HAIDAR ya farka daga dogon barcin da duniyar maye ta cillashi. Ya dubi kafarshi da manyan takalman na kamfanin tumber land kwama kwama Wanda bai samu zarafin cire su ba ya hau gadon dasu duk ya mutsike gadon da dattin da ya tako.
Yaja tsaki kafin ya cire takalman ya fada bandaki yayi wanka yafito Yana sharce sumar kanshi wadda ya Tara Yana shafa Mata wani Jan Abu me kona gashi tamkar furfura duk cikin gayu ne.
Ya sauya Kaya ya fito sai zuba kamshi yake. Ya zauna kusa da alh balarabe Wanda yake break Yana fadin dady morning. Ya. . .