Haka suka tafi da yake basu da nisa da masallacin suna tafiya yana gaisawa da mutane kowa ya gansu sai sun burge shi .
Haka sukayi suka dawo yace "su dau hotan tarihi" .
Aikuwa ya dinga daukarsu kuma sunyi matukar kyau Musa ya shigo yace "yawwa karbi ka daukemu; Mu biyu" ya nuna masa yadda zaiyi ita dai tana tajin kunya ya riketa suka dinga bada style a karshe suka zauna suna ta dariya .
Musa ma Haidar yace "bari na dauke ka kai ma" san nan ta zuba masa abinci ya tafi .
Haka suka sha bikin Sallah su cikin farin ciki. . .