayaki yana fita tamkar dai wutar da ke shirin ruruwa.

Hayakin ya cika dakin ya turnike su kafin Lauje ya soma fadin, “Ayi hakuri ba za a fara ba ayi hakuri. Sai ga hayakin yana ficewa daga cikin kwaryar zuwa tagar dakin yana fita.

“Wai hayakin me ye wannan? Ya tambayi Lauje da kosawa.

“Wace mata ce kake kokarin Aure Aminu? Alhaji Aminu bai yi mamakin yadda Lauje ya samu labarin auren shi ba don lauje mugun hatsabibi ne wanda ke hango bakin labari

Alhaji Aminu ya shafi gashin sajen shi yana fadin. “Halima ce fa Lauje matar Muazu wanda Zubaina ta bukaci jinin shi na kuma bayar. “Tashin hankali ! Lauje ya fada kafin yace,”Wa ya aike ka neman matar Muazu? Allah Ya taimakeka da baka riga ka tare da matar ba da ina me tabbatar maka ka siyo bala’i da kudin ka don naman jikin ka ne zai Rika zaftarowa.

“Ban gane ba lauje. Wai me kake son sanar dani ne? “Kada ka sake ka ce zaka Auri matar Muazu ko hada jini da ahalin jinin Muazu don baku dace da jinin ba matukar kayi hakan ko shakka babu kaine za ka tsiyace karshe kuma kayi ta ciwon da ba za ka warke ba. Don Haka kana iya neman kowace ka aura amma banda abinda ya shafi Mu’azu in kuma ka shirya to Zubaina da iyalanta ma sun shirya shine dalilin wannan hayakin da ka gani wanda karshe wuta ce zata tashi kuma zata kone.

Alhaji Aminu ya kwabe hula zufa na tsiyaya yadda ya jarabtu da son Halima kuwa zai iya hakura da ita?

Lauje ya zuba mishi ido yana ganin yadda yake hade zufa ya sheke da dariya

“Meye abin tada hankali haka mutumina?

“Lauje zan iya Rasa farin ciki na duka idan na Rasa Halima Rokar min Zubaina afuwa akan wannan sharadin

Lauje ya Kuma debo garin maganin ya watsa acikin ruwan kwaryar suka zubawarRuwan ido da son suga abinda zai faru sai dai babi hayaki wannan karon sai wani haske mai kamar an haska madubi a rana ya soma zaga saman Ruwan kafin Kuma ya dauke Duff.

“Kai gaskiya mutumina Zubaina na kaunar ka tunda har take maka sassauci.

“Ta yarda da Auren Halimar? Ya tare shi da tambayar. “Bata fa yarda ba, Amma ta yarje maka rayuwa da Halima amma ba da Aure ba !

“Ban Gane ba lauje?

“Komai ma za ka iya yi da Halima amma banda aure. Ma’ana ka kamawa Halima daki tamkar kuna zaman aure Amma fa a kul ka kuskura ka ce igiyar Aure zaka kulla da ita to yanzu ne labarin zai sauya.

Ya soma sosa gashin sajen shi yana tur da Allah wadai da shamakin da zai shiga tsakanin shi da Halima.

“Kai fa wani lokacin baka da dabara mutumina. Manya kicimomi irinka basa rasa Matan da suke ajewa a guest House don Haka sai ka yaudari Halima in har sonta kake da gaske sai ka sakar Mata kudi ta yadda zata bika ku more.

“Bana Jin hakan zata yuwu lauje Halima Yana da kafiya da taurin Kai wannan Auren ma ba da son ta bane tursasawar tsohuwar ta ne Kuma nafi Jin ta tsohuwar akan Halima ita na San zaka bani lakanin da ba zatayi min gardama ba.

“Gashi ma kuwa . Ya jawo wata jakar fatar damisa ya fito da wani kwalli ya Mika mishi. “Karbi wannan yozalin da zaran kunyi ido hudu da ita ko birnin sin kace ta bika sai ta bika. Ya karba Yana juya shi a hannun shi.

Ya taho Yana mamakin hanyar da Yake biye ta neman shahara da daukaka yau gashi duk wata shahara da daukaka babu wadda Bai samu ba Amma anayi mishi shinge da Jin Dadi.

Ya shigo gidan jiki a sanyaye inda Wasila ta gama kulla makircin ta har tayi nufin yaudarar shi.

Cikin Fara a ta tarbeshi har da runguma tana tambayar shi dalilin sauyawar shi.

“Haba Ango kasha kamshi meye matsalar? Ya shafi fuskar ta Yana duban tsakiyar idonta Yana murmushi
“Babu komai uwar gida Ran gida da Ina samun Haka Anya kuwa zanga wata mace har ta burgeni?

“Kar dai ku kyallo dai musamman ku hadu da wadda ta iya fari da idanuwa.

Ta fada tana kawo mishi tiren abinci ta shiga hada mishi ya kuwa kwashi girki tana kashe shi da murmushi da fira har ya gama tace ta hada mishi ruwan wanka.

Ya shiga bandakin inda Hajiya Wasila ta kyalkyale da dariya tana fadin haba bawan Allah ai kazo hannu manta uwa kaci ba Halima kawai ba kai da furta kana son wata mace watakil dai sai ko lahira.

Shigar shi bandakin kawai ya samu kanshi da kelaya Amai sai da ya juye abinda yaci kafin ya zubawa Aman ido sai kuma yayi murmushi. Wasila kenan aikin ki baici ba sai kin sake.

Tsayin kwanaki Wasila na faman tarairaya tare da hada girkuna Amma baya ci sai ta kawo zaice mata zuciyar shi tashi take dole take hakuri.Amma fa kamar ta dura mishi take ji Amma dai ai tunda ya ci sau daya ai angama

Hajiya Kulu kam ta rabu da ji daga gare shi inda ta tabbatar wata matsalar ce ke shirin faruwa kuma ba ga kowa ba sai ga Halima amma sai ta bari taji daga bakin shi Alhaji Aminun yayin da shi kuma lamarin ya dame mishi shi da kanshi Yana shakkar tunkarar Halima da wata magana bare Kuma alfasha

Amma dai yau ya sha alwashin jaraba sa a inda ya shafa kwallin na sihiri ya kuma dora bakin gilashi saboda gudun sabani ya nufi gidan Halima da fatan ya yi ido hudu da ita ya kuma zayyano mata bukatar shi.

<< Hawaye 13Hawaye 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×