Skip to content
Part 2 of 3 in the Series Ibtissam by Aysha Galadima

ABLA!!! Wacce aka kira da Ablance ta kallesu cikin muryarta da bata fitowa sosai ta soma magana “ Saunawa zan fada muku duk wahalar da zamusha kada mu taba yadda muzubar da mutuncin mu, ya kamata mu yarda da kaddara, kome zasuyi mana mudunga kai wa Allah kukan mu su basu ita su cutar da mu ba , kar na kumajin wata magana irin hakan.” Wacce aka marace ta kara sakin kuka.

“Abla basu da kirki mugayene, idan bamuyi musu abunda sukeso ba zasu cutar da mu“ ya’ken da yafi kuka ciwo Abla ta saki.

“Karki damu Allah na tare damu, nawane kudin naki da ya fadi?“ share hawayenta arwa tayi kafun ta furta “170 ne.“ Kwance gefen dankwalinta Abla tayi taciro wasu matattun kudi, dari da saba’in din ta irga kafun ta bawa Arwa, girgiza mata kai Arwa tayi.

“Abla kinsan matarnan ba mutunci ne garetava in na karbi kudin nan zata gana miki azabane.“ bata kai karshen zancen taba daya daga cikin yan mata ta miko mata kudin da ta kudun dune “ Abla ni ki karbi nawa, ni se ayi mun hukunci”, kafun abla tayi magana ta gefen wacce ta miko kudin itama ta miko mata nata “ abla ki karbi nawa , ni se ayi mun hukunci ba sai anyiwa Anee ba.“

Girgiza musu kai Abla tayi “ karku damu bazan karbi kudin kowa ba , yanxu kunga dare yana karayi in bamuje kun kai mata kudin nan ba zata sa aduke kune, kuzo muje “rungumeta sukai gabaki d’aya su ukun banda ta karshensu da sai faman harararsu take a fakaice, Sarai abla ta ganta shareta kawai tayi, Arwa ce ta kalleta.

“Husna ki taho mutafi mana.“ girgiza mata kai husnan tayi a dan yake ta furta “ ku tafi zan taho daga baya.“ Bata jira cewarsu ba ta bar wajan, guntun tsaki Anee taja “ ni fa shiyasa kwata kwata bana shiga harkar husna, sai kace yar uban shugabankasa mutum sai fadin rai.”

Ta ukunsu ce me suna Ilham ta tabe baki “ matsalarta, ni bazan sawa kaina damuwar ta ba Wallahi”, shiru abla tayi musu dan itama ta fara gajiya da halin husna , a darare suka fara wuce mutanan wajan , Daidai bakin window suka tsaya ,gabaki dayansu tsoran shiga suke, basuyi auneba sukaji an shako rigar abla , da sauri suka juyo, gabaki dayansu razana sukai da ganin UWAR KARUWAI ga wasu mata guda uku a bayanta.

“Tsinannun yara uban me kuka tsaya yi anan, wato kun tsaya muna furcin da kuka saba ko ,zinariyya ku dakko mun su” tana kammala maganarta taja abla kamar wata kayan wanki ga wuyanta da ta shake da kyar take iya shakar nunfashi, Wanda aka kira da zinariyya itama kan Anee ta janyo kafin ta tsinka mata mari tare da janta a kasa kamar kayan wanki, ragowar mata biyun da akallo daya zaka musu kaga manyan karuwai suma haka suka janyo Arwa da ilham, duk inda suka gifta sai dai a kallesu a dunga shewa. Can cikin wani daki da ya cika da tarkacan kwalaye Uwar karuwai ta jefa Abla take a wajan kanta ya bugu da Gini, bata gama shiga a zabar buguwar da tayi ba taji saukar mari dama da haku a kumatunta ,” shegiyar yarinya gwanda inkashe ki in huta babu abunda kuke tsinananun “

Daidai lokacin da ake shigo da su Anee suma, kallansu uwar karuwai tayi gabaki d’aya mummunar fuskarta a hade ta ke binsu da wani mugun kallo, katan hannunta da yaci uban Jan farce ta miko musu ba tare da ta furta komai ba , da Sauri gabaki dayansu suka saka mata kudadan hannunsu banda abla dake nishin azaba.

“Ku d’auke su anan “ cewar uwar karuwai, ba musu kuwa suka d’auke su gabaki dayansu kukan da sukai ya bata musu fuska . Kallan ta uwar karuwai tayi ,”ina kudin ki” cikin dishashewar murya abla ta furta “ sun fadi”, bata Kai karshen zancan taba uwar karuwai ta hanbare mata baki take a Wajan bakinta ya fashe.

“Bansan asara ba , sannan bana daukar asara ,duk acikin yaran da nake hulda dasu kece tsagerarsu, in baki sani ba na tuna miki , ke din ba kowa bace face baiwa da ko dabba ta fiki gata , rayuwarki tana hannuna sai yanda nayi dake tukunna, dan haka ko kina so ko ba kyaso dole kiyi karuwanci ki kawo mun kudi.” tana gama zancanta ta kwallawa zinariya kira.“ ki kai ta dakin shirgincan, ki tabbata bata samu abunda zata kwanta ko lulluba akai ba ,abude winduna yanda sauraye zasu shiga ciki, banaso kuma naga kaske na yawa a ciki.“

Wani shu’umun murmushi zinariya ta saki kafin ta ja abla data gama galabaita zuwa wani dakin shirgi da ko mara gata sai haka , gabaki d’aya dakin dattine a cikinsa ga uban shirgin kaya a ciki sai faman wari yake , kamar yanda uwar karuwai ta umar ta haka zinariya tayi kafun ta kalli abla cikin lashe baki “ ki bani kanki kawai na dan dana zumarki, zansa uwar karuwai tayi miki sassauci.“ Ta karasa zancanta zata taba abla, cikin wani irin zabura abla ta hankade hannunta , gabaki d’aya ta gama galabaita.

“Karki sake kazamin hannunki ya kuskura ya taba fatar jikina, ta Allah ba taku ba kuma mugaye azzalumai, kamar yanda kuke kokarin cutar damu insha Allahu munfi karfinku“ Shake mata wuya zinariya tayi “ kar kiga ina binki ta lallami, ko kina so ko bakyaso sai kinzama mallakina, sai na dunga jin dadinki.“

Tana kai karshen maganarta tasaki wuyan Abla, sai alokacin wani irin tsoro da firgici ya kama Abla ganin zinariya na kokarin barin dakin, bata gama shiga cikin firgicin ba zinariya ta kashe fitilar wajan tare da kullo ‘kofa. Cikin fita hayyaci abla ta soma magana.

“A’a , A’a , ku budeni, banaso Wayyo ku budeni, duhu banasan duhu , duhu zasu kamani bana so , ku bude mun kofa , ku bude mun kofa. “ A haukace ta soma dukan inda take tana kiran su bude ta , kara ta soma saki kafun ta fara dukan kanta kamar wata tababbiya.

“Dan Allah ku bud’eni bana san duhu” yadda nunfas yake sama da kasa kamar xai fita daga cikin jikinta, gabaki d’aya jikinta rawa yake take a wajan ta fara shakuwa kafun nunfashinta ya dauke gabaki d’aya a wajan.

New York, Fifth Avenue

8:15pm Little ne zaune kan daya daga cikin rantsatstsun designer cushions din falon , hannun sa dauke da system dinsa dayake game, Prince na gefensa dauke da waya shima, fitowar wannan black American dattijon da Akalla zaiyi shekara 50 a duniya ne yasa Little ajje system dinsa.

“Uncle Iron man ,” murmushi mutumin yasakar masa “ Na’am uncle little “, ba little ba hatta Prince dariyar kalmar uncle Little din daya fada suka saki , ganin lokaci na tafiya ne yasashi kallansu “ lokacin dinner yayi , let’s go and eat “, kashe system din sa little yayi kafun ya mike tsaye, “bari na kira yaya BOBO.”

Gyada masa kai sukai kafin su nufi wani rantsatstsan dinning , da in aka bar mutum bazai taba gajiya da kallan sa ba, iya haduwa dinning din ya hadu , ga wasu set din dinning daya ‘kara fito da haduwar wajan, kan d’aya daga cikin kujerun da mutane goma zasu zauna suka zauna batare da sunyi magana ba.

A sama kuwa direct wani irin corridor Little ya nufa, yanda tsarin corrider din yake shikadai ya isa kallo, wani door me dan tsaho ya nufa kafun ya tura kofar babban door din, kayataccen falo ne me shegen girma duk da bai kai girman falon kasa ba , iya tsaruwa da haduwa falon yayi , wani kamshi turare ne ke tashi a cikin dakin ga sanyin falon da ya cika ko ina, ganin babu kowa a cikin falon ne yasa shi nufar d’aya daga cikin doors din kofar.

Astagfirullah ya Allah , babban daki ne me shegen kyau a wajan, komai na cikin dakin brown colour ne , ga wani dan ubansun king sized bed me shegen girma da daukan ido, iya haduwa da tsaruwa dakin yayi kamar ba ‘a anfani dashi, shiga cikin d’akin little yayi bakinsa dauke da sallama, babu kowa a d’akin har ya juya zai fita wata ran tsartsiyar waya ta fara haske alamun kira ya shigo ciki, ganin yaya bobo baya d’akin yasa shima ya share zai fita ,sai kuma ya ‘kara dawowa cikin sauri zai dauki wayar aka turo wata kofa dake cikin dakin.

Fuska a hade BOBO ya kalleshi babu alamun fara’a akan fuskarsa, “ what are you doing here “, rawa bakin little ya fara , kamar me ‘kin’kina ya furta “ Na dauka Yaya ne”, sakin fuskarshi bobo yayi kafun ya karaso inda yake “ you’re very stubborn little, gwanda yayan naka ya dawo ko kashiga taitayinka“ zaro masa ido little yayi zai marairai ce masa bobo ya harareshi,” my phone”, da Sauri Adil ya mika masa wayar, wata number bobo ya danna, kusan ringing biyu ba a dauka kiran ba, ana ukunne yaga kiran number ,da sallama abakinsa bobo yayi magana , shiru kusan tsawan mintuna biyu banji me akace masa sai kallan Adil da yayi “ your stubborn brother ya dameni, talk to him”, yana kammala zancan sa bobo ya mika masa wayar da sauri Adeel ya kar’bi wayar har wani dariya dariya na kwace masa “ Yaya big boss,“ ya fada kamar me rada banji me aka ce masa ba sai kallan bobo da yayi kafun a shagwabe ya furta.

“Sorry yaya Assalamu alaikum,” kusan mintuna daya kafun ya furta “Yaushe zaka dawo yaya nayi missing dinka, gidan ya rage dadi fa” kallanshi bobo yayi alamun zaka sani, ga baki d’aya Adil ya manta bobo na kusa dashi, gyada kan da Adil yayi ne yasa bobo gyara tsayuwar sa.

“Eh fa yaya ,yau graduation dina amma kaga yaya bobo yayi punishing dina , Kai nake jira ka dawo karamamun”, bai kara zancansa ba yaga bobo na dage masa gira ,”Innalillahi wa’inna ilaihi raji’una, na mutu na lalace yaya bobo daman kana nan.”

Kit aka kashe kiran daga can ‘barin, gyara tsayuwarsa bobo yayi “ ina punishing dinka ko, come over here , zo nan”, zaro masa ido Adil yayi “ Haba yaya bobo na kasan ina sanka , I’m sorry kaji “, not accepted cewar bobo, ja da baya little ya fara yana kokarin guduwa, hannu bobo yasa zai janyosa yayi saurin zillewa , cikin dariya ya furta “ nifa bazan bari ka kamani ba yaya bobo, nace fa ina sanka me and you one heart ne.“

Harararsa bobo yayi, ”come over here,“ nace fa sorry yaya bobo, kace idan mutum yayi lefi kuma ya bada hakuri anaso mutum ya dunga yafiya”, murmushi bobo ya saki da yayi wa kyakkyawar fuskarsa kyau “ ni zakayiwa siyasa“, girgixa masa kai little yayi “ yaya nifa yunwa nake ji , kuma kai kadai nazo na kira kaji yayana , I love you “, gyada masa kai bobo yayi “ok let’s go”, da Sauri kuwa little ya karasa wajan bobon, be auneba yaji bobo ya kama kunnansa, saurin dafe kunnan little yayi , cikin dan kara ya furta “zafi yaya kunnena “ da sauri bobo ya saki kunnan nasa “inane yake maka zafi?”

Kunnan little ya nuna masa,”it’s ok zea dena” kama hannunsa little yayi“ yaya bobo, kayi mun alkawari fa ranar graduation dina zaka goyani“ kallansa bobo yayi “ as big as you are zan goyaka , so kake ka karyani”, shiru little yayi masa har ya kama tafiya bobo ya riko hannunsa “ hau mu tafi , kafin ka hana mu bacci “, da sauri kuwa little ya d’ane bayan bobo, har suka sakko falourn kasa Adil na bayan bobo kamar wani karamun yaro, murmushi uncle iron man ya saki, shi kuma prince girgiza kansa kawai yayi , “ sorry uncle iron man, sorry yaya Prince dina “, hararar sa Prince yayi , tun dazu yake jin yunwa da yake Adil dan iskan yarone ya barsa yana faman shiri rita, waje bobo da little suka samu kafin Prince ya danna wani button, cikin seconds din da bazea wuce d’aya ba wani soja ya shigo cikin falon, sara musu yayi kafun ya fara tanbayarsu abinda za a yi serving Dinsu, kowa fadar ra’ayinshi ya ke banda bobo da little ya zabar masa , yazo zea tafi Adil ya sakar masa murmushi “Thank you uncle James,“ shima Wanda aka kira da james din murmushi ya sakar wa Adil kafun ya kara sara musu ya bar wajan.

Tunda suka soma cin abinci babu Wanda yace da wani kala har saida suka kammala cin abincin su, basu kara 50 minutes a falon ba kowa ya nufi bedroom dinsa. Karfe 2 da rabi Bobo ya fito daga part dinshi , direct dakin su Adil ya nufa ganin ko wannansu yayi bacci, gyara musu kwanciya yayi kamar wasu yara kafun ya kara yi musu addua ya totto fa musu, iya dum light ya bari a dakin kafun ya fito, haske kad’an ne a falon amma duk da haka sosai falourn ya kara kayatuwa,sai da ya zagaya ko ina na falourn kafun ya fito waje , awajan ma fitulu ne masu haske kamar rana da suka kara haska kyan gidan, sojojine birjik a tsakar gidan tare da wasu manya manyan karan sojoji da suke shawagi a wajan, duk inda ya gifta sai an sara masa, saida ya tabbatar da lapiyar kowa kafun ya koma part dinshi.

Washe Gari

Washe gari ana kiran sallah asuba wata iriyar jiniya ta karade ko ina nagidan , gabaki d’aya kowana mahaluki na gidan ya tashi banda Prince da Adil da suke baccinsu,
Akaro na biyu Jiniyar ta karayin ‘karar da bata kai ta farko ba, pillow Prince ya dauka ya toshe kun nuwansa dashi tare da kara janyo blanket yana rufe har fuskarsa, Adil ma baccinsa yake hankali kwance, A hankali aka tura kofar d’akin, bakowa bane face bobo dake tsaye abakin kofa, hasken d’akin ya kunna kafun ya karasa inda Adil yake “ Adil!!! Get up lokacin sallah yayi”, ko motsi Adil beyiba, shafa gashin kansa bobo yayi “ get up now ,ok”, dan motsi Adil yayi kafun ya soma karanto adduar Tashi daga bacci a hankali, karasawa wajan Prince Bobo yayi , shima kiran sunansa yayi, amma ko gezau beyi ba, kara kiran sunan shi yayi akaro na biyu sai wani pillow da ya dauko zai toshe kunnensa, 2 fingers dinsa bobo kawai yasa ya dakawa Prince duka a gefen hannunsa, azabure Prince ya furta “ su wanene suke shirin yin yaki”, be karasa zancan saba yaga bobo tsaye a kansa, ga Adil dake faman kumshe dariyarsa.

“Just 5 minutes na baku, if you like ku koma and see”, yana kammala zancansa ya bar dakin, bashiri kuwa sukai brush da Alwala ko wanka basu tsaya yi ba , a ‘kasa suka tarar da bobo da uncle iron man , gabaki d’aya masallacin dake cikin gidan suka nufa, sojojine suma cike a wajan suna jiransu, musulman ciki suka shiga masallaci, ragowar kuma suka fara motsa jiki.

Ana idar da sallah kowa ya koma masaukinsa, su Prince ma basu tsaya a falour ba suka nufi d’akunansu , Prince ya zo zai kwanta Adil ya tsayar dashi,”yaya Prince kasan yaya bobo yana jiran muko , wallahi ka koma bacci babu ruwana kasan babu abunda zai hana a nunka maka wani motsa jikin”, yana kammala maganarsa ya shigo toilet, tsaki Prince ya ja kamar yayi kuka , Adil na fitowa shima ya shiga wankan, shaf shaf suka shirya cikin kayan motsa jiki, a tsaye suka tarar da bobo shima da nasa kayan motsa jikin , sa’banin nasu shi kayan motsa jikin sojojine a jikinsa, sakkowa sukayi inda yake kafun su sara masa” Salute”, shima hannunsa daya ya d’aga batare da ya sara musu ba ya furta “salute, kun ‘kara 2 minutes Menene hukuncinku “, gabaki dayansu sakin baki sukayi suna kallansa “ Yaya” eyes dinsa ya zuba musu , gabaki d’aya saurin sunkuyar da kai sukai kamar abun tausayi,girgiza kai kawai yayi “ let’s go” wata iriyar ajiyar zuciya suka sauke gabaki dayan su, cikin d’an gudu gudu suka fara tafiya , suna fitowa harabar gabaki d’aya sojojin suka sara wa Bobo kafun su hada baki wajan furta “Salute” hannu ya daga musu, kafun su Prince su fara motsa jiki , sai da sukayi 2 hours suna motsa jiki kafun su koma part Dinsu.

9:30am James ya serving Dinsu breakfast , Tunda suka fara Breakfast gabaki d’aya babu Wanda yayi magana saida suka kammala.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.6 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ibtissam 1Ibtissam 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×