Skip to content
Part 60 of 61 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Zuwan su Husna a station yayi daidai da zuwan Abokan Aikin Yaya muhsin Wanda suka samu labarin Yana tsare

Baccin zuwan Abokan Aikin nashi da su Amal basu samu damar ganin shi ba Suma don sun nuna ID card din su Kuma daga higher court shine dalilin barin su. Husna da Amal na Rabe gefe suna kallon ikon Allah.

Aka fito da muhsin Wanda ya sauya kamanni duk da ba a Fara matsar shi ba Akan yayi bayanin inda Husna take don shi kanshi Alh Aminun yasan Mai Kano ne Kawai yasan inda Husna take shi muhsin hukuncin Auren Husna ne da yayi a boye ake mishi izaya da zaman cell kafin ajuyo kanshi don Yana zaton akwai yuwar hada Baki shi da Mai Kano shiyasa yace a kashe Mai Kanon.

Yana kallon Husna dake kallon shi tana zubar HAWAYE sai yaji wani farin ciki ya lullube shi ko Babu komai dama itace kadai a Ran shi sai Kuma gata ya gani.

Su Barrister nura da Ahmed suka kebe suna gaisawa suna jajanta mishi yayin da idon shi ke Kan Husna har dai suka Gane hankalin shi ya tafi kanta su dai Yana Jin su ne Kawai. Nura ya dafa kafadar shi

“Wai wacece waccan ne da kake ta kallo ne ko madam din ce? Ya dubi nuran yana fadin, “Ita ce”.

“Haba Ni na San sai itan Amma Kuma muhsin wane action aka dauka Akan ka ne?

“Barrister Babu wani Abu illah sauraren hukuncin Allah don cas din daga family ya fito.

“Ba zaiyuwu ba muhsin koma daga Ina yake idan har Abun Yana da bukatar gyara Sai akawo shi court kawai don Haka azo court Kawai. Yanzu Bari muje tunda Naga hankalin ka Yana ga madam in yaso zamu dawo gobe da Haka sukayi mishi sallama suna zolayar Husna har suna musu kyautar kudi

Suka tsurawa juna ido inda Amal ke ta gaishe shi Bai ma ji ba sai da Husna tace, “Anty Amal fa na gaishe ka kafin ya juyo Yana duban Amal din,”Yi hakuri my sister banji ba Ina Mami? Mami tana gidan Baba Hassan.

“Gidan baba Hassan Kuma? Tun yaushe? Tun Ranar da yazo ya fiddo ta daga Nan…

Ta kwashe komai ta fada mishi. Ya yi shiru Yana nazari kafin ya maida kallon shi ga Husna.

“Kuka kike darling? Ta saka gefen hijabinta tana Kara goge idonta tana kallon shi.

Ba Dole nake kuka ba abubuwa sunyi min yawa Yaya muhsin Kaine tudun da Zan dafa Kai kuma ga yadda Allah yayi da Kai.

“Kar ki damu ke dai kiyi ta ajeni a zuciyar ki shine kawai fatana don nayi Miki alkawarin Nan da kwana biyu sai na fito dama wadan Nan da suka fita yanzu sune Kawai nake saka Ran zasuyi wani Abu Kuma nasan zasuyi din.

“Allah ya Amince ta fada tana aje mishi ledar da ta siyo mishi shawarma har da gwangwanin maltina da Haka suka fito kamar Kar su Rabu Yana Basu tabbacin zai fito soon.

Umarnin da tsini ya samu daga Alh Aminu na su aika da Mai Kano kiyama shi ya Basu damar tahowa da fatan cika Aikin. Mai kano Yana daure a inda suka daure shi suka Soma kwance shi tsini na fadin. “Yau zaka Gane taurin Kai baida Riba idan kaji hancin ka na tunkuyar bangon kashewa karamin Dan iska da Kai . Haka suka kwance shi tsini na ta zagin shi tamkar zogale. Wasu daga cikin su ne suka dauko shi daukar Cali Cali wasu suka dauko kafafun shi wasu kuma suka Ruko hannuwan shi don baya iya tsayuwa ga daurin da sukayi mishi ga dukan da sukayi mishi lafiya ma Babu ita shiyasa suke ganin Rijiya kawai zasu jefa shi can ya Ida mutuwa ba sai sun wahalar da kwanjin su ba.

Suka fito dashi daga gidan inda suka iske me napep din su ya dauko su suka nufi hanyar da zata sada su da Rijiyar da suka saka shi inda Kuma suka ga motar Yan sanda na biye dasu inda Daya daga cikin su Yake cewa tsini kwalawa ne fa suke biye dasu ai kuwa sukace me napep din ya Kara gudu ai kuwa ya burka suka cilla helux din ma ta Kara gudu sai gasu sun Sha gaban su har sauran kadan Napep din ta daki helux din ai kuwa su tsini suka fice aguje inda Kuma helux din ta bisu aguje me napep da yaga Hala shima sai ya watsar da Mai Kano a bakin titi ya auna aguje don in har ya sake ya SHIGA hannu to shima ba zai Sha ba don Haka ya bace.

Husna da Amal dake tafe a hanya suna fatan kafin jibi Ubangiji ya fito da Yaya muhsin sai Kuma suka ga abinda ya faru da napep da helux har zuwa inda suka watsar da Mai Kano Wanda Rigar shi taja hankalin husna har sun wuce tacewa Amal su dawo ita fa Rigar Wanda aka jefo daga napep din Nan tayi Kama da ta Yaya Mai Kano ai kuwa Amal ta juyo Kan motar suka dawo suna cin burki Abu a wajen gari shiyasa ba kowa ma ya kula da Mai Kano ba suna fitowa kuwa suka ga Mai Kano ne kwance shame shame tamkar marar numfashi ai kuwa suka kwallara Kara a tare suna ihu husna dai na tausayin halin da taga Mai Kano yayin da Amal kuwa kukan shin zai tashi ko kuwa ya mutu?.

<< Hawaye 59Hawaye 61 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×