Wata farar mota ce ta kamfanin Elentra Mai bakaken gilasai ta kunno Kai a cikin Asibitin general hospital dake garin katsina aguje take tamkar zata tashi sama inda mutane suka dare suka Bata hanya Kuma suna Raka ta da ido . Kasancewar Asibiti ne sai mutane sukayi wa matukin motar uzuri na marar lafiya kila gareshi me neman agajin gaggawa.
Amma ga zaton su kenan don ba hakan bane duk da matar shi ce ke nakudar haihuwa Amma ba Wai tausayin ta ne jigon gudun ba A a yadda ya taho aguje a motar Hala zuciyar shi ke fusace Yana tafe. . .