Skip to content
Part 24 of 24 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Hajja ce ta tura qofan ɗakin Afrah ta shiga tana faɗin “wai Fatuma yau ba za ki je…” Maganan ta kasa qarisawa kawai ta sanya salati “La’ilaha illallahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, ni jikar mutum huɗu me zan gani? Fatu baccin asara kuke yi tun ɗazu dama baki shirya ba kin biyewa Munawwaratu ita da ba uwar inda za ta leqa ko qofa ta-kashi, to tashi kamun na qira Nura yanzunnan” ta faɗa tare da zubawa Afrah bugu a cinya.

Afrah kaman za tayi kuka ta tashi dan ita sam duk ta mance yau Wednesday ne suna da school, sauqa tayi a gadon tana qunquni “ni wallahi na manta yau akwai makaranta kuma yanzu lokaci ya tafi ko naje nasan duka na za’a yi, ni ba inda zanje” ta faɗa tana shigewa toilet.

Taɓe baki Hajja tayi sannan ta juya ta fice a ɗakin tana cewa “sai kinje dan uban wani ne ya sanya ki yin bacci ko stabar samun waje wai karuwa da sallahn walha, to za ki fito ki tafi kuma yanzunnan zan qira Nura na sani shi ne dai-dai da ke ‘yar fatarin uba ta renani ina takwararta”, Hajja ɗakinta ta shige ta samu sweetie na game na maciji a Nokianta, zama tayi tana faɗin “ƙawar Hajja kamomin layin baffanki Nura dan in bai stawatar wa wannan sakalalliyan ba nasan ba inda za taje yaran zamani duk idanuwanku a tsai-staye kun fistare qafafuwanku bakwajin maganan kowa sai na iyayenku dan carɓin rashin ta idonku kun cike shi cass, mu a zamaninmu ai ko kakar kishiyar maƙociyar goggon mai anguwan garin su pendon uwar ubanka ce ta maka magana tsaff muke biyayya amma ku yaran yanzu sai addu’an shiriya domin wasu yaranma ko na iyayensun basa ji, to Alhamdulillahi tunda kunajin nasu Allah ya muku albarka ya shirye ku”.

Sweetie jin lissafin kalen dangi da Hajja ta surfa ai sai ta dinga tiqa dariya kaman za tayi kuka har sai da Hajja ta dundeta kamun ta tsagaita ta qira mata layin Daddy, yana shiga ya kashe ya qira ta miqawa Hajja ta cigaba da dariyanta.

“Nura ka qira yarinyarka yanzunnan ta shirya ta tafi makaranta ko na mata rashin kirki” faɗin Hajja cikin faɗa ko gaisuwan da Daddy ke mata bata amsa ba.

Daddy haquri ya bawa Hajja sannan ya gaisheta ta amsa suka yi sallama ta kashe wayan tana faɗin “Muheebbah kekuma taho mu karya”.

Sweetie tana dariya ta shirya tsaff suka fito da Hajja suka zauna dinning da aka gama jera kayan kari, ba jimawa sai ga sweedy ta fito, ta gaishe da Hajja itama ta zauna suna Indianci da sweetie.

Afrah wasta ruwa tayi ta fito ta shirya sama-sama ta juya zata fita qira ya shigo wayanta, tana ji tasan Daddy ne kaman za tayi kuka ta ɗauka dan bata isa taqi ɗauka ba.

“Hello! Daddy good morning”.

Daddy a ɗaya ɓangaren jinjina kai kawai yayi yana addu’an shiriya ga yaran nasu ya ce “Afrah morning daga ina? Har yanzu kina zaune baki tafi ba kina sane da exam’s za kuyi nan da kwanaki ko, ki fita idona Afrah maza-maza ki shirya ki tafi kar na saɓa miki”.

Kaman za tayi kuka ta ce “kayi haquri Daddy na gama shiryawa yanzu zan tafi”.

“Good a dawo lafiya kuma a mayar da hankali ayi karatu”.

Sallama tayi da Daddy ta kalli sweerie da ke shiryawa ta ce “sistor na tafi makaranta jaraba kai da hutawa sai ka mutu, kai ni Allah bani miji nayi aure na huta kuma Allah yasa ya ce bazan cigaba ba dan sai nafi murna, kuma Allah ko su Aunty Afreen ba suyi aure ba yin abuna zan yi tunda dai ban hanasu ba bari Allah ya bani miji kugani har Hajja sai tasha mamaki” ta faɗa tana ficewa a ɗakin.

Sweerie dariya ta dinga yi har ta kammala shirin ba jimawa itama tabi bayan Afrah.

Bakin nan a gaba an cunnon sa aka fito tana ta harare-harare, hanyan waje ta nufa za ta fice sai Hajja ta tsayar da ita “yunwa ba baffanki Mustapha bane dan haka sai kinsa abu a cikinki za ki tafi, ba zaki jawa mutane ja’iba cuta bayan rai ba, ulcer ta kamaki ki tashi hankalinmu” cewar Hajja tana wastawa Afrah harara.

Sweetie miqewa tayi cikin shagwaɓa ta ce “Aunty masoyiya zan biki school naku nima sai na tayaki karatu”.

Afrah da ta haɗa fiska jin abinda sweetie ta faɗa sai ta kama dariya tana faɗin “mintin zuciya dama ana raka mutum makaranta ne? Kiyi haƙuri yanzu zan dawo ba zan jima ba kinji”.

Sweetie bubbuga ƙafa ta kama yi tana kukan rigima ita sai ta bi Afrah, sweedy gajiya tayi da jin hayaniyan gashi ana ɓatawa Afrah lokaci dan zuwa yanzu kamun ta isa ma tayi latti, stawa sweedy ta dakawa sweetie akan in bata daina ba zata haɗata da Darling, qin yin shiru tayi, Afrah sama-sama tasha tea ta kama hannun sweetie ta ce “mu tafi in aka dakemu tare kin huta dan nayi latti” suka fice a Palourn sun samu driver na jiran Afrah kawai suka shiga ya ja su sau school.

Hajja da kallo ta bisu har suka fice a palourn sannan ta yi magana “gaskiya ni fatuma ina ganin abubuwa iri da kala, duk jikoki ace babu na yasarwa amma guda na Allah da Manzonsa mai jin magana kawai ke ce Muhseena sai dama-dama Jabiru, to ni mai zan ce in ba addu’a da fatan shiriya gareku ba, Allah rufa muku asiri kar jikokinku su muku abinda kuka min dan na tabbata sai kun haukace, yaran wannan zamanin ma ya aka qare balle na wani zamani, to Allah ka kyauta ka shirya mana zuri’a alfarman Annabi Muhammad SAW, Ameen”.

Sweedy murmushi tayi itama ta amsa da “Ameen Hajja tamu”.

Sweerie zama tayi tana gaishe da Hajja, sai Hajja ta haɗe fiska taƙi amsawa, sweerie dai abun dariya ya bata sai ta gaishe da sweedy da Indianci tana tambaya Afreen, Hajja ce ta ce “yara gaba da baya kun rungume harcen Hindu kunqi na ubanku, ko wa ya faɗa muku haka akeyi oho muku ku kuka jiyo ai, inbaku koya ba ma ku ta mastewa, ke kuma wato na ɓata rai ban amsaba shi ne ba za ki tambayi laifinki ba kika gaisheda yayarki kika bawa banza ajiyana, to a kunnen Mustapha tunda baccin asara da mutuwan rai kuke yi har kun ja Fatu na ta makara, aka taɓa ta akanki zan rama mata”.

Sweerie murmushi tayi ta ce “Allah huci zuciyan Hajja tamu ta malam muhammadu, Allah baki haquri”.

Hararanta tayi ta ce “in Allah ya bani haqurin sai ki ƙwace, dan tsabar lalacewan zamani ace da asuban farko ki kama qiran sunan bawan Allah yana kwance makwancinsa cikin rahamar Ubangiji nasan yanzu haka kin kora sallahn asuba da ya kai masa ziyara ja’ira”.

Duk dariya suka sanya, sai ga Afreen ta fito tana faɗin “a wani islamiyyan aka faɗa miki haka Hajja?

“A islamiyyan uwaki Maryam da ubanki Nura tunda ke saboda balagan rashin jinki sai yanzu kike fitowa kuma ba gaisuwa kike stomo baki cikin zance na da jikokina”.

Afreen taɓe baki tayi ta zauna sweerie ta gaisheta sannan ta haɗa shayinta tana korawa, buɗe kulolin tayi ganin abinda yake ciki ta ɓata fiska ta ce “ɗumamen tuwo sai kace muna cikin daji gaskiya yau zan koma abun ya isheni”.

Hajja guntun tsaki taja ta ce “Nura ma da ɗumame ya ci ya girma har ya auro Maryam ta haiho ki, ki koma dama ba wanda ya gayyato ki ke kika kawo kanki neman wajan zama, ‘yar kalen dangin stiya”.

Afreen bata kuma cewa komai ba ta cigaba da lasta wayanta, sweedy ma shirun tayi dan kaman ma hankalinta baya wajan sai sweerie da ke aikin dariyan surutun Hajja.

Hajja miqewa tayi bayan ta wanke hannu ta wuce ta zauna a kujerun palourn tana faɗin ” ‘yan banzan sai yaushe za su sakawa mutane vidiyon masu karairaye jiki kaman ba qashi ne da su ba (kung-fu China Film🤣).

Innai suna isowa da Rabe Allah ya taimaketa ana assembly tukun ba’a fara tare latti ba, hamdala tayi ta shige makarantan cike da ɗaukin son ganin Afrah, dan kaman fushi take da ita rabuwansu na qarshe.

Layin ‘yan ajinsu ss1 taje ta staya tana ta kan leqe-leqen ta ina zata hango Afrah dan bata kalleta ba, wata Malama ce ta masta alama da ta nustu daga wajan stayuwan malamai, sai na daina leqe-leqen tana Allah-Allah a kammala taga Afrahnta.

Har aka gama assembly, aka yi inspection bata ga Afrah ba, itama Allah ne ya taimaketa da an doke ta dan anbada style ranan bata zo ba bata da lafiya, aka gama aka sallami ɗalibai kowa ya kama hanyan ajinsu, sai lokacin ta tabbatar Afrah bata iso ba dan leqawa ta dinga yi ba ita har suka isa aji kowa ya samu wajan zamansa ya zauna, ba jimawa Malam ba wasa ya shigo.

Afrah tun daga mota take aikin yarfe hannu da ta tambayi driver ya faɗa mata time dan ta tabbatar yau ta kaɗe har hanjinta, sweetie sai surutunta take yi ita kaɗai Afrah tunaninta na kan lattin da tayi, suna isowa kuwa lokacin angama wastewa a assembly kowa ya tafi aji, tun daga bakin gate take hango ‘yan latti, kaman za ta zura a guje haka take ji, driver ya sauqesu ta kama hannun sweetie suka shige, fiska tayi suka yi hanyan class amma discipline Master ya daka mata stawa ya stayar da su, Afrah jikinta na ɓari suka dawo wajan suka bi layin tare lattin, sweetie ce tayi magana qasa-qasa “Aunty masoyiya mukam ba’a dukanmu latti a Canada ki ce Darling ya maidake school namu na Canada”.

Afrah kaman za ta yi kuka itama qasa-qasa ta ce “mintin zuciya kibar magana za mu ƙara laifi”.

Sweetie shiru tayi tana dariya qasa-qasa.

Jay ne ya fito da shirin sa staff na tafiya office, qananun kayan da suka yi mugun karɓansa ya fito sanye da su, dinning ya wuce yana kan duba agogon da ke maqale a hannunsa, mummy da Daddy ya samu a dinning ɗin, ɗan rusunawa yayi ya gaishe da Daddy ya amsa ya kuma gaishe da mummy itama amsawan tayi ta tashi ta sanya masa abun karyawan, Daddy ne yayi gyaran murya ya ce “Jabeer kai da ɗan uwanka ku dage kuje Maiduguri ku stayar da mata dan kun fara isanmu, iyayenku mata su kula da mu su kula da ku, yanzu dubifa a maimakon kai ko matarka wani yayi saving namu shi ne mamanka ce take saving naka ba kunya ka amsa ka ci, to ko kuje ku duba da kanku ko muyi magana da Mustapha a zaɓa muku kawai a ɗaura”.

Jay kansa a qasa bai cewa Daddy uffan ba yana jefa chip’s nasa a baki da wuri-wuri yana bi da tea da mummy ta gama haɗa masa yanzu.

Mummy ce tayi magana itama “maganan ɗaukomin yarinyana ka tabbatar ka dawo da wuri kaje ka ɗaukota”, kaman zai yi kuka jin surutun iyayen nasa ga shi yayi latti sauri yake yi ya ce “Habibty dude zai je dubo su sweetie inyaso sai ya ɗauko ta”.

“Eh dole tunda ni ban isa da kai ba ka ce son zai ɗauko ta, to kai nakeso kaje ka ɗauko ta banson rashin kunya”.

Jay ba yanda ya iya ya ce “to habibty zan ɗauko ta Allah huci zuciyanki”.

Qwafa Daddy yayi ya ce “yara duk kunbi kun rena mutane, wato dan an sake muku shi ne zai zama abin yinku, ba laifinku bane nine na qyaleku tun kuna yara kuke qiramun mata Habibty, to ya isheku kowa yaje ya nemo tasa habibtyn kubarmin tawa in ba za ku ƙirata mummy ba sai ku ƙirata Maryam mu tabbatar kun girma”.

Jay ganin yau iyayen nasa da shi suka tashi a wuya sai ya ɗaga cup na tea ɗin ya shanye tass ya miqe ya musu bankwana bi jira sun ce komai ba ya fice abinsa yana faɗin “yau ko wa ya taɓo ku kuke sauqewa a kaina oho! To Nima na tafi kuma daga asibitin zan wuce Ashaka tare da ita za mu dawo inyaso ayi mana faɗan tare ba ni kaɗai ba” ya shige motansa ya nufi FMC Gombe.

Kwance yake a haɗaɗɗen gadon sa yana mustu-mustu alaman yana son farkawa, qarar da wayansa yayi ne ya sanya shi qarisa buɗe ido ya miqa hannu ya ɗau wayan, ganin sabon number sai bai ɗauka ba ya miqe ya zauna, can sai ya tashi ya shige toilet yayo wanka ya fito ɗaure da towel iya guiwansa, wayan ne ya qara ringing ya ɗauka ya ga Numbern ɗazu ne sai yaja staki ya wuce gaban mirrow ya gama shafe-shafensa ya gyara gashin kansa da gemunsa sannan ya wuce ya sanya kayansa, wayan ya ɗauka yana ƙoƙarin fita sai ga qira Managern sa na Jigawa, fasa ficewan yayi ya koma bakin bed ɗin ya zauna yana picking call ɗin Managern ya gaishe sa ya kuma qara jajanta masa sannan ya ce “Sir inba mastala akwai buqatan zuwanka Companyn kana da baqi”.

Dafe kai DMD yayi dan shi a wannan yanayin bayajin yana da nistuwan da zai iya haɗuwa da wasu, cikin yanayin rashin son magana ya ce “su waye ne baqin?

“Sir wasu turawa ne sai Alhaji Abdullahi Naira, sunce suna buqatan ganinka na faɗa musu akwai bussyn da kakeyi amma sun dage a haɗa su da kai shi ne nace sai na faɗa maka sai a sanya lokacin meeting”.

Iska mai zafi ya busar a bakinsa sannan ya ce “gobe Thursday by 2pm su tabbatar ba su yi latti ba dan ina da abun yi”.

“Okay Sir”.

Kitt DMD ya kashe wayansa cikin gajiya dan yasan gobe ranan yin ciwon kansa kenan, in akwai abinda ya stana meeting barinma da turawa dan su basusan darajan lafiyan jikinsu ba surutu kaman dan shi kaɗai aka tsaga musu baki, saqo ne ya shigo wayan ta Gmail nasa ya shiga ya duba ganin wani abun sai ya kuma dafe goshi yana faɗin “na fara gajiya da ayyukan nan mutum ba zai yi lokacin kansa ya huta ba, am not going to Canada without Ammi duk abinda zai samu Companyn ya same sa mtsww!”

Miqewa yayi ya fice a ɗakin ya sauqo palourn qasa ya tarar Daddy na shirin fita, gaishesa yayi ya amsa yana faɗin “son zan fita ko akwai wani magana?

DMD kaman baison buɗe baki ya ce “Daddy ba komai dama inaso ne a maida kuɗin reward na wanda ya kawo Ammi ya koma 10millions ne”.

Daddy murmushi kawai yayi ya ce “karka damu son, in duk duniya abinda muka mallaka za mu bayar Maimuna ta dawo to za mu bada, amma bana tunanin issuen kuɗi ne ya sa haryanzun ba labari kai dai mu dage da addu’a, in na dawo za muyi magana ko”.

“Okay Daddy a dawo lafiya”.

Daddy ficewa yayi yana tausayin yaran, Darling dinning ya wuce ya haɗa tea da kansa ya sha ɗan dai-dai sannan ya miqe ya nufi ɗakin mummy, a hanya suka haɗu itama tana nufo palourn, gaisheta yayi ta amsa sannan ya juya zai fita, mummy da kallo ta bisa tana faɗin “yau ko shayin ba za’a sha bane balaraben Ammi?

Yana murmushinsa mai stada ya juyo ya ce “habibty na sha har da chip’s na taɓa sai na dawo” ya faɗa yana ficewa a palourn shi ma.

Mummy dai ta yarda ya ci dan tunda yasan anyi chip’s to yaje dinning dan haka sai ta qira mai aiki ta tattare wajan ita kuma ta zauna tana kallo.

Yana ficewa ya hau motansa haɗaɗɗe ya nufi FMC Gombe, yana isa yayi parking ya shige hanyan office na Jay, turawa yayi ya shiga bai ko yi knocking ba Allah yaso ba kowa sai Jay da ke faman rubuce-rubuce a files, jin an shigo ba sallama ya ɗago da tunanin ko DMD ne ai kuwa shi ɗin ne, girgiza kai yayi yana faɗin “nasan ba mai shigomin office haka sai kai dude, wallahi ka bi a hankali dan watarana kunyataka zan yi domin ni kasan ba kunya gareni ba kana shigowa kawai ka ganni saman babe muna sharholiya”.

DMD zama yayi a kujeran dake gefe can da Jay yana faɗin “aikinka kenan, ga shi ka zama likita sai iskancin ya ƙaru, ni na rasa dalilina na son biyoka ma tunda samun ciwon kai kake”.

Dariya Jay ya kwashe da shi ya ce “to daganan za ka fahimci in tarkona ya kama mace to fa ta shiga uku ba sukuni sai ta ga jabirunta ta faɗin Hajja wai jabiru, kai da kake namiji ma kana ta bina balle mace ah kace nikan ba ruwana da suratul Yusuf ko Maryam normal ne”.

DMD miqewa yayi ya shige room ɗin cikin office ɗin ba tare da ya tanka masa ba, zama yayi a kan 3seater da ke ɗakin hankalinsa gaba-ɗaya na kan wayan hannunsa, qoqari yake ya ji da issuen Companies na Canada ba sai ya koma ba.

Jay ya tashi zai bi DMD ciki sai patient suka shigo, sai da ya gama da su sannan ya biyo DMD yana faɗin “dude ya batun zuwa Ashaka?

DMD da hankalinsa ke kan aikin da yake yi ya ce “yaushe muka yi da kai zan je Ashaka?

“Dude banson irin maganannan ba kai kace za kaje dubo su sweetie ran Wednesday ba, ko ka manta ne?

“Ohh god! Wallahi gaba ɗaya Jay na mance, yanzu ga tafiya Jigawa gobe ya kamani ga zuwa Ashaka bari na wuce yanzu dan na dawo da wuri” faɗin DMD yana ƙoƙarin miqewa.

Jay ya ce “dude please ka dawo da Afreen wallahi Habibty ta damu a ɗauko mata yarinyarta kuma ga shi ni anjima ma ina da operation”.

“Amma dai jabeer Habibty ta ce ba Mufaddal ba ko dan haka ba wacce zan ɗauko a mota ta”.

Jay yasan dama za’a rina dan haka ba yanda ya iya sai ya ce “to ka jira ni sharp-sharp nayi operation sai mu wuce, dama Habibty ta ce ni ta aika ba kai ba ni zan ɗauko mata yarinyarta”.

DMD komawa yayi ya zauna bai ce wa Jay komai ba sai ma hankalinsa da ya qara maidawa kan abinda yake yi a wayan.

Jay ficewa yayi, can ba jimawa ya dawo ya sanya labcort ya fice, eye glasses nasa ya sanya sannan ya sanya safan hannu da facemask ya fice a office ɗin, direct theater room ya wuce inda ya tarar duka nurses ɗin suna jiransa sun kammala komai wa patient ɗin theatern kawai zai yi.

Sai da suka kwashe a wanni biyu a theater room ɗin sannan ya cire safan hannun ya jefa a bowl na nurse’s ɗin ya fice, yana shiga office nasa ya zare facemask yana faɗin “Allah ka basa lafiya kasa munyi a sa’a” ya shige room da DMD yake ya cire labcort ɗin ya shige toilet sai can ya fito ya gyara jikinsa yana faɗin dude ka sanya wani bawan Allah a addu’a sai kaga yanda cutan ulcer ta masa kaca-kaca da hanji, kai jama’a Allah raba ɗan adam da wahala, ai cuta masifa ce yau duk qiyayyarka ga mutum ba zai sanya maka ciwo ba ai ba qinka yake yi ba, wallahi ulcer babbar cuta ce gwanda ka dage da ci dude inka staya rigima ta kama ka za ka faɗawa ‘yan Canada billahillzi”.

DMD ba tare da ya ɗago ba ya ce “Allah ya basa lafiya, mu wuce yanzu”.

Jay hararan wasa ya aikawa DMD ya ce “amma ba ka da mutunci balle imani, na staga bawan Allah nayi tafiyata ai ma jira anjima kaɗan mu tabbatar komai normal sannan ko hutawa ban yi ba, gaskiya ba ka da kirki dude ko zuciyan musulunci ma ba ka da”.

DMD murmushi yayi kawai da gefen baki hankalinsa na kan wayansa bai ce masa uffan ba, Jay ya tashi ya koma office nasa.

Sai da aka jima sannan Jay yaje da kansa ɗakin da aka dawo da patient ɗin ya tabbatar komai lafiya sai jiran farkawansa sannan ya ce da Nurses su kula da shi zai je aikan mummynsa zuwa dare zai dawo ya duba jikin patient ɗin, ya koma yayiwa DMD magana sannan ya miqe ya fito suka shiga motan DMD Jay yabar nasa a asibitin dan in sun dawo sai ya biyo asibitin kamun ya koma gida, suka kama hanyan Ashaka Jay na surutun sa DMD sai jifa-jifa yake amsa wani maganan.

Malam ba wasa tun da ya shigo yake satan kallon Innai dan gani yayi ta rame amma ta ƙara kyau, magana yayi a zuciyansa shi kaɗai “wannan yarinya akwai kyau kaman aljana, ba dan rashin girman ta ba me zai hana nabi ta shawaran Jay”.

Innai dai yau ko ta kan malam ba wasa bata bi ba hankalinta gaba-ɗaya na kan qofa zuba ido take taga ta inda Afrah za ta ɓullo, shiru-shiru ga shi windonsu ko ka leqa baya facing na gate balle ka kalli ‘yan latti dan bata cire tsammanin Afrah latti ta yi.

Malam ba wasa sai da ya ɗan yi wasu abubuwa sannan ya fara qiran sunan rigister, yana tsaka da qira sai ga discipline master ya yi sallama a bakin qofan ajin, barin qiran sunan Malam ba wasa yayi ya ce “Malam ka shigo”.

Discipline master shigowa yayi suka gaisa da Malam ba wasa ɗaliban ma suka miqe suka gaishe sa sannan ya ce “Malam Farooq ‘yar a cikin ‘yan ajinka waɗanda suka yi latti ana dukansu ɗaya a cikinsu ta faɗi ta suma”.

Malam ba wasa cikin ko inkula dan haushi students masu latti suke basa ya ce “ku wasta mata ruwa in ta farfaɗo ku qara mata ta kuma suma ku wasta mata ruwa haka-haka har ku gama dukan naku ai ita tajawa kanta tunda yara basa ji, kuzo makaranta akan lokaci ya zama aiki mu malamai ma sai mu rigasu zuwa dan tsaban sun renamu kuma a hakan iyayen suna stawatar musu da ba’a stawar musu wa yasan lokacin da zasu dinga zuwa”.

Discipline master ya ce “malam Farooq wallahi an watsa mata ruwa amma ko mosti bata yi, ga shi tazo da wata yarinya wacce da alama ba’a makarantan nan take ba, yarinyar ma sai indianci take yi wai su a Canada ba’a dukan su latti ga shi an daki auntynta an kashe ta sai ta kullemu”.

Malam ba wasa cikin haushi ya ce “dama har da ‘yar rakiya ta taho? Me sunanta?

“Students naka sun ce sunanta FATIMA NURA MUHAMMAD”.

Discipline master na kammala faɗin sunan Afrah ba ɓata lokaci Innai kaman wacce aka stikara kaman aljana kamun malam ba wasa ya ce wani abu har ta fice a class ɗin da gudu tayi wajan ‘yan latti tana qiran Afrah dan har ta fara hawaye, Afrah ta taɓa faɗa mata ita in aka daketa ciwo take yi storon duka take yi”.

Malam ba wasa da mamaki ya juya suka fice da discipline sai kuma ya dawo ya jawa ‘yan ajin kunne sannan suka wuce, ya iske Innai ta rungumi Afrah sai kuka take kaman ance mata ta mutu, ga sweetie kuma a gefe sai sharɓan nata kukan take itama tana masifa da indianci, malam ba wasa kallonsu yayi tare da yin qwafa ganin irin ihun da yarinyar da aka zo da ita take yi tana qoqarin tara musu jama’a dan har malamai sun fara nufo su ga ɗalibai sai leqowa ake wasu ma fitowa suka yi daga ajujuwansu suna ganin gulma.

Stawa ya dakawa Innai yana magana da turanci “ki ajiyeta ki koma class kamun na yi ball da ke, za ku tara mana mutane mutuwa ta yi ko kasheta aka yi”.

Innai duk da kuwa stawan ya storita ta amma ko mosti bata yi ba, malaman da suka iso ne suka fara tambayan akasi, shi malam ba wasa haɗe fiska yayi sai discipline master ke bawa Kowa amsan abinda ya faru a taqaice in suka tambaya.

Duk malaman sun taru anrasa ya za’a yi, har sai da principal yazo da kansa sannan ya stawatar musu sun saka yara gaba ba zasu yi wani motsin ba in yarinya ta mutu fa? Duk haquri suka bada saura suka bar wajan aka qira Malama mace tazo ta ɗauki Afrah suka kai ta masallaci, aka shashshafa mata ruwa amma ko mosti bata yi ba ganin haka aka qira malam ba wasa akan ko za’a kai yarinya gidansu, malam ba wasa ya ce eh yasan gidan nasu, sai principal ya ce a ɗau school boss a kai su.

Innai duk abinda ake yi tana maqale da Afrah tana kan shararo hawayenta, ita kuma sweetie surutu take kan yi, malam ba wasa sai yanzu ya kula da ita ya ce “sweetie” kallonsa tayi kaman ta ganesa shi ne wanda suka je gida da big bro aikam ta ce “uncle sun kashe Aunty Afrah akan latti kuma ba kyau dukan yara ɗalibai” ta faɗa da turanci, murmushi malam ba wasa ya yi a ransa yana faɗin “wannan dokan ku ne a ƙasashen waje mukam a Nigeria ba ruwansu a ta jibgan yara kaman jakkai Shiyasa wasu yaran ma basa fahimtan karatun”.

<< Jahilci Ko Al’ada 23

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×