Bissimillah
Gida ne matsakaichi ne mai kyau kana kallon gidan zaka san gidan me rufin asiri ne dai-dai gwargwado.
Ikram ! Ikram bazaki fito na kaiku Makaranta ba duk yaran nan sai sun riga ki fitowa.
Gani nan ta fito tana ta sauri yarinya ce baza tafi shekara 16 to 17 ba kyakyawar gaske ce irin matan nan matsakaita tsayi ce ga diri tubarkallah.
Kafin ta shiga motar yace" dakata Ikram kin san Allah , idan har biki abun arziki a neco da waec din nan ba kina kalo zan biya wa hafsat kudi ta tafi kara tu kasar waje ta. . .