Skip to content
Part 15 of 15 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Afrah qasa tayi da kanta ta qarisa cikin palourn wanda shima Farooq idon sa ke kanta yana danne dariyan sa dan yasan bata san me ya kawo sa gidan ba.

Qarisowa palourn tayi ta durqusa ta gaishe shi sannan tayi wa big bro sannu da dawowa.

Jay yace “yauwa qawar qwailar budurwata”.

Afrah tura baki tayi tare da yin qasa da kanta duk a tunaninta ba wanda yasan abinda ta faɗa bata san Jay kam ya jima da juyewa malam ba-wasa.

Afreen tura qofan palourn nasu tayi ta shiga da sallama, ganinsa yana zaune yana danna waya sai taji sanyi a ranta ta qarisa ciki zuciyanta na dukan uku-uku dan kuwa tasan halin sa sarai.

Tun shigowanta yaji mostinta har qarosowan da tayi palourn da kuma idanuwan da ta zuba masa duk yana sane amma sai ya basar.

“Darling kayi haquri da halin Hajja” ba tare da yace komai ba ya lumshe idon sa gami da jinginar da kansa a jikin kujeran da yake zaune, yana sauqe ajiyan zuciya.

Haquri taci gaba da bashi tare da masa sannu da zuwa amma ko kallonta bai yi ba balle ya tanka mata, har sai da ta yi addu’an Allah bayyana Ammi kamun cikin sanyi ya buɗe bakin sa yace “Ameen ya Hayyu ya Qayyum” iyaka abinda ya faɗa kenan ya kuma rufe bakinsa gum kai kace baya magana.

Hajja da sallama ta shigo, inda ta hange sa zaune ta nufa tana faɗin “Malam Muhammad Mufaddal, yaro mai sunan larabawa, babban mutum a daina fushi da Amarya mana”.

Tun shigowan stohuwar yaji ransa na qara ɓaci, duk surutun ta kuwa bai ko haɗa shi da qasa ba, sai ma earpiece nasa da ya maida kunne.

Zama tayi gefensa tace “haba Angon Hajja mijin Hajiya fushi kake da Amaryan ka?

Duk surutun Hajja ko kallonta bai yi ba bare kuwa ya kai ga mata magana dan DMD sosai yake da zuciya ga rashin son surutu, amma kuma bashi da riqo.

Hajja rarràshi tayi kaman wacce ke rarràshin yaron goye amma ko kulata yaqi yi sai da qyar kamun ya buɗe baki yace “Hajja komai za kuce ku daina sako Ammi ba ruwanta ba abinda ta sani”.

Hajja jin ta samu ya kulata ai cikin kwantar da murya ta ce “ai ni tsakanina da Maimuna baiwar Allah sai addu’a da fatan alkairi barin ma dai da ta haifamun ku, karka damu an daina Angon Hajja, amma kai ma ka dubi girman Allah da Manzon sa ka rage wannan halin naka”.

Sai lokacin yayi ajiyan zuciya yace “kuma kiwa yaronki ma magana komai za suyi shi da matarsa su daina sako Ammi kowa ya staya iya mastayinsa ya zauna iya mazaunin sa”.

“Ai karka damu tsaff na ɗauki mataki na gama dan na sani Rabi’atu cikakkiyar munafuka ce ga kirsa, ai ita abin nata ma yayi yawa yo gaki ba kyau ba ga kuma munafurci, kuma fa damuwan ta duka dan bata haihu bane, ai ni nagode wa Allah da ban haɗa jini da ita ba, kaikam kayi haquri ko Allah ya bayyana maimuna”.

“Ameen” ya faɗa a taqaice yana miqewa zai fice a sashin, da Hajja da Afreen duka miqewa suka yi suka bi bayansa.

Motansa ya shiga ya zauna ya mata key kamun ya juyo a daqile yace wa Afreen “ki gayawa Jay na tafi”.

Hajja salati tayi kawai ta tafa hannu dan ita tama rasa irin zuciyan wannan jikan nata ko na uban wa ya ɗauko oho, ubansa Mustapha nada zuciya amma ba irin wannan baqar cin rai ɗin ba “to Allah ya shirya” ta faɗa tana shigewa sashin ta.

Afreen kaman za tayi kuka haka tabi bayan Hajja bayan taga fitan motan sa, sosai take mugun sonsa amma ko kallo bata ishe sa ba, ta rasa ta ina ma zata fara ɓullo wa ta nuna tana sonsa kuma gashi ba wanda yake saurara balle ta sama da maganan “Allah dawo dake lafiya Ammi nasan kece kawai zaki mallaka min masoyin raina” cewar ta tana shigewa palourn.

Jay na jin dirin motan DMD nan suka fito shi da Farooq, kusan karo da Afreen suka yi nan ta faɗa musu abinda yace, tana gama magana ta qarisa ta ciki dan lallashin kanta, su kuma suka shige nasu motan.

Jay yaje ya ajiye Farooq sannan shima ya kamo hanyan komawa cikin Gombe.

Anci hutun qarshen mako an suɗe amma har yanzu qafan Innai bai warke ba har da ɗingishi take yi, baabaa da idanuwanta ke kan Innai da tayi hanyan banɗaki girgiza kai tayi tace “Allah Ubangiji ya yaye wa ɗan mutum jarababben raki da son jiki irin naki takwara, dan kekam abun sun taru sun miki yawa, kece qan-jiki kuma kece raki to wai ma ta ina ciwo zai sake ki in ya kama ki? Ai ranar da za ki haihu akwai kwasan ƴan kallo, Allah dai ya kawo miki da sauqi ya yaye miki, amma tabbas duk shawaragin mijin da ya aureki takwara sai dai a bisa da kondunan haƙuri cikin akori-kura, yarinya gaba-ɗaya kaman wacce nono bai isheta ba, uhmñ ni Allah na tuba ai ma nonon ba isanki yayi ba babu laifinki Allah shiryi uwaki Indo”.

Har Innai ta fito banɗaki baabaa na kan mita, kallonta baabaa tayi tace “wai yau har rana ta fito gasto-gasto kina ta yan-yana qafa halan baza ki bokokon ba?

Innai zama tayi gefen baabaa tana faɗin “washh! Qafata, baabaa sai jibi za muje makarantan yau da gobe babu”.

“Uwar masu sakalci yanzu wannan ɗan tafiyan shine har da wani washh, na washo miki kan baabaarki Indo, ‘yar shawaragin buhun uba”.

Duk tsawon kwanakin nan da duk abunda ya samu Innai har taji sauqi Inna ko sau ɗaya bata taɓa gwada ce mata sannu ko ya jiki ba, tun Baffai na fushi har ya gaji ya sauqo yana bin ta da addu’an Allah kyauta dan ya tabbatar lamarin Inna sai a hankali, tun yarinya na stumman goyo har ta girma ta zama budurwa amma babu soyayya da kulawan mahaifiya, sai dai ya qudure a ransa tabbas zai ɗauki mataki kuma itama Baabaa Mero tana nata shirin daban, don abun ya kai su bango zuba mata ido da suke yi shi ne laifin su.

A ɓangaren DMD kuwa zuwa yanzu ko magana baya yi da Abiy akan abinda Aunty Amarya ta faɗa wa Abiy, wanda saura kaɗan Abiy ya stine masa Daddy ne ya taka masa burki, sai Hajja da tace ya dai bincika dan zai yiwu sharrin Rabi’atu ne ko kuwa gaskiyanta fitsaran shi yaron ne.

DMD dai duk zuba musu idanuwa yayi yana kallon su dan shi damuwansa Ammin sa, in ta dawo duk zai koma kan maganan ya ɗau mataki dan ya fahimci matar Abiy na buqatan qarin hankali.

Su sweerie sun gama fahimtan Amminsu ɓacewa tayi kawai Abiy lallaɓasu yayi.

sweetie kuwa kukan yau daban na gobe daban kullum dai ita Ammin ta, gashi Darling tunda ya kawo su bai dawo ba har dai yau da ya kama Monday.

Hajja zaune da jikokin nata a palour, sweetie ke kukan darun da ta saba “Ammiiii naaah! Wayyo Ammiii naaaah! Whmmmmm!…. Ammiiii….” Kuka take da gasken-gaske dan har muryanta ya dishe.

Sweerie tashuwa tayi taje gefen sweetie ta zauna, idanuwan ta cike da qwalla tace ” Muheebbah please kibar kukan nan haka za kisa Ammi yin shaquwa kiyi haquri kinji zata dawo” ta faɗa tana qoqarin jawo ta jikin ta, amma sweetie sai ta zille tana kan kuka tana qiran sunan Ammin ta.

Sweerie ganin haka sai itama ta fara hawayen, Afrah dake kallon su itama kukan ta kama dan sosai take son sweetie bata son ganin ta cikin damuwa balle kuma sweerie abokiyar ta, Hajja da ta cika tayi fam kaman ta fashe cikin jin haushin kukan nasu tace “Wai nikam ance muku uwar taku mutuwa tayi ne? Kun maida mun gida gidan makoki to bazai saɓu ba, ubanku yazo ya ɗauke ku ya maida ku gidan sa dan wannan kukan mutuwan ba’a gidan Fatuma ba”.

“Eh ɗinnn an…an..anyi kuuu kann.. ai dan ke maaa..maaaan..kii bata duniya shiyasaaaa.. Wayyo Allah na Ammi na!” Sweetie ta faɗa cikin kuka.

“Eh lallai kukan munafurci kike yi muhibba, yau dan staɓar carbin fistaranki a cike yake ni zaki cewa Uwata ta mutu? Yau dama uwar waye ba zata mutu ba, Uwar kowa ma sai ta mutu dan haka zaku barmin gida na bana uwaku ba, yarinya qarama sai cikakken rashin kunya, waye baisan haquri ba inbanda rashin hankali da ke damunki”.

Sweedy da ke zaune gefe damuwa ya taru ya mata yawa ga kukan sweetie da yake ci mata zuciya ga kuma labarin Ammi shiru sannan Darling tunda ya kawo su bai waiwayo su ba.

Afreen da ta shigo palourn yanzu wajan sweedy ta nufa tana faɗin “lafiya da tagumi? Cikin harshen turanci.

Sweedy kaman mai shirin kuka tace “komai ma ba lafiya ba ni banma san ya zanyi ba wallahi gaba ɗaya duniyan tamun zafi, gashi layina na Nigeria na nemeshi na rasa Darling bai zo ba bai neme mu ba”.

Hajja da take ta aikin hararan sweedy tace “ai dole duniya ta miki zafi tunda a bakin kura kuke, shi yayan naku ai stakar dokan daji ya aje ku dole kice bai waiwayo ku ba, ooh ni fatuma na shiga aljanna na kasa fita wai yau ace jikoki na neman maida ni zabiya ko stigai rana tsaka abinda banyi tun tale-tale ba sai yau rana tsaka, gaba ɗaya jikoki sunbi sun buwaye ni”.

Sweedy ko kallon Hajja bata yi ba balle ta mata magana dan ita bata cika hayaniya ba, indai stiwa kake so to ka samu sweerie ko sweetie dan halin DMD da sweedy ba banbanci basuson yawan magana.

Afreen da idanuwanta ke kan sweedy tace “yanzu ki amshi wayata ki qira Darling inyaso sai ya rarrashi sweetie da kansa, zuwa gobe sai mu nemo miki layi”.

Murmushi Kawai sweedy tayi bata ce komai ba ta amshi wayan tayi dialing layin Darling, ganin sunan da Afreen tayi saving sai abun ya sanya ta murmusa sosai har fararen haqoranta suka bayyana tace “Wow! Sunan yayi daɗi ina aure haka zan dinga qiran mijina da shi Insha Allahu”.

Ta qira yakai sau 3 bai ɗauka ba sai kawai ta tura message ta rungume wayan a qirjinta idanuwanta akan su sweetie.

DMD dake zaune gaban Daddy kansa a qasa yana sauraran faɗan da Daddy ke masa sai jin qira ya shigo wayan sa yayi, bai kalli wayanba balle ya duba har akayi qira uku duk suka kaste, Daddy yace “son ba qiranka ake yi bane?

Ya buɗe baki zai yi magana sai yaji shigowan message, ɗaukan wayan yayi ya duba ganin abinda aka tura sai kawai ya lumshe ido ya aje wayan yayi shiru.

Daddy ganin haka sai yaci gaba da maganan sa “son shi fa mahaifinka ne, baka da kaman shi ko madadin sa a duniyar ka, ka daina gaba da mahaifinka akan abinda bai taka kara ya karya ba dan nasan baka mari Rabi’atu ba”.

DMD dai kansa a qasa baice uffan ba har Daddy ya gama, godiya kawai ya masa ya tashi ya fice a palourn yana ciro wayan sa dan qiran qannensa.

Mummy da kallo tabi sa har ya fita kamun ta sauqe ajiyan zuciya tace “gaskiya lamarin Mufaddal sai addu’a, Rabi’atu bata kyauta ba haka shima Abiy bai kyauta ba duk da yaron sa ne amma kuma Mufaddal bai yi dai-dai ba akan ɗauke yiwa mahaifinsa magana, Ammi shiru ba labarin ta shi Abiy da kuke tare ai sai ku dage ku rabu lafiya da shi”.

“Ai ni rasa abun faɗa nake habibty addu’a na kawai Allah dawo da Maimuna lafiya dan har da rashin ta ya qara ta’azzara wasu abubuwan a halayyar sa duk da dama dai Mufaddal bauɗaɗɗen mutum ne” cewar Daddy yana ciro wayan sa dake qara a aljihu.

Sweedy na zaune riqe da waya shiru tana tunani kawai ta ji qaran shigowan qira har sai da ta razana, ganin Darling ne mai qira sai ta ɗauka ta kara a kunne “Hello”.

Cikin Yaren Indianci ya mata magana a ɗaya ɓangaren “Sweedy ya aka yi?

“Darling, sweetie kuka sweerie kuka ni na rasa ya zanyi sunqi bari na naji da abu guda ɗaya ga layina na Nigeria ya ɓata”.

Ajiyan zuciya ya sauqe yace “kuyi haquri Ammi ta kusa dawowa in Allah ya yarda, sa wayan a handsfree”.

Sawa tayi a handsfree kaman yanda ya umurce ta cikin yaren hindi.

“Sweetyn Ammi kukan me kuke?

Sweetie da ke aikin ajiyan zuciya jin muryan Darling da sauri ta fara magana da Indianci cikin dashashshiyar muryanta “Darling, Abiy yace Ammi na gida amma munje gida ba Ammi sai yace kuna tare a gidan Hajja, mun ganka ka kuma kawo mu gidan Hajja yau kwanmu 4 ba Ammi bamu ganta ba kuma Hajja tace Ammin mu ta ɓace”.

Dafe kai kawai DMD yayi jin irin surutun da take korowa bata ko jan numfashi ga kuma ciwon kai dake kan addaban sa “sweetie kina ji ba, to kuyi haquri ba yau Monday ba to Ammi zata dawo ranan Thursday kinji ki dena kuka kiyi shiru okay”.

Sweetie tura baki tayi kaman tana gaban sa tace “Darling kai kuma yaushe za kazo to nayi missing naka kuma Abiy ma yaqi zuwa”.

Busar da iska yayi kamun cikin gajiya da magana yace “zanzo Wednesday” kittt ya kashe wayan, yana qarisawa wajan da ya Parker motansa ya fice yayi wajan Jay dake asibiti.

Yana isa direct office na Jay ya nufa, qwanqwasa qofa yayi nan aka basa daman shiga, ya tura qofan ta shiga ko kallon Jay bai yi ba ya nufi wani qofa ya tura ya shiga, Wow! Kai ka ce ɗakin wata Amarya ne dan kuwa kujeru ne set guda ga kuma fridge ga kuma wani madaidaicin gado a gefe.

Jay buɗe qofan yayi ya shigo, ganin DMD akan dogon kujera mai ɗaukan mutum uku sai ya qarisa ya zauna akan 1seater yana faɗin “dude lafiya kuwa?

“Normal” abunda ya faɗa kenan a taqaice yana mai lumshe ido.

Murmushi Jay yayi sanin stokana zai yi, sai yace “dude ko dai abun ta mosta ne?

Wani banzan kallo DMD ya wasta masa sannan ya kuma maida idon sa ya kulle.

“Dude in abun ne in nemo magani ko kuma na qira maka ɗaya daga Nurses namu” ya faɗa yana danne dariyan sa dan yasan tabbas ya nemo magana.

Tashuwa zaune DMD yayi rai a ɓace kaman wanda aka stare da bindiga dai yayi maganan ya ce “Jay kasan bana son maganan banza ko? In abinda kake yi kenan ance maka ni kai ne da ko wacce qazamar zata taɓa? Mind ur word’s, u know i hate this, mutum ko da yaushe ba shi da magana sai na mata to za su kashe ka, in kuma batun magani ne kai ka sani na fika sanin maganin mastalata dan kai ne babban ciwo na, mutum kullum surutu ka dinga saka mun headache, ina barin Nigeria ciwo na ya warke” faɗin Darling yana komawa ya kwanta.

Jay dariya yayi dan ko kaɗan kalaman DMD basu damesa ba “dude nima dai saurayine gal a leda kaman kai…” Knocking da ake wa qofan office nasa shi ya sanya shi miqewa ya fice dan dama akwai patient nasa da ya tura yin scanning su dawo.

DMD gyara kwanciyan sa yayi ya lumshe ido dan bacci yake buqata ko kansa zai yi masa daidai.

<< Jahilci Ko Al’ada 14

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×