Mai Kano da ya iso ya samu Husna na kuka shabe shabe ya kuma samun kanshi a rudani.
Bai tsinke ba sai da Salma ta fada mishi sanadin kukan husna wadda ta fada jikin shi tana gunji ba baka sai kunne.
“Garin Yaya hakan ta faru? Ya tambaya jiki na kyarma
“Lafiya Lau muka kwanta da ita Amma muka wayi gari babu ita inda muka Gane tun tsakiyar Dare ta fice don gidan ta bude ta fice.
Wani matsiyacin duka da yaji akan shi tamkar an buga mishi guduma shi ya tilas ta mishi Zama ba don ya shirya zaman ba Yana dafe kanshi. “Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Yake ta maimaitawa gaba Daya lissafin shi ya Burke bashi da sauran idea Banda ambaton sunan Ubangiji . Sai Kuma ya tashi ya fice inda yayi ta bulayi da tambayar ko an ga Halima. Amma Babu wata amsa da ta gamsar dashi haka Yake tafe Yana wurga idanu fatan shi ya hango Halima Amma ko kyallin ta Bai gani ba da zuciyar ta amsa sai HAWAYE ya Soma wanke mishi fuska ba komai Yake hange ba sai halin da Halima zata kasance gashi ba lafiya ba duk da sauki ya Soma bayyana Amma fa Bata magana Kuma yadda Duniyar Nan ta zamo meye ba zai faru ba?
Bai damu da mutanen dake wucewa suna kallon shi ba Alhinin mahaifiyar shi da tausayin ta shine damuwar shi. Har Gefin magaruba Yana zaune inda Kuma Alh Aminu ya wuce a mota ya hange shi da sauri yaci burki Yana zaro wayar shi ya dokawa tsini Kira. Tsini shine Dan ta addar da suke tare da zarto harma yafi zarton Rashin imani don shi har kisa Yana you . Da sauri kuwa yake bawa tsini kwatancen inda yake yace Yana son yazo yanzu ga Mai Kano ya gani. Ai kuwa minti Sha biyar ba a Rufa ba sai ga tsini da tawagar shi napep ya diresu ba su jira komai ba suka cakumi Mai Kano suka wurga cikin napep din wasu daga cikin su suka SHIGA aka burka . Rukon da sukayi mishi ne da wukar da Daya daga cikin su ya Dora mishi a makoshi akan Yana yin magana zai shatale shi yasa Dole ya zuba musu Ido cikin tafasar zuciya. Motar da tazo ta shudasu ta Alh Aminu Wanda ya leko ya dubeshi ya Kuma karawa motar gudu shi ya shinshinowa Mai Kano wannan tsiyar ba daga kowa take ba sai shi Alh Aminu don ko Babu komai ace yaga an auna shi da wuka Amma ya Kara gudu Bai nemi taimakon shi ba lallai akwai lauje cikin Nadi.
Tafiya Mai nisa kafin suka Zo wani gida Wanda ya dai Rike da sun wuto sabon gida sun kama hanyar jibia sai Kuma yaji an waske sai gasu a wani gida da ba zai ce ga wurin ba . Haka suka kawo shi gidan suka zubar suna kallon shi suna muzurai. Sai Kuma suka juya suka fice tare da kulle gidan suka barshi cikin DUHU Wanda tuni ya gama lullube samaniya. Ya sunkuyar da kanshi ba wannan halin da ya SHIGA yanzu ne damuwar shi ba a a halin da Halima zata kasance. A Ina take yanzu da duhun magaruba Yake lullube samaniya? Taci abinci ko kuwa me? Duk sauron dake mishi guda a kunnuwa da neman ya Basu Dama su zuki jinin jikin shi Basu Dame shi bare ya Basu tsoro ta hanyar Kora sai ma ya Mike kafa Yana zabga tagumi inda kuwa saurayen suka ce maraba gasasshe Wai kura taga bakin jaki suka kuwa Yan yame shi.
Safina da ta gaji da zaman shiru ta fito sashen haj wasila don ta bada sakon Dole a ciyar da ita tunda har yanzu zaman su take sai ta iske Amal na gugar HAWAYE. Ta kwabe Baki tana fadin
“Amal lafiya? Amal din ta Rattabo Mata bayani akan yadda Daddy yasa aka Kama Muhsin da Mami.
“An ga muhsin din ne? Amal ta dubeta cikin takaici “Wai ko bakiji nace Miki Daddy yasa an Kama shi har da Mami ba?
“Ban da damuwa Amal don an Kama Mami muhsin shine damuwa ta Bari naje station din yanzu zanyo belin shi ai mune da Yan sandan
Ta kuwa fice da sauri Amal na binta da kallo
Tsini ya zube Agaban Alh Aminu Yana fadin
“Alhaji me zamu kaddamar wa yaron can tunda yazo hannu?
Alhaji Aminu yayi murmushi Yana shafa gashin sajen shi.
“Wato tsini bayani kawai nake so yaron Nan yayi muku na inda kanwar shi take da zarar ya fada muku inda take to shikenan aiki kawai zakuyi mishi wato ku kashe Dan iska ku jefa Rijiya inda babu Wanda zai San ya mutu ayi jaje a gaji a barwa Allah…
“An gama alaji ya fada Yana cije Baki irin na tatattun Yan iska Alh Aminu ya kawo kudi ya bashi suka Rabu Akan ya Soma matsar Mai Kano har ya fada mishi inda Husna take da Haka tsini ya baro gidan. Ai kuwa tun a Daren tsini suka daure Mai Kano tamkar wani goro Suka Fara nuna mishi azaba da uku ba duk dai akan ya Fadi inda kanwar shi take inda ya Gane baiyi kuskure ba da yace Aiken Alhaji Aminu ne sai dai duk wuyar da su tsini suka gana mishi Bai sa ya Fadi abinda suke so ya fada ba wato sanar dasu inda Husna take Haka suka barshi ya kwana cikin tsamin jiki da ciwon gabbai
Husna da hankalin ta ya kasa kwanciya Akan fitar Yaya Mai Kano da Rashin dawowar shi don ta San ba a hayyacin shi ya fita ba sai Kuma wayar shi da ake ta Kira tana ringing Amma baya dauka . Sai ta Kuma kara SHIGA tashin hankali inda ta Kira Yaya Mubarak da suke can jihar bayelsa suna bautar kasa shima dai Bata sameshi Dole ta hakura har gari ya waye Amma Babu Labarin Mai Kano har tayi nufin zuwa gidan hajiya sai Kuma ta fasa saboda ita kanta a yanzu son boye kanta take ko don sake yin Arba da baba Aminu Wanda shine ummul aba isin tarwatse masu farin ciki don Haka sai kawai ta Kira muhsin shima tashi wayar Akashe. Sai kawai ta Rushe da kuka tana ganin Bata da sauran madafa
Salma ce Mai Bata hakuri da nuna Mata Allah shine mafi sani Akan halin da take ciki tayi ADDU A zaifi ta yi kuka tunda shi Allah ba bu Mai mishi tilas Akan Dole sai yayi mishi yadda yake so.
Kai tsaye Safina ta nufi gidan su inda ta samu Anty maimuna tana Rokon ta Akan ta Kira kawar ta Anty gimbiya wadda mijin ta shine DCO don yasa ka Baki a saki Muhsin.
Anty maimuna ta dubeta a sheke tana fadin
“Ai Ni na zare hannun na Akan duk wani Abu da ya shafeki Safina tunda Kika zabi muhsin akaina duk cin mutuncin da wasila tayi min Amma saboda kece wadda Kika Rako Mata Duniya an koreki Amma saboda Rashin Daraja Kika kwashi jiki Kika koma to ki wanye lafiya Amma Ni wannan sune kawai zan zuba Miki . Ta nuna idanun ta Kuma Koda wurin gimbiyar kikaje Wallahi zance Kar ta sako mijin ta acikin maganar ko da Yake jeki ma da kanki ko don Baki San itama abinda kikayi ya Sosa Mata Rai ba? To Babu Ni acikin harkar ki Haka ma karki sako min wani Dan uwa ko amini yanzu ke ba Ahali na bace Ahalin wasila ce Ni Kuma babu Ni babu Ahalin wasila har Duniya ta nade haihata haihata don Haka tashi ma ki bar gidan Nan tun Raina Bai baci ba Wallahi.
Haka Safina ta taho tana Jin wani takaici. Dawowar ta ya Kara Mata wani takaicin don Bata da komai na abinci komai nata ya Kare gashi Kuma mutan gidan suna neman tarwatse wa Dole ta dawo wurin Amal tana karbar abinci.
Alh Hassan Yayan haj wasila ya iso garin katsina ya samu wadan da cas din haj wasila da muhsin suke hannun shi suka zauna inda yayi nasarar samun belin haj wasila amma Muhsin Kam ance ba za a bayar da belin shi ba shima don Yana da Alfarma aka bashi haj wasila Bai Sha haushi ba sai da aka fada mishi Wanda ya kulle su wato Alh Aminu don Haka ya dauko haj wasila a motar shi wadda tace ba zata koma gidan Alh Aminu ba Amma da Yake Alh Hassan mutum ne me zuciya sosai Bai ko saurareta ba Kai tsaye ya nufo gidan Alh Aminu ya Kuma sameshi a gidan.