Skip to content
Part 59 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Alhaji Hassan ya shigo gidan Amal na mishi barka da zuwa tana kamo Haj wasila tana farin cikin ganin ta ta fito.

Alh Aminu ya sauko daga bene don ya ga shigowar Alh Hassan din ya Miko mishi hannu suka gaisa Yana tsare shi da idanun shi masu kaifi da son ya fashe masifar dake cin shi.

“Wata tatsuniya najiyo bayan wasila ta Kira Ni Ina Abuja ta sanar Dani Wai tana caji office sai da naje nake bincikar Wanda ya kulle su Wai sai aka sanar Dani Kaine.

Wane irin abin kunya ne Haka Aminu fidda zancen iyali zuwa ofishin Yan sanda kuma abin kunya Wai Mata da yaron ka?

“Dama ka taba zuwa kayo belin ta ko kuwa yau ne karon farko? Ya tari Alh Hassan.

“Ko da yau ne kawai kana ganin kullewar itace hanyar gyara? To nayi belin Wasila Muhsin kuwa duk hukuncin da kace ayi mishi wannan Ruwan ka ne in ma kisa kaga Dacewar ayi mishi babu me Asara sai Kai Wasila dai ba Zan taba Bari ko akaifar ta ta salwanta ba yanzu ma nazo ne don ka fada min abinda sukayi maka.

“Ai ga tanan ka tambaye ta ta fada maka abinda sukayi Mana.


Ya fada Yana hararar Alh Hassan din
Haj wasila ta Soma Rattabo mishi bayani Akan Auren da muhsin yayi Wanda ya Auri Husna wadda shi Alh Aminun ke so shine fa Kawai yasa aka Kama shi har cikin gidan Nan Kuma daga tayi magana itama yace ahada da ita.

“Wannan matsalar shi ce . Kuma yanzu kana so kace so kake muhsin ya saki matar shi Kai ka Aura Anya kuwa anyi hangen nesa Alh Aminu? Wata halak din fa don kunya ake barin ta.

“Hassan ka bar maganar Nan tunda ba hurumin ka bane Ni nasan abinda nake nufi akan hakan muhsin kuwa Dole ya saki Auren Husna ko da zuciya ta Bata karbeta ba saboda wani Abu guda Daya Tak!. Na gode da ka Gane muhsin iko na ne Kuma Wasila da kayi belin ta to ka wuce da ita can gidan ka don a yanzu gaskiya bana bukatar ta kusa Dani.

“Itama haka ta nema don kar na Zama babban kawai yasa na kawo ta Amma ita ta Fara cewa ba zata dawo gidan Nan ba Kuma tunda kace haka alhamdulillah. Ya dubi haj wasila Yana fadin, “Juya muje. Amal da ta nemi binta Alh Hassan ya ce “Ke Ina kike Shirin binta? Nan shine dolen ki itama zata je inda Yake dolen ta Amal na kallo suka fice taji Hawaye na bin gurbin idonta me Yake damun Daddyn da Yake neman fita hayyacin shi?

Mai kano yana daure jikin wani karfe Wanda suka sakale hannuwan shi da kafafun shi ahaka ya kwana babu ta yadda zaiyi motsin kirki tamkar kusa aka sa aka kafe shi

Tsini ya shigo Yana zare mishi idanu.

“Wato kaima Nan Jan wuya ne ko Ina tambayar ka inda bebyn Nan take kaki kayi magana ko? Koko wuyar da na baka ce tayi maka kadan? To Yasin yau matsar da zakaji sai ka Fadi yadda uwar ka ta kawo ka Duniya. Ya fada Yana murza shimfideden tafin hannun shi me kama da faranti.

“Dubi hannun Nan. Ya nunawa Mai Kano ya tado fuska Yana kallon hannun.

“Ka ganshi Nan? Rain da ya fitar Yana da yawa don ba zai kidayu ba kaima zaka shigo cikin lissafi matuka ka kawo taurin Kan da ka kawo don wannan hannun da kake gani baya Jin wahalar yiwa gangar jikin ka part part . Yanzu ne zai fizgo kunnuwan ka ya ajiye su Agaban ka.haka Kuma zai iya Ciro kwayoyin idanun ka Suma ya zube su kasa . Hancin ka kuwa da harshen ka duk cikin sauki zai sauke maka su ka Kare musu kallo da kyau don Haka wane ka zaba? Mai kano ya dube shi Yana ayyana Banda daure Yake Wallahi sai tsini ya Gane shi ba Dan iska bane shi da ya Rayu a ciki garin Legos garin da in zaka shige shi ba ayi maka welcome to sai dai a fada maka Nan fa Legos ce inda duk wani karamin takadari ya ke gogewa da iya shege Amma sai ya barshi ya zabi yin shiru ne don baya Jin zai Fadi abinda suke son ya fada.

Tsini ya gaji da kallon da Mai Kano ke mishi don yayi zaton zai fada mishi abinda ya nema ko Kuma yaji tsoron abinda ya fada.

“Kana kallo na Dan samari ko nayi Kama da kanen tsohon ka ne? Murmushi Mai Kano yayi Wanda ya fusata tsini ya Kai mishi naushi a hanci sai ga jini na biyowa kafofin hancin Mai Kano.

“Don kaza kazan ka Dariya ma na baka da kake kallo na kayi min dariya? Ya Kuma Kai mishi naushi a tsakiyar makoshi inda Mai Kano ya Runtse ido don yaji tamkar zai Suma ya bude idon shi Jin abinda tsini ke fada Wai tunda ba zaiyi magana ba Bari ya nuna mishi yadda ake fede masu taurin Kai irin shi.
Ya bude idon ne daidai da tsini ya zaro wata siririyar aska daga kwibin shi.

Ya bi askar da kallo ga mamakin shi sai yaga tsinin ya shatala mishi ita a tafin hannun shi dake daure sai ga jini Yana diga amma duk radadin da Mai Kano yake ji Bai nuna yadda tsini zai Gane ba.

Haka tsini yayi ta gana mishi azabobi iri iri na Wanda imani Bai kusanta ba Amma baya ce yaji Amon muryar Mai kanon ba bare ya samu amsoshin tambayoyin da Yake jera mishi Dole suka Kira Alh Aminu suka sanar dashi abinda ke faruwa na Mai Kano dai ya Sha wuya Amma Bai bude Bakin shi yayi magana ba bare ya Fadi inda Husna take.

“Tunda ya saka taurin Kai tsini ku kaddamar mishi kawai ku kashe Dan iska gawar tashi ma ku jefar Rijiya dama ko da ya fada ba zai tsalake wannan siradin ba.

“An gama Alaji tsini ya fada ya na murza shimfideden tafin hannun shi.

Husna da ta gaji da jiran tsammani sai ta karbi wayar Salma tana Kiran Anty Amal don taji abinda ya boye Yaya muhsin don gare shi take saka Ran zai samo Mata labarin Yaya Mai Kano ai kuwa Amal ta cabe Kiran jin muryar Husna.

“Ke kuwa baiwar Allah Ina Kika shige Ina ta neman layin ki na kasa samun ki?

“Uhum Anty Amal ki Bari kawai kaina ya kusa kamawa da wuta sai ta sakawa Amal din kuka inda itama Amal din ta Rushe da nata kukan suka taru suna ta sharbar kuka a waya kafin Amal din ta koma Rarrashin Husna.

“Nafi ki kasancewa cikin damuwa Husna. Ciwo biyu ke damun zuciyata akasin ke da Yake guda Daya. Ciwon son Yaya Mai Kano Husna yayiwa zuciya ta muguwar illah gashi wayar da nake samun shi ma na Daina samun shi ga halin da Mami da Yaya muhsin suke ciki.

“Me ya samu mamin da Yaya muhsin din?
Amal ta fada Mata Yaya muhsin Yana kulle Daddy yasa aka tsare shi yayin da Mami kuwa Daddyn ya koreta.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un take maimaitawa.

“Don Allah Husna ki hada Ni da Yaya muhsin na sake tallata mishi soyayya ta ya CeCeni Kar na mutu abubuwa sunyi min yawa zuciya ta na dab da tarwatse wa.

“Shi ne ai na Kira don na nemi taimakon Yaya muhsin Anty Amal yau kwana biyu Banga Yaya Mai Kano ba alhalin yazo muna cikin wani hali gashi Kuma kin sanar Dani Wai Daddy yasa an Kama shi. Sai ta Kuma saka kuka.

“Anty Amal ke Abu biyu ne damuwar ki Ni yanzu abinda Yake damuwa ta yafi guda biyar ga Yaya Mai Kano ban San halin da yake ciki ba ga mahaifiyata da itama take cikin wani hali na neman agaji itama ban San halin da take ba ga Yaya muhsin da nake ganin shine kadai garkuwa ta shima ga yadda Allah yayi dashi Ni yau na Shiga uku na lalace ta Kuma fashewa da kuka inda jikin Amal yayi sanyi Jin Wai ba a ga Mai Kano ba . Tayi karfin halin tsaida husna daga kukan ta.

“Kinga yanzu ki yi hakuri ki bar kukan Nan yanzu mafita zamu nema.

“Ta Ina zamu nemi mafita Anty Amal?

“Yanzu kina gidan haj na sameki sai mu San ta inda zamu Fara?

“Bana gidan haj Amma kizo Nan wurin kudin wayar Salma suka Kare Bata bawa Amal kwatancen ba

Amal ta biyo sahunta tayi mata kwatance tace ta jira ta ga tanan zuwa. Da Haka ta aje wayar tana Kara tsananta kukan ta . Lallai Daddyn da gaske Yake shine har ya Kai muhsin aka tsare?

Amal ta karaso suka Soma laluben mafita inda Husna ta nace da lallai sai dai suje inda Yaya muhsin Yake su dubs shi kafin su San abinyi.
Dole Amal ta Mike suka nufi station din cikin motar Amal din.

<< Hawaye 58Hawaye 60 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×