Skip to content
Part 63 of 63 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

 Muhsin ya karasa gaban gadon Mai Kano Yana ta jera mishi sannu ya Mika mishi hannu Wai suyi musabaha wani matsiyacin fushi ya sauka fuskar Mai Kano kamar ba zai bashi hannun ba ya dai yi ta maza inji mata ya bashi suka gaisa Yana tambayar jikin nashi Amma ban zaci Mai Kano ya amsa ba hakan ya sagewa muhsin gwiwa yayi shiru Yana kallon Mai Kano da ya ke kallon Salma wadda ta dafe Kai ko uhum batacewa kowa ba. Husna da Amal kuwa kowa ya shiga taitayin sa ganin abinda Mai Kano yayiwa muhsin.

Tsit kamar Babu kowa a dakin muhsin ya gaji da ganin Salma cikin halin da take wanda ya fassara mishi komai kenan. Ya Kira sunan ta Salma.

Ta yi firgigit ta juyo tana kallon shi.

“Salma babu gaisuwa ne? Tayi wani murmushi Wanda yafi Kama da Yake masomin kuka.

“Na zaci mun gaisa Yaya Mai Kano ya jikin?

“Na ji sauki ya mutan gidan? Ta Kuma yin murmushi tana fadin, “Suna Nan yadda ka San su halin su Bai canja ba.

Amal da tasaki Baki tana kallon yadda Mai Kano ke fira da Salma don Bata zaci ya iya sakin fuska Haka yayi magana da mace ba macen ma irin Salma da takewa kallon local.

Mai kano yayi murmushi Yana fadin, “To Zan Zo kuwa gidan tunda na San taken gidan
Salma ta dubi Amal tana fadin, “Bamu gaisa ba fa ko?

Ya Mai jikin? Ta amsa Mata da da sauki kafin ta dubi Husna da take aikawa Muhsin wani sako ta ido. “Mrs Juliat ya Mai jiki?

Husna ta juyo tana fadin ga shi Nan ai kin tabbatar…

Muhsin ya gaji da mugun kallon da Mai Kano ke watso mishi ya Mike Yana Fadin

“Allah ya Kara lafiya friend ga wannan sai dai Babu yawa….

“Nagode Amma kaje dashi bana bukata. Wani Abu marar Dadi ya daki zuciyar muhsin har ya koma ya zauna Yana fuskantar Mai Kano.

“Mai kano Wai ko Akwai wani Abu ne bayan Auren mu da Husna ne da nake karbar cin fuska daga gareka irin Haka?

“Kwarai kuwa akwai shi Muhsin Amma ba zakaji komai daga bakina ba ka koma ga mahaifin ku ka tambaye shi wani Abu da Ni na turo ka ya fada maka zaka Fi gamsuwa idan kaji daga gareshi Zan Kuma baka damar yanke hukunci da kanka tsakanin Ni da Ahalin ku don Haka jeka na gode da ziyara ka Kuma yi hakuri da kusanto mu don ina tunawa da abun da Yake faruwa idan na ganka idan Kuma Husna ke sawa kana bibiyar mu ai na fada maka kotu zata raba.

Wani matsiyacin rudu ya ziyarci muhsin da Amal sai Muhsin ya juya ya fita har yakai kofar fita ya juyo Yana kallon Mai kano

“Kayi min Alfarma Naga Husna na minti biyu.

Ya dubi muhsin da wata fuska Yana fadin, “Bakaji abinda nace ba ne? Banajin Zan Kuma yiwa Ahalin ku wata Alfarma guda daya anan Duniya ka fice kawai idan Kuma ka sake dawowa duk abinda nayi maka Kai ka siya.

Idon muhsin ya kada yayi jajir sai kawai ya dawo inda Husna take ya Rada Mata wata magana a kunne ya fice abin shi.

Amal ta sunnar da kanta kasa cikin wani tashin hankali meye ya hada Mai Kano da Daddyn su? Yaci ace itama ta marawa Dan uwan ta baya sun bar Mai kano da Ahalin shi Amma ina ! Zuciyar kauna ta nutse a tafkin kaunar Mai Kano Wanda Bata iya jayayya da umarnin da kaunar shi ta saka ta.

Husna dake Rera kuka tana Jin tamkar ta hadiye zuciya ta huta Amal da Salma suka Rufu akanta suna Bata Baki abinda ya kular da Mai Kano Amma sai zuciyar tausayi ta kwabe shi yayi shiru yana jinta sai kawai ya huce akan Amal.

Ya juyo daga barin da ya mayar da fuskar shi bayan ya gama girbawa muhsin Rashin mutunci ya fuskanto Amal dake Rarrashin Husna.

“Kema ya kamata ki wuce gida Haka Nan zan hado dukkan list din abinda kikayi min na turo akawo Miki har gida na gode sosai.

Amal tayi wani murmushi me tafe da HAWAYE kafin tace,

“Ni Kam bani da zuciya Akan ka Yaya Mai Kano saboda tuni na baka kyautar ta da zaka farke kirjina zaka Tara’s babu komai aciki sai kaunar ka so kayi hakuri Dani bani da zuciya abinda ke tsakanin ka da Daddy Kuma babu Ruwa na dashi in kuwa ka danganta Ni dashi to Allah fa ba zai Bari ba don Haka kar ka kalleni a cikin Ahalin da kake yiwa kiyayya ko zakayi hakan Ni kayi min adalci na Roki Allah idan har zai har ba Zan samu so daga gareka ba to ya datse tsayin kwanaki na a Duniya idan kuwa da Akwai wani Abu da ya shirya a tsakanin mu to ya bani juriyar abinda Zan gani daga gareka…….

“Babu wani Abu da Allah ya shirya a tsakanin mu Kar ma ki yaudari kanki kema Zan Baki sako irin Wanda na bawa yayan ki muhsin kije ki tambayi mahaifin ki me ke tsakani na dashi kema zanyi Miki adalci idan ya sanar dake duk hukuncin da kika yanke zan gode miki.

“Yadda nake jin ka a raina da zuciya ta sai na fi daukar abinda zaka fada min Akan mahaifina da bana zaton zai fada min gaskiya Amma Kai na Roke ka da ka fada min abinda mahaifina yayi maka nayi maka alkawarin kawo gyara don nasan Kai ba zaka boye min ba tunda har ka Fadi Haka tunda ban sani ba sai yanzu da ka fada Amma na tabbatar Daddy ba zai fada min abinda ke tsakanin ku ba matukar ba Mai Dadi bane.

Ta Kare tana jiran ji daga gareshi Amma ya bawa banza ajiyar ta Dole ta gaji da jiran cewar shi tayi shiru cikin dogon tunani. Salma ta Mike tana fadin, “Zan wuce Allah ya Kara lafiya.

Ya Mike daga kwanciyar da Yake Yana fadin, “Bari na Rakaki ko Salma.

Haka kuwa ya biyo bayan Salma Amal na Rako shi da kallon mamaki don ta gama fuskantar Yana nufin Salma Yake so? HAWAYE ya Kuma wanke Mata fuska suka hade Kai ita da Husna da take ta Rera kuka suka ci gaba da shakar abun su.

Da sauri kuma Amal ta mike tana fadin,

“Wallahi sai naje na samu Daddy sai ya fada min abinda yayiwa Yaya Mai Kano.
Ta Suri Jakarta ta fito inda ta hango Mai kano Yana fadawa Salma wata magana da ta nutsar da salmar har tana Rufe fuska da hijabinta abinda Amal ta tabbatar akwai soyayya a tsakanin su tana kallo ya tsaidawa Salma napep ta SHIGA Yana daga Mata hannu har napep din ta auna aguje sai da ta kulewa ganinshi kafin ya koma cikin Asibitin Bai ko kula da Amal ba dake kallon su cikin zubar HAWAYE

Ta SHIGA motar ta jiki a sanyaye tana Kuma hango yadda zatayi da sabon kalubalen da ya Kuma tunkaro ta na kutsen Salma acikin Rayuwar Mai kano da take fatan SHIGA. Kenan yanzu yakin ya koma biyu Haka ta tashi motar ta nufi gidan da fatan samun Daddyn agida.

Alhaji Aminu da ya Kira tsini Yake tambayar ya Aiki ba a samu wata matsala ba dai ko? Tsinin ya sanar dashi abinda ya faru a Ranar.

“Yanzu a Ina me Yake kenan? “A napep muka barshi fa Alh kwalawan Nan na Gane sun Dade suna fakon mu kokon kanmu suka so tarwatse wa muka nuna musu Jan wuya shine fa suka sakar min harsashi a kafa.

“Kai dai mahaukaci ne wallahi tsini Hala kwayar ka ka Sha har hakan ta faru? Yanzu kana nufin shi Mai kanon a napep kuka barshi ko me ye?

“Ni fa ta Raina nake alaji ban San yadda suka Kare ba.

“To ka tabbatar ka saka wadan da zasu Nemo min me napep din da Yake dauke da Mai Kano.

“Kasha kurumin ka alaji dukan da Gayen Nan yasha ba zai tashi ba ko kaji ance ya farko ne?”

“Shiyasa nace Kai mahaukaci ne shi me napep ai ba zai San ba a bukatar Rayuwar yaron ba yanzu idan ya Kai shi ga hukuma fa?”

“Na Rantse maka alaji ba zai taba tashi ba baya da numfashi fa muka fito dashi kafin kwalawan su tado mu ya fa mutu ko za a nemi wani nashi ba yanzu ba sai gawar shi ta gaji da Zama mutuware.

“To ka samu wasu ka saka su binciko mana me Napep din muji inda ya kai gawar.

“Ina da number shi ma bari na kira shi yanzu.

“Yauwa to Kira shi yadda kukayi sai ka fada min inaji ajikina yaron ba zai mutu ba don nafi zaton ya hada jinsi da aljanu.

“Ko aljanin ne alaji Zan Kare mishi gudun maleji in ma Bai mutu ba na Rantse maka da kabarin uwa ta sai na kashe maka shi.

Yanzu kira kaji kome kenan ya datse wayar Yana jiran Kiran tsini sai ga muhsin ya shigo da wata irin dakiya babu tsoro bare shayin Daddyn ya zube Agaban shi Yana mishi wani kallo Mai Kama da tuhuma.

Wayar tsini ta shigo kiran shi ya dauka yana fadin, “Me ya ce ne?

“Wallahi cewa yayi a titi ya zubar dashi an ce Kuma wasu Yan Mata sun dauke shi a motar su.

“Kace dai kawai ya dawo gida? Ya fada da wata murya me amo kafin ya datse Kiran Yana juyowa wurin muhsin Yana mishi wani kallo me kama da Wanda ya kashe maka Dan ka na fari.

“Daddy Kar ka boye min ka fa da min gaskiya meye tsakanin ku da Mai Kano Wanda Yake turo Ni wurinka in tambaya?

“Wane Mai kanon kenan?

“Na gidan marigayi Baba mu azu. Ya fada min baya bukatar mu na Rabar su saboda Kai saboda abinda kayi musu. Daddy Gaya min kawai abinda kayi musu Kar ka boye min don na Rantse maka Daddy ba Zan bar gaban ka ba sai ka fada min abinda kayi mishi. 

<< Hawaye 62

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×