Skip to content
Part 5 of 6 in the Series Izina by Matar Sadiq

Aisha POV.
Cikin shigar riga da skit na atamafa super ta shirya me launin ja da adon blue, kalloh daya zakai -wa atamfar ka gano irin tsananin tsadarta, jace atamfar mai mai manyan patan wanda aka musu ado da launi blue, hannunta rik’e yake da k’aramar jakarta ta rataya-wa itama blue. mayafin-tama blue ne, wanda hakan ba k’aramin fitowa da asalin sihirtaccen kyau da tsarin surar da allah ya-bata yayi ba, musamman tsananin farar fatar ta tamkar wacce bata ta’ba shiga rana ba, gashin kanta kuwa abun sha’awa ne ga kowanne Namiji da mace, tsayin-sa da tsananin laushin-sa tare da bakin kalarsa tamkar wata balarabiya ko ba’indiya.. bakinta d’an karamine wanda kalarsa ta sirka da pinck color idanuwanta kwa manyane farare masu kalar madara, tana da oily eyes wanda a nesa kana iya hango wani haske da maik’o acikin idanuwanta. a kukusa kuwa tamkar hawaye ne ya kwanta. hmm abun-abum burgewa. tana da zarazaran gashin ido dana gira tare da kwantacciyar suma a saman goshin-ta , sannan tana da matsakaici diri tare da tsawo. Hmm Aisha de ta ko’ina ta cika a kirata mace, hakan-ma kyakkyawar mace wanda kyau ya ratsa gaba da bayan-ta, tana da sanyin hali da sanyin murya, amma idan ‘bangaran shari’a ne, sai ka rantse ba wanda yakai-ta magana a duniya.

Cikin takunta me cike da nutsuwa, ta k’araso kusa dashi, k’amshin daddad’an turarenta ya shak’a hakan yasa shi ajiye aikin laptop din nashi ya juyo, wani abune yaji ya tsarga masa har-jinin jikinsa saboda tunda yake a rayuwa bai ta’ba cin karo da macen da-ta ja ra’ayinsa ba kamar ma’isha.

A hankali ya d’aura idonsa cikin lafiyayyun idanuwanta masu kamar madara, da sauri ya sauk’e idanuwansa, saboda yanda idanuwanta suka had’u cikin nasa, duk iya rayuwar da ya-yi a india bai ta’ba ganin mai kyawun idanuwan ma’isha ba.

Dakyar ya iya saita dukkanin nutsuwarsa, cikin lallausar muryar-sa yace, kin shirya?
Murmushin tayi tare da cewa, hmm ai bana-wasa inde ta ‘bangaran aikina ne!!
“Da kyau!

“kin sanar da mami akan cewar zamu-fita tare dake?”

“A hankali ta juya kwayar idanuwanta, kafin tace eh tasan da fitar-mu..
Mik’ewa ya-yi shima farar shaddah ce maitukar kyau da tsada a jikinsa, driver-n’ na hango-su ya tashi motar, tare da zagayo-wa ya bud’e musu murfin motar
Motace k’atuwa mai kyau da tsada k’irar luxury car bak’a.
kai-tsaye cikin wata unguwa ta masu k’aramin karfi motar ta kutsa, duk da bawan-da yasan gidan amma shi drivern ya-sani da yake shi mayar da matar gidan-ta daga cikin asibiti.

Cikin fara’a dattijuwar ta kar’besu, duk alamu sun-nuna basa cikin yanayi na dad’i
Tabarma ta shimfid’a musu tare da k’atuwar garduma, wacce da alamu-ma sabuwa ce,
“acikin d’an wani k’ok’o ta kawo musu ruwa, ma’aisha ce kawai tasha.

“Saida suka nutsu daga bisani, suka gaisa” aisha ce ta tambayi ina yariyar take, tana d’aki ta bata amsa.

Da sauri ta mik’e ta nufi d’akin da yarinyar take, matashiyar budurwa ce wacce bazata wuce sa’arta ba, saide wahala kawai da ta ramar da ita.

A kwance take tana kallon-sama idanuwanta taf da kwallah, kusa da ita ta zauna, cikin lallausar muryar tace sunana Aisha ni barrister ce mai kare hakkin-mata wanda aka zalunce-su ta hanyar fyad’e.

“Stop her crying” sam kuka bai dace dake ba.”

Cikin muryar kuka tace, hmm yazan-yi idan banyi kuka ba? “wannan itace kad’ai hanyar da nake samun sassaucin rad’ad’in dake cikin zuciyata. bani da wata makama idan ba wannan kukan ba.

Kuka bashi-ne mafita agare ki ba, nima irin wannan matsalar ta faru.. shuru tayi ba tare da-ta k’arasa maganar ba!

Kiyi hakuri ki daina wannan kukan mara amfani, ki sanar-dani, abun da suka faru?.
Kona fad’a miki, bazamu iya-yin komaiba saboda bamu da k’arfin arzikin da zamu tsaya shari’a dashi.

“Am ummita ki daina sa wannan a ranki, “but” banzo nan domin ku-biyani wani abu na tsaya muku bisa shari’a ba, In-fact idan nazo nan dan ku-biyani kud’in shari’a, nima bazan fara ba, saboda yanayin k’arfin-ku.

“Daidai lokacin Malik suka shigo d’akin, shida mahaifiyar ummita!!, cike da tausayawa ya kalli fuskar “ummitan” ya kauda kai!,

Cikin kulawa ya maida kallonsa zuwa-ga mahaifiyar ummita, cikin nutsuwa yace, umma kun-de shigar da k’arar kamar yanda na fad’a-muku ko?

Eh nashigar yaro!

Is okay, wannan itace yarinyar da zata tsaya muku a kutu, kuma in-sha allah gobe zamu-je da ita domin ta gabatar da kanta a matsayin lauyar da zata tsaya muku.
“But I have to know” musan wanene ake k’arar domin ita a bata damar fara bincike akansa!!, suna address d’insa, sana’arsa, da inda yake zaune!

Toh sunan-mahaifinsa de, alhaji mustapha wada giwa!! tsofan Senator
shi-kuma yaron sunan-sa “ANWAR” kuma yaron d’an gata-ne sosai
“Da sauri, Aisha ta mik’e cikin tashin hankali, tace “what alhaji mustapha wada giwa, wanne daga ciki?

“Wannan de mai-manyan company’s d’in nan?

“Dama tun farko umma nasanar dake baza-su iya ba, dama can talaka bai ta’ba yin shari’a dashi yaci riba ba.

“Da kuma na fad’a maka sunan shi tun farko da ba’ai karar-sa ba.

“Shut up” Umma ba haka bane. I am coming back!

Tana fad’in haka ta mik’e, hankalin-ta a tashe ta nufi mota!!
“Shima mik’ewa yayi tare da bin bayan-ta.
“Aisha lafiya kuwa, what happen? a kawai matsala ne?
“Yaya dan allah ka shigo mu-tafi, zan maka bayani daga baya!

Cike da tsananin mamaki ya shiga motar shikuma driver-n yaja motar suka tafi.

“Yaya tabbas akwai babbar matsala, wannan’ wanda ya aikata laifin d’an gidan babban aminin daddy ne, kuma mai-gidan daddy ne!

Dogon tsaki ya-jahh tare da cewa to sai-me idan mai-gidan daddy ne!!, kina nufin bazaki amshi wannan k’arar ba?

A’a ba haka nake nufi ba, ina tsoran fushin daddy?” bazan bari ya gano kece zaki tsaya akan wannan shari’ar ba!

“Kallonsa tayi, irin wannan kallon na mekake nufi?

“Kai ya jinjina mata alamar eh” koda ace daddy ne ya aikata wannan laifin, to tabbas shari’a sai tayi aiki akansa!!, kuma bazan bari kowa ya tsaya ba, fa-ce ke?

“kuma wllh sai an gurfanar dashi a gaban shari’a.. kimun alk’awari baza-ki ta’ba ajiye wannan aikin ba koda daddy ya-sani?

“I promise” in-sha allah, saboda na riga nayi rantsuwa da alkur’ani zanyi aiki bisa gaskiya da amana ko da akan kaina ne?

Murmushi yayi cike da jin dad’i yace na gode, ni-kuma zanyi k’okari domin naga na tallafa miki.

“Na gode sosai”

kai tsaye babbar kutun ya biya da ita, domin gabatar da kanta, basu-wani ‘bata lokaci a wurin ba abun ka da babbar lauya mai zaman-kanta a wurin, saida drivern ya biya ta gida ya sauk’e Mu’isha daga bisani ya wuce da malik zuwa wurin aikinsa.

“tun daga nesa ya fara hango sauran ‘yan jaridan da suke zaune zaman jiran-sa.
Fitowa yayi daga cikin motar, nan take jami’an dake wurin suka fara masa gaisuwar ban girma.

Har yazo zai ra’ba ta tsakaninsu ya wuce wani daga cikin (jonalist d’in ya dakatar dashi, cikin dagun murya mai sauti.

“Yalla’bai!! Yalla’bai!! ko zaka iya fad’awa mutane wani sahihin bayani, kuka samu dangane da mutuwar maigirma commissioner.

“Har yanzun bamu samu wani gamshashshen bayani ko hujjah wacce zata nuna mana mu tuhumi wani ko wata dangane da mutuwar maigirma G. I. G ba?”

“Yalla’bai amma an-ce kwararrene amma ya akai haka?”

“Bazan-ce komaiba batun kwarewa ko rashin kwarewa, ai nasara daga Allah ne..”
“Hakane yalla’bai amma ai da jajircewar jami’i ma.”

“Eh hakane amma kusani jiya-jiyan nan na sauk’a acikin wannan garin, bamu-fara gudanar da bincike ba, amma da yardar allah zamuyi nasara?”

“Amma duk da haka al’umma suna so suji daga gare ka, wane k’warin gwiwa kake dashi, akan damk’e wanda ya aikata laifun, kuma taya-ya zaka gano shi?”

“Wannan aikin bincike ne zai tabbatar da hakan, maganar ta ina zamu kama-shi wannan sirri-ne, ko nace allah shi zai toni Asirinsa.”

“Munji labarin kai haifafan garin nigeria ne, wannan gaskiya ne ko ba gaskiya bane?”

“Eh wannan gaskiya-ne amma a’halina ba’a nan suke rayuwa ba.”

Yana fad’in haka, ya juya, sauran ‘yan-jaridun suka-k’arayin kansa, nan take jami’an suka kewaye su.

“A fusace ya juyo ya fuskanci Ma’aruf, cikin had’e rai yace,

“Ma’aruf ban yarda a k’ara barin wani d’an-jarida ya k’ara zuwa nan ba matuk’ar bani na buk’aci hakan ba.”

“An-gama yalla’bai.”

Har ya juya zai-tafi, yace,

“Ma’aruf.”

“Na’am Yalla’bai!”

“Bana-so kowa yasan inda ‘yan uwa a nan garin, saboda rayuwar-su zata iya fuskantar had’ari.”

“Toh yalla’bai.”

“A kiyaye!”

“Ka turomun da Faruq Ahamad yanzun-nan.”

“Cike da hanzari ya fita, cikin k’an-k’anin lokaci, suka dawo tare. Batare da ya d’ago kai ya kallesu-ba yace,

“Mun shirya fita club daga k’afe sha-d’aya na dare zuwa k’arfe d’aya na dare, daga kai sai ma’aruf nake-so mu fita, ku tabbatar kun shirya kafin lokacin, ban buk’aci kowa yazo mun da kayan aiki ba, pasinal dress nake buk’atar gani a jikin-ku. bana buk’atar kowa yasan da fitar-mu yau, komai ya-tafi in secret”

“To yalla’bai!! zaku iya tafiya..”

Anwar POV.

Yarone matashi kyakkyawa, d’an zamani, farine sosai amma ba over ba, domin ya had’une da najin dad’i, sanye yake da riga da wando trequater’ farar T-shirt da blue d’in wado, zaune yake gaban k’aton swimming pool wanda aka k’awata gaban shi da jajayen furanni kala-kala.

A hankali ya mik’a hannunsa sama k’aton table d’in ya d’auki glass cup d’in wanda aka sanya coconut milk juice a cikin-sa.

A hankali ya fara shan coconut milk d’in, dai-dai lokacin screen d’in wayarsa tayi haske alamar kira-text massage ya shigo.

“Dan ƙaramin tsuka yaja haɗi da d’aukan wayar,, pretty shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, picking call ɗin yayi haɗi da kara wayar akan kunnensa batare da yace komaiba, cikin wata irin shaiɗaniyar muryarta, tace “Hello Baby !! ɗan ƙaramin murmushi yayi haɗe dacewa “Ya’akayi ne pretty ?” jin abun daya fad’i ya-sanya ta sake gyara zama haɗe da ƙara kashe murya tace ” Ina guest house ɗinka pls Baby kazo. “

Okay ” yafaɗa a taƙaice haɗe da kashe wayar.

Wata haɗaɗɗiyar Blue car yashiga haɗe da bata wuta yafice daga cikin gidan…..

Kaitsaye wata k’atuwar unguwa ya nufa inda nan-ne guest house ɗinshi yake, yana zuwa maigadi ya wangale masa gate ya-cusa motar tasa ciki.

Tun-daga ciki yake jiyowa sautin yanda kid’a ke tashi daga cikin k’aton falon, kai-tsaye ya kutsa cikin tafkeken falon, wa’iya zubillah tarin ‘yan-matane da samari gaba d’ayan-su baza-su wuce sa’o’in juna ba. kowacce acikin su manne-take da jikin saurayin-ta, suna aikata masha’a, ta gefe guda-kuwa kayan ciye-ciyene da shaye-shaye, kama daga kan lemo juice zuwa kwalaban shaye-shaye.

Wata guda d’aya daga gefe wacce ta ware kanta da alamu itace pretty-n da-sukai waya da anwar. suna ganin-sa dukkanin-su suka nutsu.

Da sauri ta mik’e fuskarta d’auke da murmushi tayi saurin shigewa jikinsa
Cikin rashin shakka ko tsoran allah ya k’ara nutsata cikin k’irjinsa.

“Oh baby gaskiya nayi missig d’inka, rabon da na-ganka tun da safe, nashiga damuwa sosai.

Murmushi yayi tare da cewa, ahh pretty yanzun ba gani ba!!, me kike-so ayi?

‘Kara kan-kame-shi tayi a jikinta tare da cewa, abun da aka . saba?”

“Really?”

“Yeah I really”

Cikin jin dad’i ya d’aga ta cid’ak ya nufi wani sashi da ita, tun daga falo zaka iya jiyo sautin masha’ar da suke aikatawa. wa’iya zubillah.

Sun shafe sama da awa biyu kafin suka-fito rik’e da hannayen juna.

“Bai ‘bata awa d’aya da fitowa ba, ya nufi hanyar komawa gida tamkar dama abun da ya-kawoshi kenan!

By Matar Sadiq

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Izina 4Izina 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×