Skip to content
Part 52 of 57 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Husna da HAWAYE ya wankewa fuska jin abinda Yaya Mai Kano ya fada yasa ta Soma Raba musu kallo shi da Yaya muhsin dake son daukar ta su wuce.

“Yaya Mai Kano ka gafarce Ni muhsin a yanzu fa mijina ne Kuma yazo tafiya Dani ne.

Kallon da ya watsa Mata ne yasa tayi shiru, “Da yawun wa Kika Aure shi ne?

“Baba Magaji ne.

“Ban yarda da wannan Auren ba Husna dauko kayan ki mu wuce Ina da abinyi.

Dole ta Mike HAWAYE na zuba tana kallon Yaya muhsin da ya kame Yana kallon ikon Allah.

Hajiya ta Mike da son nuna kwanjin ta “Babu inda zakaje da yarinyar Nan in Kuma ka zabi komawa inda ka fito ne to yanzu kuwa Zan Kira Alh Aminu yazo ya mayar da Kai.

Ya dubi hajiya Yana hararar tamkar idanun shi zasu Fado.

“Ki fa tsaya matsayin ki kulu mahaifiyar mu CE ikon ki ba mu ba mune ikon ta ba ke ba. Ai ke da kanki kin San ba Zan kyale abinda Kika sa akayi min ba ko kin manta abinda na fada na sai na farke cikin ku ke da tsinannen mutumin can?

Husna ta fito da hijabinta ya Mika Mata jakar kayan shi inda hajiya ta fizgo Husna shima ya jawo ta ya Kuma nade hannu Yana Nuna Mata zai hambare ta idan ta Kuma kawo hannu Dole ta saurara ya nunawa Husna hanya ta kuwa fice kuka na kwace Mata.

Muhsin da ya biyo su da sauri ya Riko hannun Mai Kano.

“Ka saurare Ni friend don Allah Kar kayi min Haka in ma baka yarda da Auren mu muje kurfi ka tambaya in ma sabon Aure kake so mu sake na yarda a sake din.

Mai Kano ya fincike hannun shi Yana kallon muhsin da wata fuska.

“Muhsin Ni ba friend din da ka sani a da bane . Ni yanzu wani gagarumin makiyin ku ne Wanda ke dab da karar da duka Ahalin ku don Haka ka sawa Ranka son da kayiwa Husna mafarki ne ba tabbatacce ba Ina son daga yau ka manta ka taba sani na ko sanin husna hakan shi zai sa na manta da Kai a cikin Ahalin Alh Aminu idan kuwa kaci gaba da bibiyar husna Ina me tabbatar maka da wutar da zata tashi har da Kai zata kone don Haka jeka abinka na sallame ka.

Husna da dake gaba suna biye da ita ta juyo tana duban Mai Kano.

“Kayi min Alfarma muyi sallama Ni da shi.

“Kun gama sallama ai Husna shi da Ahalin su basu Dace da SHIGA Rayuwar ki ba ke da kanki akwai lokacin da Zaki Gane hakan.

Dole ta wuce tana dagawa muhsin hannu shi da ita suna HAWAYE abinda ya guda shi ya Tara’s Yana kallo Mai Kano ya tsayar da napep suka SHIGA suka wuce inda ya juya don dauko motar shi ya bi bayan su Amma tuni napep din ya bacewa ganin shi Dole ya juya zuwa gidan Hamis inda zazzabi ya Rufe shi Amma Rai da zuciya Naga yadda Za ayi akwato kauna da soyayyar Husna.

Alhaji Aminu kuwa da yaci uban burki a kofar office din DPO ya fito da jakar breif cas wadda ke lode da kudi ya SHIGA office din suka gaisa da DPO.

“Ranka ya Dade ya akayi aka saki yaron Nan bayan me laifi ne criminal ne? Ba bayyanar yarinyar ne kawai abinda nake tuhumar shi ba na Gaya maka har son sace Ni Yake kokarin yi don karbar kudin fansa Kuma Tasha fadar sai ya kasheni.

“Alh Aminu bincike ya tabbatar Mana da bashi da hannu a dukkan laifukan da muke tuhumar shi saboda yarinya ta tabbatar da bashi da hannu Akan fakuwar ta Kuma binciken mu ma ya nuna Mana hakan,

Ya aza mishi jakar wadda ke cike da farare bugun Abuja.

“Ranka ya Dade ga wannan a siyawa Yara sweet ba yawa. Ya bishi da kallo don yaga yadda ya karbi kyautar sai yaga fuskar DPO n ta hade ga Alama Kuma ba irin Wanda ake yaudara da kudi bane.

“Wato ka Gane Ranka ya Dade bana son yaron ya Zama safe Alfarmar da nake nema don Allah a saka sunan shi a cikin manyan criminal ta yadda zai Kare Rayuwar shi a gidan maza koma ya SHIGA sahun Wanda za a yankewa hukuncin kisa!

Zan karo Dan abinda za a siyawa Yara sweet Ni dai fatana yaron ya zamo in Dangerous shine kawai nake bukata don yaron barazana ne gareni.

DPO Yana kallon bakin shi dake zubo bayani shi Kuma Bai katse shi ba sai da ya aje kafin ya Dora
“Alh Aminu naji bayanin ka na Kuma gode da kyauta sai dai kuskuren farko kenan da ka Fara bani cin hanci Akan muradin zuciyar ka Wanda Kai da kanka kasan son zuciya ne . To magana ta gaskiya Ni bana daga cikin layin masu irin wannan Alfarmar da kake magana akanta yau da na Kama yaron Nan da laifin da kake tuhumar shi Wallahi Zan hukunta shi ne Akan laifin shi Amma Alfarmar ka gaskiya ba zanyi maka ita ba don har gobe Ina Jin zafin kudin goron da akewa Yan sanda Akan aikin su to har gobe gaskiya ba tayi Kama da karya ba don Haka dauki kudin ka na gode yaro Kuma na sallame shi tunda Allah Bai aza mishi kaddara ba kaima kayi hakuri da nema mishi jafa I in kuwa ba haka ba Wallahi Kaine zaka kunyata.

Duk gabobin Alh Aminu sai suka sage ya kasa motsawa har sai da DPO n ya Mike saboda fitar da zaiyi shima Dole bashi da zabi ya Mike jiki amace ya baro kudin da yayiwa DPO kyauta sai shi DPO ne ya dauko su ya saka mishi a mota.

“Ni fa Ranka ya Dade ba Kai na bawa ba Ya’ya na nace ka siyawa sweet.

“Ranar da kazo Babu wata matsala sai ka bawa yaran naka abinda zaka Basu Anna yanzu dai sai dai nace ka siyo sweet din ka kawo musu.

Da Haka sukayi sallama inda yaji wani bakin ciki na neman shake shi Anya kuwa Mai Kano ba jinsin hatsabiban aljanu Yake ba?

Da sauri ya dawo gidan hajiya inda Kuma ya iske bakin labarin Wai Mai Kano ya Zo ya tafi da Husna
Kamar ya Dora hannu aka ya fasa ihu.

“Hajiya ina kike tunanin zai kaita? Nafi zaton Legos ya wuce da ita

Ya jawo wayar shi Yana Kiran layin Husna don yaji inda suke.

Mai Kano kuwa da ya tsayar musu da napep Kai tsaye ya wuto wurin mamar su don karba Mata sallama inda ya iske Salma. Husna da taga Halima cikin yanayin hauka sai ta karawa kukanta sauti inda Halima ke Mata Dariya don ganin tana kuka.

Tuni Mai Kano ya gama cike dukkan takardun da aka bashi har suka fito da Halima da Salma wadda tayi musu jagora har zuwa gidan shehin malamin wato malam Abdulrazak Wanda yazo ziyara Kuma Yake dab da komawa Saudi Arabia inda Husna ke tambayar Mai Kano dama mamar tasu tana kusa dasu cikin wannan halin na hauka inda ake kallon ta bace?.

“Husna abubuwa da yawa suke faruwa ga mama Wanda kusan Akan idona suka faru.

Nayi shiru ne don kar na tada hankalin ku don inajin Ni kadai ma Zan iya yanzu Ina so ki kula da mama ne shiyasa na taho dake na San kina Jin zafi na Akan Raba ku da muhsin ko? To kiyi hakuri Akwai lokaci Wanda ke da kanki Zaki nemi Rabuwa da shi.

Ta share hawayen ta Amma ta kasa cewa komai inda yayi Mata bayanin Salma da irin taimakon da take bawa Halima sai taji tana son salmar.

Wayar ta tayi Kara inda taga sunan Alh Aminu ta dubi wayar ta Kuma dubeshi inda ya Mika mata hannu ta Mika mishi wayar ya Kuma katse Kiran ya kashe wayar duka ya saka ta cikin aljihu da Haka suka iso makudawa gidan shehin malamin inda aka Soma da yiwa Halima wanka da Ruwan Rubutu da ganyen magarya cikin ikon Allah Kuma haske ya Soma samuwa har Halima ta Soma dawowa hayyacin ta inda Kuma Mai Kano ya barsu ya wuce Legos inda yace zai dawo Ranar juma a.

A kullum Salma tana zuwa duba Halima har ta Ruko musu wani Abu inda a yau Husna ta nemi Salma da ta Ara Mata wayar ta ta kuwa bata ta shigar da lambobin Yaya muhsin dama duka Suna kanta bugu Biyu ya dauka inda ya jiyo muryar husna na mishi sallama.

<< Hawaye 51Hawaye 53 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×