Ikram ta dawo ta shirin dora girkin dare dan da ta dawo Haidar ya fita ta kammala komai bayan isha Haidar yadawo yace "ina ta jiran naji an koromin ke har na gaji na fita" ta kwada masa harara tace "zan rama kuma Yaya".
Suka zauna ta bashi labarin Momi tace "zata zo harda su Abba da Al'amin".
Yayi murna sosai yace "kinga gurin zai karayin albarka kenan" tace "gaskiya dai" ya kira Abbansa suka sha hira dashi dan yanzu Ikram jitake kamar babanta ne dan ya dauke mata rashin Daddyn ta , dan shi mutum ne mai kulawa da. . .