Afrah qasa tayi da kanta ta qarisa cikin palourn wanda shima Farooq idon sa ke kanta yana danne dariyan sa dan yasan bata san me ya kawo sa gidan ba.
Qarisowa palourn tayi ta durqusa ta gaishe shi sannan tayi wa big bro sannu da dawowa.
Jay yace "yauwa qawar qwailar budurwata".
Afrah tura baki tayi tare da yin qasa da kanta duk a tunaninta ba wanda yasan abinda ta faɗa bata san Jay kam ya jima da juyewa malam ba-wasa.
Afreen tura qofan palourn nasu tayi ta shiga da sallama, ganinsa yana zaune yana danna waya sai. . .