Tana fita ta cewa Haidar" mu tafi "tayi gaba Haidar jikinsa yayi sanyi duk rawar jikin nan da take da haka zasu saka mata kumar cincin din ya gani yana so yace me yasa bata ajiye ba haka kurum yaji yana jin nauyin hakan .
Mai Napep ya tsayar musu suka shiga tana kuka dole yasa hannusa ya riko nata yana dan matsawa alamar tayi shiru tayi hakuri, ba tace da shi komai ba har suka zo gida yace" ki shiga sai na dawo suna ta damuna da yawa" daga masa kai kawai tayi ta fita taje ciki ta bude ta. . .