Ikram na kallon yaranta tana farin ciki sosai .
Abba da Haidar suka shigo, bayan sun gaisa Haidar yake ce ma ta ' wannan likitar mahaifiyata ce".
Nan ya bata labarin gamuwar su da Mami sanadin haihuwar Ikram din.
Tayi farin ciki sosai ta tayashi murna .
Basu jima ba sai ga Mamin tazo ta zauna ta gaida Abban Haidar cikin mutunci.
Haidar ya gaisheta cikin kulawa ta ɗago ta dubesu tace" ina so muyi magana yanzu tunda yarinyata taji sauki sosai hankulan mu sun samu nutsuwa".
Abban Haidar yace " tom bisimillah.."
Tayi ajiyar zuciya tace" Haidar ka yafemin dan Allah ban manta. . .