Goga ya SHIGA lissafin yaushe ne hussaina zata Kira shi?, Gashi layin nata akashe haka ya wuni Kiran layin Amma shegiyar matar Nan me zakin muryar tsiya na sanar dashi sai dai ya sake Kira lokaci na gaba. Duk da wannan magana da computer ke fada mishi bai hakura ya Daina Kiran layin ba.
Gaba daya ya sauya daga gogan da zuwa wani sabon gogan. Yayi mamakin yadda soyayyar Hussaina ta sauya shi. Sauyi Kuma me yawa. Dama haka Allah yake shi son maso wani koshin wahala ne. Ga can hassana na muruwar son shi kamar ta hadiye shi ta. . .
