Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da Aminci marasa adadi su yi ta tabbata ga shugaban mu ANNABI MUHD S A W, da ahalin gidansa madaukaka da masu bin su da kyautatawa har izuwa ranar alkiyama.
Sakina ta zaro ido afirgice ganin da gaske balarabe yake Shirin kyara musu fetur din da zai konesu ita da danta,
"Wai da gaske kake za ka iya sanya mana wuta hubby",
"To Ki dai jira idan kikaji yadda wuta zatayi sukuwa afatarki sai ki fidda shakka da kokonto ki tabbatar da gaske Nike",
Ya bude murfin galan din Yana kokarin watso. . .