Skip to content
Part 51 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Alhaji Aminu ya iso gidan hajiya inda yayi Arba da Husna da Kuma sanar da hajiyar abinda muhsin yayi mishi Akan Auren Husna.

“Aikin banza sukayi ka Rabu dasu a yau din Nan ka turo muhsin ya saki Auren ta don kuruciyar su ta tabbatar musu su din Yara ne.

“Angama hajiya Bari naje na Nemo shi yanzun Nan.

Ya Mike Yana ficewa inda Husna ta Kira wayar muhsin tana sanar dashi abinda Daddy Yake Shirin aikatawa.

“Karki damu dear Babu inda Daddy zai ganoni don ba inda zai ganni na tsaya ba Ni da zakiji shawara ta ma da kin taho mun bar garin Nan don nasan akwai wani Abu da Daddy zai Mana.

“Na bar Yaya Mai Kano a hannun hukuma Yaya muhsin kake so? Ba Zan iya Barin shi ba nayi maka alkawarin Ni din taka CE duk Runtsi duk wahala ba Zan barka ba.

“Na sani Husna Ina da tabbas Akan ki Amma Banda tabbas Akan abinda Daddy Yake shirya Mana akan abinda mukayi mishi Amma na yarda dake Kuma igiyar Auren Nan tana hannu na Babu Kuma Wanda ya Isa ya sakar min ita sai Ni da kaina Allah ya dubi Rauni na ya taimake Ni Kar ayi nasara akaina.

“Ai Kaine Mai nasara a ko yaushe don Haka kasaka Ranka inuwa Ina tare da Kai.

Suna Gama waya da Husna wayar Alh Aminu ta shigo tashi wayar. Kamar ba zai dauka ba Amma dai ya nemi tsarin Ubangiji ya dauka.

“Kana Ina muhsin? Ya fada ba tare da ya saurari gaisuwar da Yake mishi ba.

“Kana Ina nace?

“Bana kusa ne Daddy.

“Idan har kana son kanka da Arziki ka saki Auren Husna in kuwa kace a a to Zan Ware kwanji na har sai na tabbatar da na nuna maka Kai yaro ne da baka Gama sanin duniya ba.

“Ka gafarce Ni Daddy naso nayi maka biyayya Amma na kasa.

“Shin zakayi abinda na saka ka ko kuwa ba zakayi ba? Kayi hakuri Daddy Ina son ta.

“Ka kuka da kanka Akan abinda zai sameka don ni da kaina Zan sakar maka Auren yaudarar da ka kullo.

Ya katse Kiran Yana Huci inda gaban muhsin ya Sara har yayanke shawarar zuwa ya dauki Husna su wuce don kar wani Abu ya faru dama shi yasan Daddy n ba kyalewa zaiyi ba don Haka ya fito a firgice ya nufo masanawa

Alh sulaiman Dan sodangi kuwa ya taho da Rubutacciyar takarda daga Alh mukhtar Wanda ya ke da Alfarma wurin DPO sai gashi ko minti talatin ba a Rufa ba an fito da Mai Kano Amma a matsayin beli don Akwai yuwar dawowa.

Mugun kullaci kuwa da mugun alwashi Mai Kano yasha shi ga Alh Aminu inda Yake Jin ko kashe shi yayi Bai huce ba. Babu babbar damuwar shi irin Halima dake can gidan masu lalurar tabin hankali don Haka ana fitowa dashi yayiwa Alh sulaiman Dan sodangi godiya ya Kuma ce zai dawo Legos gobe zuwa jibi da haka yayi mishi Rakiya har Yana bashi kudi Akan yaje Asibiti a duba lafiyar shi da Haka sukayi sallama ya taho Yana siyowa Halima kayan da ta bashi sautu wato dawo da Kuma kuli kuli inda ya hado mata kayan marmari da Madara da biredi har da kifin gwangwani yanufi gidan inda ya iske Salma tazo ta kawo Mata abinci har da sabulun wanka da Kuma dawon da take kulafucin son ci Haka ba tare da an dama ba.

Wata irin kauna da girmama wa yaji Yana yiwa Salma wadda yaji saboda kula mishi da mahaifiya da tayi.

Ya dubi Salma Yana fadin, “Salma da wane bakin Zan gode Miki? Da me Zan iya saka Miki?

“Kar ka damu Ina Jin mama kamar uwar da ta tsuguna ta haifeni Babu komai fatana dai ka karbi shawarar da Zan baka don kullum idan nazo da ita nake zuwa sai dai Rashin samun ka ya kusa kawo tazgaro.

“Zan karbi shawarar ki Salma don kema kin zamo Yar Uwa ta da take kula min da Uwata fada min naji.
Ta juyo ta kalle shi inda taga jikin shi da ciwukan da ke jikin shi don Bata kalle shi ba sai yanzu.

“Subhanallah wani Abu ya faru dakai ne?

Yayi murmushi. Na samu tsautsayi ne Amma da sauki shine dalilin Rashin ganina kwana Biyu.

Ta jajanta mishi inda ta dubi Halima dake ta cin biredi da dawo Bata kula da firar su ba.

Ta maida hankalin ta ga Mai Kano. “Dama don na baka wata shawara ne wadda ita muka taka har Allah ya bawa mamar kawata lafiya wani malami ne da yazo daga Saudi Arabia malami ne da Yake Aiki da Al kur Ani da ayoyin Allah Babu sihiri acikin aikin shi bare kauce hanya shine ma dalilin da naji Ina son nayi maka magana Akan a duba idan da Hali akai mama wurin shi in Allah yasa an Dace shikenan don mamar su Rukayya yanzu Haka ta Soma samun sauki tana Kuma karbar magunguna na Rubutu da na Islamic don na lura da yawan masu lalurar tabin hankalin nan ciwon su ba na Nan gidan bane da an dangano da Al kur Ani da tuni an wuce wurin Amma ka gafarce Ni idan magana ta ba tayi maka Dadi ba.

“Na gode kwarai Salma Nima na taba irin wannan tunanin Amma tsoron aikin shirka da kaucewa ya sa na hakura Amma yanzu tunda kin kawo shawara anyi an gama Wallahi Salma Zan Dade ban samu mutumin da ba Zan iya mantawa kamar ki ba . Amma yanzu ki saurare Ni zuwa jibi tunda Kinga yanayin jikina
Ya fada Yana Miko Mata kudin da ya damtso Wanda Alh sulaiman ya bashi ya kuma ce ta bashi lambar wayar ta.

“Ta kawar da kanta daga kudin da Yake Miko Mata Wai ba zata karba ba ta Kuma sanar dashi Bata da waya.

“Ya Miko Mata tashi wayar Yana fadin Dole ta karbi har kudin.

Da kyar ta karba sukayi sallama tana cewa Halima. “Mama na tafi.

Halima da ta cika Baki da biredi tace.

“Nagode Yar diyata me kawon dawo gobe ma ki kawo min kinji?.

Da Haka ta fice tana fadin Zan kawo Miki in Sha Allah.

Ya dubi Halima Yana fadin Mama kina lafiya ko? Ta dubeshi tace

“Ina fa lafiya Mai Kano ai ba lafiya….

“Me ya faru ne? Ta nuna mishi dakin da wata marar hankali take tace,

“Kaga me dakin can kullum sai ta Hana Ni bacci da haukan ta dama ina so kazo ka fidda Ni daga gidan Nan dama Kai ka kawo Ni.

“In Sha Allah kin kusa Barin gidan Nan Allah ya baku lafiya ku duka.

Tayi saurin amshewa da Ameen tana jeho mishi tambayoyi wasu kamar na hankali wasu Kuma na soki burutsu.

Ya jima Yana sauraren ta in ta tambaye shi ya amsa Mata in ta nema Kuma ya fito ya samo Mata har yayi Mata sallama ya taho shima dai sakon dawo ta bashi da Awara.

Husna da ta Soma jiran zuwan muhsin su Arce taga shigowar Mai Kano da sauri ta taho tana Rungume shi inda hajiya ta fito tana mishi wani banzan kallo. Shi ko kallon ta baiyi ba ya Ruko hannun Husna Yana fadin ki hada kayanki yanzu zanje na dawo mu wuce Lagos. Bai jira sauraren ta ba ya fita inda Kuma Alh Aminu ya faka motar shi ya SHIGA gidan inda Kuma muhsin ya karyo kwana yaga motar Alh Aminu a kofar gidan hajiya inda Kuma yaji wata faduwar gaba me tsanani ya dafe kanshi Yana Kiran sunan Allah. Da sauri ya koma baya Yana shawarar SHIGA har dai ya Gane ba shigar bace mafita ya koma gefe can nesa da gidan ya aje motar Yana kallon kofar gidan.

Alh Aminu da ya shigo gidan hajiya ta tarbeshi tana fadin ya karbo takardar sakin? “Bai yarda muka hadu ba hajiya Amma Ni da kaina ma Zan iya sakin Auren muhsin don Haka yanzu kuwa Zan sake shi.

A take kuwa ya fito da biro da takarda ya zana sakin kwarara har guda uku ya linke takardar ya mikowa hajiya ta karba tana fadin.

“Shikenan kuwa Amma ka San kuwa an sako Mai Kano? Ya zabura Jin Wai an sako Mai Kano

“Anya kuwa Mai Kano Kika gani hajiya? Shine Wallahi yanzu ma ya fita anan.

Ya Mike Yana fadin Bari naje na samu DPO naji yadda akayi Haka. Ya fice aguje don yasan bayan tiyar akwai wata cacar Kai tsaye ya nufi office din DPO.

Da sauri muhsin da yaga fitar Daddy ya tsallako ya SHIGA gidan inda Kuma Mai Kano ya dawo ya iske muhsin Wai zasu wuce shi da Husna.

Hajiya ta mikowa muhsin takardar sakin tana fadin.

“Kai fita idona yaro kaji dama wannan Auren na yaudara da kuka kullo ai kasan karshen shi kusa Yake to ga takarda Nan yanzu ubanka ya saki wannan gantalallen Auren don Haka fice sahunka a likkafa.

Mai kano ya dubi hajiya ya Kuma dubi muhsin yayi musu wani banzan kallo kafin ya dubi Husna Yana Fadin

“Kin hada kayan naki? Fito muje wannan matsalar su ce da hajiya da wannan Gayen shi da Uban shi duk me magana Akan ki ya sameni gida Amma kin gama kwana garin katsina bare ayi Mana kama karya.

<< Hawaye 50Hawaye 52 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×