Sumayya ta samu Aljannar duniya a gidan mijinta da Ubangiji ya yi mata musa ya ta alheri wato alh Kabir Mai motoci.
wani hamshkin me arziki ne Wanda Allah yayiwa daukaka ta hanyar kasuwar shi ta siyar da motoci, mutum ne me kulawa da iyali don Allah yayi shi me tausayin Mata musamman da sumayya Bata boye mishi halin da ta kasance a gidan tsohon mijin ta Uban yan buyun ta ba,
don haka sumayya Bata samu matsala dashi ba sai dai matar shi zaliha. Zaliha macece me kishin jaraba. Ko dayake shi kishin ance ba dab'i a bace. . .