Da kyar Haidar ya rarrasheta bayan tafiyar Abdul.
Abdul ma duk jinkin shi yayi sanyi ya koma gida Daddyn su na waje suna hira damai gadin su yace daga ina kake Abdul sai yanzu ?" Ya dan sosa kai yace" Daddy na ɗanyi ziyara ne shiyasa na jima ".
Gir-giza kai kawai Daddyn yayi san nan Abdul ya wuce .
Haka rayuwa ta cigaba a gidan Daddy da kuma gidan Ikram.
Zuwa yanzu Momi ta kwantar da hankalinta suna waya jefi- jefi da Ikram.
Najwa da Abdul tuni sun koma makaranta.
Rayuwa ta cigaba a ɗan kwanaki da sattitikan da suke zuwa. . .