Skip to content
Part 6 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Zubaidah da ta ke da yawan uzurirrika har kuɗi take ba wa Asma’un don ta yi mata nata ayyukan, ita kuma ta samu damar fita sabgoginta, amma Asma’u ba ta karɓar kuɗinta kuma sam ba ta ƙiya wa, ita daɗi ma take ji tana ganin sun ba ta wani matsayi da ba ta yi tsammanin samu ba a gidan.

Yau da gobe Asma’u ta saba, ta goge da duk wani nau’in aikin gidan har da shiga kitchen. Hajiya Yaganah ce ke kokarin hana ta don tana jiye mata wahalar ayyukan da take sa kanta ko duk da cikin da ke jikinta, amma ina ba ta san ma lokacin da take yi ba tunda Hajiyar ba zama take a gidan ba. Ɓangaren ci da sha Asma’u ba ta rasa ko ɗaya ba, don gidan babu yunwa, suttura ma sannu a hankali suka fara ba ta kwance musamman Zubaidah.

Cikin ɗan lokaci Asma’u ta fara sauyawa, sannan alamomin ciki duka suka bayyana a tare da ita. Hajiya na ta ƙoƙarin bin umarnin Likita wajen kaita Asibiti lokaci zuwa lokaci. Duk sa’ar da su Ummita suka fice suka tafi makaranta Hajiya ma ta tafi harkokinta gidan ya kan rage sai Asma’u kaɗai, wanda kafin zuwanta kulle gidan ake a aika makullin maƙwabta don Nasir ma idan ya fice tun safe ba ya dawowa sai dare.

Kusan ko da yaushe ƙofar gidan ba ya rabo da samarin Zubaidah, Ummita har da Firdausi. Ta wannan fannin Asma’u na ganin sakaci da gazawar Hajiya.

Ba ta da matsalar komai sai ta kaddarar da ta afka mata, ga rashin sanin taƙamaiman halin da Innarta take ciki, tana so ta haife cikinta ta koma gare ta.

*****
Ta yi nisa sosai cikin tunaninta ba ta sani ba har Zubaidah ta shigo ɗakin tana ta rafka sallama har sai da ta taɓa ta.

“Ke lafiyarki, tunanin me kike?”

Banda abin Zubaidah har ta tambaye ta tunanin me ta ke? Ita ce fa Asma’u.

Ta ɗago idanunta da suka cika taf da kwalla tana dubanta, Zubaidar ta ɗan ji tausayinta amma sai ta da ke ta sake cewa, “Kuka kuma za ki yi Asma’u, me aka miki ko su Firdausi sun maki wani abun ne?”

“Babu komai Anti Zubaidah.”

“Amma ki ka zauna kina irin wannan dogon tunani haka har da kuka.” Shiru ta yi don ba ta da amsar da za ta ba ta. “To kin ga ni don Allah wani taimako za ki min, aiken ki zan yi don su Maryam ba sa gidan nan.”

Asma’u tana jin daɗin yadda Zubaidah ke saka ta aiki cikin mutuntawa da neman yardarta, saɓanin su Ummita da suke mata tamkar sun samu baiwar su. Zubaidah ta zira hannu cikin jakarta ta fiddo kuɗi ta miƙa mata tare da sanar da ita abin da za ta siyo mata, ta karɓa. Har ta kai bakin ƙofa za ta fita sai kuma ta ji ta kira sunanta, ta juyo tana kallonta.

“Idan kin dawo akwai maganar da nake son za mu yi da ke.” Asma’u ta girgiza kai tana mamaki da tambayar kanta ko wace magana za su yi? Har ta je ta dawo ba ta samu amsar tambayar ba.

Ta kawo mata fulawa da sauran kayayyakin sarrafawa don yin nau’ikan abubuwan da za ta tarbi baƙinta. A ɗakinta ta same ta,

Zubaidan ta nuna mata kujera. “Zauna a nan.” Ta zauna cike da saƙe-saƙen Zuci.

“Asma’u idan ba za ki damu ba wata tambaya nake son yi miki game da cikin jikinki.”

A hankali Asma’u ta ɗago kai tana kallon Zubaidah da ke danna wayarta kamar ba ita ta faɗi maganar ba.

“Wai ni kam wane hukunci kuka yanke kan abin da ke cikinki, ina nufin idan ki ka haihu ya za ki yi da ɗan ko ‘yar, shin da shi za ki koma ƙauyen ku?” Zubaidah ta jefo mata tambayar da ta kiɗima ƙwaƙwalwarta duk da cewa ko da yaushe ita kanta wannan tambayar na yawo a ranta ta kuma kasa samun amsarta. Ba ta da abin yi face ta gyaɗa mata kai alamun tabbatarwa ba tare da tana tsammanin hakan mafita ce gare ta ba.

“Kenan ku a al’adar ku rainon cikin da ba ta hanyar aure aka same shi ba shi ne yake zama abin kunya da gudu, ba goyonsa ba ko?”

Asma’u ta girgiza kai a halin yanzu ƙwalla na ƙoƙarin cika idanunta.

“Kin ga ni fa ba na son kukan nan.”

Ta ce, “Duka abin kunya ne Aunty, har gara ma cikin don idan goyon ne ɗan ma ba zai tsira ba, musamman idan ya yi wayo zai yi ta haɗuwa da tsangwama daga wajen yara har manya, wasu moɗa ko kwanon cin abinci idan ya taɓa sun bar amfani da su har abada. Akwai Habi da irin haka ta taɓa faruwa da ita yaron ya shiga cikin ‘yan uwansa yara yana wasa sai gawarsa aka kawo musu wani da ba a san ko waye ba ya kashe shi kuma babu abin da aka yi.”

“Danƙari! To amma a haka kike so ki koma ƙauyen da naki ɗan.”

“Wallahi Anti har yanzu ni kaina bayan na haihu ban san makomata ba, ya zan yi da abin da na haifa? Ban sani ba.”

Zubaidah ta ƙura mata ido tana nazarinta a taƙaice, jim kaɗan ta sauke ajiyar zuciya. “Abu ɗaya za ki yi ya fishshe ki ki fita daga damuwar da kike ciki har abada Asma’u.”

“Har abada fa kika ce, ta yaya wannan baƙin tabon zai goge a cikin rayuwata har abada? Bana jin hakan zai yiwu Anti Zubaidah.”

“Zai goge, tabbas zai goge matuƙar za ki ɗauki shawarar da zan ba ki ki yi amfani da ita, sannan ni zan taimaka miki.”

“Wace shawara ce wannan, sannan wane irin taimako za ki min?”

“Ki zubar da cikin.” Zubaidah ta faɗi ba ta ko ɗar.

Asma’u ta rintse idanunta kana ta buɗe su a hankali tana kallonta, ita ma ɗin kallon ta take cike da son ganin yadda za ta karɓi batun sai kuma ta miƙe zumbur kamar an mintsine ta.

“Wannan ce dama shawarar ta ki Anti, kin san matsayin wanda ya zubda ciki a shari’ance? Ba zan iya ba ki yi haƙuri kar ki ce na ƙi bin maganar ki.”

“Zauna ki ji Asma’u.” Zubaidah ta fada.
“Ko na zauna ma ba zan fahimce ki ba.”

“Kina nufin dai ba ki san illar rainon shege har ki haife shi ba. Kar ki manta zai tashi bai san Ubansa ba, na yi imanin ba zai gafarta miki ba muddin ya san kin haife shi ne ba ta hanyar raya Sunna ba. Duk irin yadda za ki fahimtar da shi bai zama lallai ya fahimce ki ba, Asma’u kada ki manta ba kowa ke iya karɓar ƙaddara ba.”

“Amma ko ya zama dole mu karɓi ƙaddararmu Anti Zubaidah.” Asma’u ta faɗi cike da jarumta da ƙwarin gwiwarta.

“Shi kenan ai, amma ki sani miliyoyin Mutane sun zubar da ciki kuma sun zauna lafiya babu wata tashi-tashina, na tabbata ko Innarki ba za ta ga aibun haka ba. Ki je ki yi tunani, wataƙila ki gane abin da nake nufi, duk ranar da Allah Ya sa ki ka gane ina nan ina jiranki kan taimakon da na yi niyyar yi miki.”

Kallon ta kawai take har lokacin da Zubaidan ta rufe maganganunta da faɗin “Ki wuce ki kai min kayan Kitchen.” Ta bar ɗakin Zuciyarta na kai komo kan duk abin da ya faru.

*****
Cikin dare tana kwance amma ta kasa runtsawa. Tana iya sauraron hayaniyar Zubaidah da samarin ta a sitting room, har lokacin da suka tashi mota suka tafi ita kuma ta dawo cikin gida, ta ji lokacin Zubaidar ta shige ɗaki tana waƙe-waƙenta.
Ummita ce ƙarshen shigowa gidan ta rufe ƙofa. Ta juya ɓangaren da su Firdausi su ke, suna ta kwasar barcinsu, yayin da ƙwaƙwalwarta ke ci gaba da karɓar amsa-kuwwar kalaman Zubaidah.

A hankali ta share hawaye gami da gyara kwanciyarta, a halin da take ciki yanzu so take ta yi barci amma abin ya gagara, ƙoƙarinta dai ta fattaki huɗubar Zubaidah tunda har yanzu ba ta samu abin kamawa ba a ciki. Duk gidadancinta ta san ba dai-dai ba ne zubar da ciki.

Har kiran sallar asubah ba ta runtsa ba. Gari ya waye cur tana abu ɗaya, don haka ita ce farkon farin fitowa tsakar gida. Kasancewar yau lahadi babu makarantar da suke sammakon zuwa, ga Hajiya ba ta gari ta yi tafiya, dukkansu sun yi luf a ɗaki abin su. Ta san yau kalacin safe ma sai gyaran Allah, matuƙar ba ita za ta shiga kitchen da kanta ta yi ba tare da an saka ta ba, abin da kuma ba zai taɓa yiyuwa ba.

Wani abun takaicin ma; suna iya tashi kowa ya yi gaban kansa, ma’ana ko wacce ta siyo abin da ranta yake so ta ci, ko su fara gasar dafa Indomie tunda suna da kuɗi a jikinsu, ita ce dai za ta wahaltu da tsarin su.

<< Kaddarar Mutum 5Kaddarar Mutum 7 >>

2 thoughts on “Kaddarar Mutum 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.