Ɗage kafaɗa Jay yayi irin ko a jikina ɗin nan, yace "uban masu jin kai ai wallahi tun wuri ka rage wannan ji da kan ko kuwa kasha wahala a hannun 'yar mutane don na tabbata za'a wahalar da kai kamun a baka haɗin kai kuma kai kaja, sannan za ta qeraka staff ka shiga hankalin ka dan mata dai sun wuce duk tunaninka a seta maza duk mulkinka a waje a gida sune masu mulkin ƴan aljanna ba Allah dai ya qarawa mata albarka da ni'ima mu kuma ya qara mana qarfin kwasan ni'iman. . .