Skip to content
Part 57 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Wani matsiyacin gudu da suke a motar tamkar masu gasar tsere . Tun a Nan muhsin ya Gane Daddyn da gaske Yake don ta mirro Yake hango fuskar Daddyn Babu sassauci sai ya Kuma Rikice wa da neman mafita don ya San manufar Daddyn ba ta ALHERI bace wannan bin da Yake mishi har yayi nufin daukar titin government house Wanda zai fita gari sai ya Gane kuskuren da zai tafka kenan idan Daddyn ya cimma shi a in da Babu yawaitar mutane don Haka sai kawai ya shawa shataletale ya juyo ya nufo gida ya San dai a gida gaban Mami ba zai yi mishi abinda mamin zata saurara ba sai kawai ya nufi gida Alh Aminu na biye dashi inda ya matsa horn Mai gadi ya bude kofar duk suka duru cikin gidan Amma kafin ya fito daga motar Alh dake bayan shi ya fito fuska murtuk Yana wucewa kamar zai shiga kofar da zata sadaka da falon gidan sai Kuma ya fasa ya tsaya a Bakin kofar Yana zaro wayar inda yake bawa me gadin umarnin Rufe kofar ya kuwa Rufe ta Ruff kafin ya Danna nomber ya Kira yace Yana bukatar su yanzu.

Muhsin dake zaune cikin mota Bai San abinda Daddyn ke kullawa ba fargabar shi ya fito Bai San abinda Daddyn zai yanke mishi hukunci ba sai kawai yayi Shahadar bude motar ya fito ya tako ya iso gaban Alh Aminu dake tsaye gaban kofar don Hana shi shigar mishi gida . Ya zube Agaban shi Baki na Rawa ya Rasa da me zai Fara Rokon gafarar Daddyn

Ya dago yaga irin kallon da Yake watsa mishi fuskar Nan sai kara tamkewa take.

“Ashe har ka Kai marar kunyar da zaka sake duban hanyar gidan Nan da sake shigo shi? Duk abinda nayi maka da wannan zaka saka min? Ai Kai da kanka kasan ba Zan taba kyale ka ba shine da kaga tusa ta karewa bodari sai ka nufo gida baka San Rami ka kawo kanka ba? Haka da Kai kaima Nan takadari ne? Har ka iya irin wannan iskancin? Kuma ka Rasa Wanda zakayiwa sai Ni don tsohon wulakanci ka zagaye aka daura maka Aure da Husna duk da na sanar dakai nine mijinta baka San cewa duk gudun barewa Bata iya kure daji ba? Ka tafka kuskure ba Dan kadan ba muhsin don yadda na azabtu da soyayyar Husna Zan iya aikata komai a ciki kuwa har da kawar da Kai don Haka Ni bana bukatar wani Karin bayanin ka Zan hada ka da wadan da baka Rai na ba su na San zaka fada musu inda Husna take Amma Ni ba Zan tambaye ka ba tunda Rainin da kayi min ya zarta na abokin wasan ka.

“Daddy yanzu Ashe Akwai Ranar da Zan tsinci wadan Nan kalaman a Bakin ka? Akan Husna d in adalci zakayi Mata ba zaka yarda a Aura Mata Wanda Bata so ba Akan hakan kake fadar zaka kawar da Ni akanta Daddy? To zanyi farin ciki idan Kai da kanka kayi Ajalina Daddy Amma kasani Auren Husna yanzu na Fara Rokon shi Babu Ranar da Zan sake shi sai dai idan na bar Duniya Sharia ta sakar min.

“Za kuwa ka bar Duniyar sai Shari ar ta sakar maka idan ka saka taurin Kai kenan Amma idan wuya ta isheka nasan Kai da kanka zaka saki igiyar Auren Husna kaga kana Raye ma hakan zata tabbata.

Kafin ma ya Rufe Baki jiniyar motar ta shaida musu ta iso ganin get din a kulle yasa Alh Aminu kwalawa Sadi me gadi Kira Yana fadin ya bude musu kofar ai kuwa Sadi ya kwasa aguje Yana budewa motar ta shigo inda kuma haj wasila da Amal sukaji jiniya a gidan suka fito aguje inda suka iske Alh Aminu da muhsin durkushe Agaban shi daidai da fitowar Yan sandan Alh Aminu na nuna musu Muhsin.

“Gashi Nan kuje dashi idan ya sauwake wa kanshi wahala ya fahimci abinda nake nufi in Kuma ya kawo taurin Kai wannan kamar da Yake da ita ku sauya mishi wata wadda zai Gane ba duka Duniya ne ke da Dadi ba wani wurin ya Fi kama da sashen jahannama.

Kafin ma ya dire wasu Yan sandan sun cakumo shi da nufin watsawa mota inda Kuma haj wasila ta fahimci zancen har tana dako tsalle sai gata gaban Dan sandan da ya Riko muhsin.

“Kai sake shi malam ka shigo har cikin gidan su ka nemi wulakanta shi?

Dan sandan ya saki muhsin Yana kallon haj wasila dake aunawa Alh Aminu wani matsiyacin kallo.

“Kana ganin wannan shine hanyar daukar mataki Akan shi? To na Rantse maka ba Zan taba yarda ba Akan ka tozarta Muhsin Akan abinda yayi sai dai mu tarwatse koma mu kone Ni da Kai Wallahi.

“Ba zamu kone ba don Ni Ina da BURI Wanda nake fatan ya cika shi Amma tunda Haka Kika ce kema sai an saya min ke Wallahi.

“Ku Kama su har ita ku kulle mun su tunda itama ta zabi hakan.

“Ranka ya Dade ayi sulhu dai tunda lamarin family issue ne.

“Yaci uban sa family din shi da issue din duk uban su ku Kama su nace ba umarni aka Baku ba.
Amal ta Soma Kuma tana Rokon shi.

“Daddy don girman Allah Kar kayi min Haka yaushe zaka sa a kulle su.

“Kema idan Kika Kuma cewa uhum Wallahi sai an hada har ke tunda duk munafukai ne ku . Dole Amal ta kame bakinta ta Rike da hannunta Amma Kuma kuka take Wai don kar tace wani Abu.

Haj wasila tayi murmushi ta dubi muhsin.

“SHIGA muje Ina ce iyakar Nan ne ba tafiya LAHIRA bace? Muje Allah ya fitar damu kunya Muhsin ya share hawayen shi Yana ganin Daddyn ya gama cin zarafin shi akan kulle haj wasila don tashi ba ya damuwa yasan ko yaje zai fito Amma ace an Kai mahaifiyar ka wannan wurin Kuma ace mijin Auren ta ne ya kawo ta a kulle ai an gama cin mutuncin shi Amma umarnin da aka bawa Yan sandan Dole suka SHIGA motar aka jasu zuwa station aka Kuma kulle su inda haj wasila ta Kira Yayanta ta sanar dashi tun suna mota Amma Kuma ya sanar da ita Yana Abuja Amma zai Gama abinda Yake kafin jibi ya dawo.

Halima dake zaune tana kallon Husna da salma suna labaran su Wanda mafi yawa husna labarin Muhsin ne take Bata ita Kuma Salma tana fada Mata yadda mahaifiyar ta Tasha fama da jinya wadda Adama ke fada kanta tsaye cewa itace ta turo Mata makarai Kuma ba zata taba warkewa ba sai dai mutuwa Kuma hakan ce ta faru.

Halima ta tausayawa mamar Salma sai tayi Mata fatan Allah yasa can ta fiye Mata Nan inda Kuma Husna har kuka tayi saboda tausayi . Wannan fira ita ta dauke su har tsawon Dare Wanda suka manta da maganin da ake shafawa Halima Basu shafa gyangyadi ya Soma dibar Halima har ta bingire bacci yaci karfin ta Suma suka kwanta Ashe ba karamin kuskure suka tafka ba Domin ko Zubaina ta Kai tsayon kwanaki biyu tana son SHIGA jikin Halima Amma saboda maganin da ake shafa Mata ta Hana tayi wani tasiri sai yau Allah ya Ara Mata Rana.

Halima cikin barcin ta taji wani Abu na Mata yawo akai Wanda ya sa ta farka ta tashi zaune inda taga ana Bata tsoro.

Ta firgita matuka Gaya sai Kuma taji Babu abinda take so sai ficewa ai kuwa ta Mike tana tsallake su Husna dake barci ta fice abinta ta nausa dawa a cikin talatainin Dare.

Acan Kuma Mai Kano Yana kwance yayi wani mugun mafarki da Halima Wai wasu bakaken karnuka da maguna suna binta tana gudu tana neman taimako Amma babu kowa har suka dangana da ita cikin wani daji me tsananin Rukuki kafin suka zagaye ta suna Mata kuka inda itama take kukan tsorata . Kamar daga sama wani Abu Mai Kama da kugiya ya zabaro ta yayi sama da ita.

Yana zuwa daidai Nan a mafarkin wani ladani ya rangado Kiran sallar asubahi ya farka Yana Jin jikin shi na kyarma yayin da ya hada uwar zufa.

Gaban shi ke harbawa tamkar zuciyar shi zata faso.

Sai kawai yaji katsina yake son zuwa dubo mahaifiyar shi don Haka Yana Gama sallar asubahi ya bugi hanya don ya jaraba Kiran layin Husna sai Kuma ya tuna Ashe ya karbe wayar sai ya koma Kiran layin Salma ita Kuma sai Kara take ba a daga ba sai yaji lallai babu lafiya.

Kiran sallar asubahi ya tashi su Husna inda suka ga Babu Halima sai su Biyu kadai inda Husna ta tashi Salma tana fadin, “Tashi Salma Banga mama ba. Salma ta tashi a firgice tana Fadin

“Kin duba ban daki Bata ciki?

“Bata ciki na Kuma duba soro Naga kyauren bude bayan mu muka Rufe shi. Da sauri Salma ta Mike suka SHIGA jaje ko sallar Basu samu damar yin ta ba inda har gari ya waye Babu Labarin Halima bare Wanda ya ganta. Sai Husna ta Soma kuka Salma na binta da fuskar jimami don ko kalmar hakuri ta kasa nufar ta da ita inda Kuma Mai Kano ya Riske su a wannan halin yayin da Adama ke auno musu Asher Wai Kar su jawo Mata Bala I gidan ta ba na mutuwa bane.

<< Hawaye 56Hawaye 58 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×