Duka dakin guda biyu yayi mata gado ,sai kujerunta a Parlour.Kitchen ma ba laifi sai kujerun dining mai hudu, gidan yayi kyau sosai dan shi kansa haidar bai taba tunanin zai samu matar da za,ai mata wannan gatan ba tunda shi ba mai kudi ba ne.
Sai dai fa tun da akawo kayan amarya dangin Ikram suka san ta shigo dan gin miji masu wahalar sha'ani .
Ko da aka kawo amarya sai dai da aka rakata zuwa ɗakin Gwaggo ta kallesu shekeke ta ce "Allah ya basu zaman lafiya" daga nan aka kaita ban garanta da yake. . .