Skip to content
Part 3 of 3 in the Series Indo A Birni by Rasheedat Usman

Taɓa bakin ta indo tayi tace, “Wannan Azzalumin ne ya Tanimu, yamin haka da baki Kuma wlh na rantse da Allah sai na bawa tumakin sa maganin ɓera sunci sun mutu, badai shi azzalumi ba Wlh sai ya gwammace bai taɓa ni ba.” Zaro idon sa, Mustapha yayi yace “Ke mahaukaciya, yanzu idan aka barki sai ki kashe masa tumaki, dake kema tinkiyar ce, hankalin ku ɗaya da tumakin, amma dai Allah ya Kawo Miki shiriya, dan wlh iyayen ki suna fama da ɓakin cikin ki, sai dai Allah ya basu hakurin zama dake.”

Yana gama faɗin haka ya buɗe motar sa da niyar shiga, indo tayi carap tace “Dan Allah ya Mustapha karka tafi wallahi ban gaji da ganin ka ba.” Tsuka Mustapha yaja tare da shigewa motar sa, yaja da ƙarfi, duk ya bule Indo da ƙura, bin motar Indo tayi da gudu tana cewa “Ya Mustapha ka tsaya dan Allah na manta bance maka kifiyar Sonka ta soke ni a ƙirji na ba, wallahi ina Sonka sosai har cikin ƙahon Zuciyata.” Shi kam Mustapha baima san tana yiba, dan tuni ya yi gaba Abinsa, juyawa Indo tayi Ranta a haɗe, cikin takaicin tafiyar Mustapha, gashi wannan zuwan da ya yi basu wani haɗu sosai ba, dawa Allah zai haɗa Indo idan ba Zainabu ba, can ta hango Zainabu tsaye ita da Hansai suna zance, lallaɓawa Indo tayi yanda Zainabu bazata ganta ba, bare ta gudu, ita ko Zainabu sam bata wani lura da Indo ba sai ji tayi an tsakomo ta.

Ware idonta Hansai tayi cikin jin tausayin Zainabu “Uban waye na kama dan kutumar ubanki, ƴar durun uwa, da kin zata kin tsokaneni a banza ne, to wlh yau na lahira saiya fiki jin daɗi.” Ƙoƙarin kwacewa Zainabu take hanun Indo sai dai ina Indo tafi ƙarfin ta, dukan Zainabu Indo take tsakanin ta da Allah, yayin da ta wurgar ta kasa, ta ɗane ruwan cikin ta, sai dukan bakin ta take tana cewa “Dan ubanki akanki zan huce haushina na yau, gobe Uwar ki Hali zata ƙara zuwa gidan mu kai ƙarata, na kuma ƙara tareki naci ubanki, karku fasa karna fasa, muga nida ku waye zai gaji.” Sannan ta sauƙa daga ruwan cikin Zainabu. Harara ta zabgawa Hansai tace “Ke kuma matsa ki bani waje, kema kinyi Sa’a, wallahi da Mai Gari ya kama Baba na, da kema naci naki uban.”

Ita dai Hansai bata kula Indo, ba har tayi tafiyar ta. Hansai ce tace “Ki tashi kiyi hakuri, kema Zainabu meya kaiki tsokanar Indo, kinsan dai Indo tafi ƙarfin ki, maza ma yaya suka ƙare da ita bare kuma ke.” Kuka Zainabu tasa, cikin jin haushin dukan da Indo tayi mata, Rabuwa sukayi da Hansai kowa ya kama hanyar gidan su.

Da kuka Zainabu ta ƙarasa wajen Goggo Hali “Lafiya Zainabu meya same ki, zaki shigo min gida da kuka.” cewar goggo Hali “Ba Indo bace, ta kama ni da duka, wai gobe ma ki ƙara kai ƙaranta gidan su, itama ta ƙara kamani da duka.” Sallallami Goggo Hali ta ɗauka, sannan tace “Kinga Zainabu ki haƙura ki bar Indo da Allah domin kuwa Indo shaiɗaniya ce, Babu mai iyawa da ita sai Allah.” Tura baki Zainabu tayi tace “To Allah ya isa na wallahi.” Goggo Hali tace “Shikenan zai kuma isar Miki.”

Misalin ƙarfe Uku na Rana Mustapha ya shigo cikin dutse, Shango Estate na gani Rubuce a mashigar Inda zai shiga, gidaje ne da yawa cikin Estate ɗin, wani gida mai shegen kyau naga Mustapha ya shiga, yara biyu ya samu a compaunt ɗin gidan suna ƙwallo, da gudu yaran suka taho wajen sa, suna Oyoyo yaya Mustapha, parking ɗinsa ya gyara, sannan ya fito yana dariya, ɗaya bayan ɗaya Mustapha ya ɗaga su yana cewa “Autan Momy, yau Babu islamiyya ne, na ganku a gida.” Sharif ne yace “Babu yaya, malamin namu baban sa ya mutu, wai sai anyi Uku mu dawo.” Mustapha cikin jimami yace “Ayya Allah ya jiƙansa da rahama, ina Momy? Ishaq ne yace “Tana ciki yaya, Aunty RAUDA ma tazo jiya take tambayan ka, Momy tace, ka tafi ƙauye wajen Hajiya Innah.” Mustapha ya taɓe bakinsa yace “Sannun ta da zuwa to.” Ya yi maganar yana kama hannunsu suka ƙarasa makeken falon, wanda ya tsaru da Adon pink da purple, falon yayi kyau sosai, idan ka ɗaga kanka sama kuma, tozali zakayi da wani ƙaton Elagement, Kama ce tsantsan tsakanin su kamar a raba ruwa biyu, haka suke, basu da wani banbanci, koda ta yatsa ne, gefe ɗaya anyi Rubutu da manyan baƙi, *MUHAMMAD MUSTAPHA AND MUHAMMAD HABEEB*, sai kuma gefe duka Family ɗin gidan, wata kyakkyawar mata na gani fara sol daga ganin ta kasan bafulatanar Asali ce, sai wani Dattijo shima kyakkyawa wankan tarwaɗa, sai kuma wata yarinya ƙarama, da kuma ƴan biyun ta Hudu Habeeb Mustapha sai Sharif da Ishaq. Muryar Momy yaji a bayan sa tana cewa “Mustapha yaushe ka shigo?.” Murmurshi ya yi yace “Yanzun nan shigowa ta, na same ku lafiya.” Momy tayi murmushi “Lafiya lau ya Hajiyan ka barta?”

“Tana lfy sai darun tsufa ni wallahi Momy na gaji da zuwa wannan ƙauyen gaskiya, Daddy ya daina tura ni, kullum naje ƙauyen nan da ciwon kai nake dawowa.” Murmurshi Momy tayi tace “Mustapha idan bakaje ba waye zaije, kasan dai Sharifa bazata iya zuwa ita kaɗai ba haka kuma Sharif da Ishaq sunyi ƙanƙanta, Habeeb kuma baya ƙasar ma gaba ɗaya, tunda kaine babba, ai dole kuma kaje ka.” RAUDA ce ta fito daga kitchen ɗin Momy hanun ta riƙe da cooler, dariya tayi tare da cewa yaya Mustapha sannu da dawowa, Haɗa Ransa Mustapha yayi, yace “Yawwa sannu.” tare da kawar da kansa gefe Jikin RAUDA ne yayi sanyi ganin irin amsar da Mustapha ya bata cikin hadewar fuska, gashi ita kuma Allah ya ɗaura ma ta jarabawar soyayyar sa, amma sam Mustapha baya sake mata fiska Asali ma idan tana waje bai cika zama ba, ta rasa Meye aibun ta da Mustapha ke gudun ta. Shigewa tayi, daining ta ajiye, foodplast ɗin dake hanun ta, ta ƙara komawa kitchen ɗin domin kwaso sauran Abincin. Shigewa ɗakin sa yayi, ba tare daya ƙara wata magana ba. Ran Momy sam baiyi daɗi ba, domin kuwa bata jin daɗin abunda Mustapha ke yiwa RAUDA, gashi ita kuma tana da burin ganin sun haɗa kansu kodan ƙudirin dake ranta na Son haɗa su, Aure. RAUDA jikin ta a sanyaye tace “Momy na haɗa komai a daining bari na shiga ɗakin ya Mustapha, na share masa.” Da To Momy amsa sannan ta haura sama ita kuma RAUDA tayi ɗakin Mustapha. Fitowar shi kenan daga tollet, ɗaure da towel, a ƙugun sa, yaga mutum Zaune gefen gadon sa, ta ƙurawa pic ɗinsu shida Habeeb ido. Tsuka yaja mai ƙarfi wanda ya dawo da RAUDA cikin hankalin ta cikin tsawa yace ma ta “Kee! Me kike nema a nan?.” Ya jefo mata tambaya “Babu komai, daman ɗakin zan gyara maka sannan na sanar da kai, Food is ready.” Tayi maganar cikin sanyin jiki “Na gode to amma sharar bana buƙata, abinci kuma na ƙoshi, kina iya tafiya.” Cikin marairaice wa tace “But amma ya Mustapha…” Da katar da ita Mustapha yayi ta hanyar cewa “Sorry Please leave me alone, kaina ciwo yake ina buƙatar hutu.” Cikowa idon RAUDA ya yi da hawaye Cikin tausayin kanta na rashin adalcin da zuciyarta ta ma ta, ta sanyata Son Maso wani.

<< Indo A Birni 2

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×