Skip to content
Part 8 of 9 in the Series Kaddarar So by Fatima Rabiu

ARMAN HARUN’S HOSPITAL LOGAS NIGERIA

Turo k’ofar Office d’in, tayi cike da yanga da takunta mai jan hankali. Sai dai d’an k’aramin tsaki taja, ganin wadda take danshi ko arzik’in ya d’ago ya kalleta ma baiyi ba.

“My Arman”

“Uhum”

Shine kawai abunda ya amsa mata.

“Haba Arman ya kamata ace zuwa yanzu kasan irin d’unbin k’aunarka da nake you should give me a chance, I don’t want to love you for myself, you should stop like that to me. Bubi fa yanzu ko kallo ban isheka ba, wallahi kaine kad’ai kake iya min wannan dizgin”. Ta idasa maganar cike da takaicin kanta

Cike da izzarsa ya d’ago dararan idonsa yana cire d’an gilashin dake manne a idonsa yana d’an dubanta kad’an. And ko kad’an Lilaah bata birgesa, duk da yasan ba k’aramin so take mai ba. But shi baya sonta ko kad’an. But the one he loves is different, and he knows that there is definitely a dust every day that he says to the one he loves. Katse mai tunani tayi da cewa “My Arman, please give me a chance and you will be happy with me”

Murmushin gefen baki Arman yayi wadda yasa ma Lilaah fad’uwar gaba, saboda wani bala’in kyau data ga ya k’ara mata, ga wani sonsa dake fisgarta. Kai wallahi idan bata samu Arman ba akwai matsala, tana jin babu abunda bazata iyayi ba akansa. Ta shagala da kallonsa, har bata san ya tashi daga inda yake ba, sai da taji saukar muryarsa, yasa tad’an saki ajiyar zuciya.

Lilaah, you should be patient now. Nasha gaya miki ni bana son mace wacce zata iya furta tana son namiji. If you were yourself, you would have kept your love for me in your heart and maybe you would have valued yourself. And ni yanzu naga wacce nake so Nan… “”What are you saying Doctor Arman” ta fad’a a zabure

D’an taku ya d’anyi ya matso gabanta ido cikin ido ba shakka fuskarsa babu wasa ya ce “what you heard me say is, I won’t reveal who I want soon”

“It will never be possible, surely whoever I can kill by God against you, I am jealous of you. Arman ina bazai tab’a yuwu ba wallahi”

You are saying that it will never be possible, and knowing yourself must be possible, where life and life are my choice”

Maganganun da yake gaya mata, daya san yadda take jin saukar su a cikin ranta da gangar jikinta da ko kad’an bazai d’akko maganar wata yana danganta kansa da shi ba. She felt a kind of heartache, including a very jealous feeling, lokaci d’aya taji ta tsani wacce yake ikirarin zai aura, lokaci d’aya taji duk duniya ba wacce ta tsada sai wannan halittar da zatai mata shamaki da samun cikar burinta. Dole ne cikin biyu ayi d’aya, kodai Arman ya aureta a zauna lafiya, ko kuma yaje yayi aure ta hanasa zaman lafiya, daga shi har wacce ya zab’a ma kansa.

ARMAN HARUN’S FAMILY HAUSE LOGAS NIGERIA

K’as k’as k’as sautin taunar chingum ke tashi a tsakiyar parlon. Humaira dake sakkowa daga kan bene tana nufar kitchen, ta d’an tsaya tana duban, Salma dake tsaye da akwati, sanye take da wasu y’an iskan k’ananan k’aya, ance matsu ga wani kafcecan gilas data manna a idonta, tana bin parlon da kallo. Ganin Humaira yasa ta k’ara wani kame kanta yatsine baki tayi, bata da niyar tanka mata, tana niyar barin wajan, ta nufi hanyar da zata sada ta da part d’in Haj Shuwa, taji Humaira na cewa “Ohh su Salma ne a gidan namu”

D’an juyawa tayi, a hankali tasa hannunta kamar bata so ta cire gilas d’in dake manne a idonta, tayi mata wani kallo kamin ta ce “hmm kware mune a gidan naku, kuma da alama munzo kenan”

“Allah sarki, ai kin san mu dama masu taimakon mutane ne, kowa yazo zai iya zama gidanmu domin yaci arzik’i yabar arzik’i inda yake”

Da sauri ta dube Humaira data yi maganar kamar wacce ba ita ce tayi ta ba, maganar ta shigeta kamin ta ce “uhum koda yake mufa munfi k’arfin muzo muci arzik’i domin muma ansan ba matsiyata bane, da abun duniyarmu a hannunmu, kuma da alama mun kusa zama masu gidan gaba d’aya, sai dai azo aci namu arzik’in”

Humaira zata sake magana kenan, Momma ta fito tana duban Salma, duk taji mi suke cewa, d’an murmushi tayi irin na manya, duk abunda matan gidan suke akan d’an nata tana sane, kuma duk wani takunsu nason had’a y’ay’ansu da yaronta d’aya tilo tamkar da dubu ta sani.

  “Humaira abunda yasa kika sakko kenan?, son magana, bana hane ki da sa baki a maganar da bata shafe ki bane?”

K’asa tayi da kanta ta ce “sorry My love” tana Idasa fad’ar haka ta Idasa shigewa k’aton kitchen d’in nasu.

Salma kuwa, ko kallon inda Momma take bata yi ba tayi shigewarta part d’in Haj Shuwa.

 Girgiza kai kawaii Momma tayi, tana tunanin a haka zata amince d’anta ya auri wannan yarinyar marar tarbiyya, ina ai bazai tab’a yuwu ba kam.

 Da gudu taje ta rungume Haj Shuwa dake tsaye tana waya.

“Ahh ahh, harkin iso, mutanan Abuja da alama jirgin safe kika biyo yanzu muke waya da Mamarki Binta ai take sanar dani ai kin taho”

 “Uhum, Umma ai dama kin san nafi son tahowar safe”

 “Hakane y’ar albarka fatan kin iso lafiya?”

 “K’alau Umma na iso”

“To madallah, ai kin san abunda muke ciki ba sai na sake miki baya ni ba. Karki sakan kance ki fad’a sonsa da gaske domin kuwa nan gaba kad’an zamu aika sa inda ba’a dawowa”

Wata dariya Salma ta saki tana duban Umma ta ce “ai Umma a shirye nake kawai umarninku nake jira”

“Tabbas dama nasan zaki iya, to amma fa akwai y’ar matsala guda d’aya”

“Wacce irin matsala kuma Umma?”

“Hmm Arman Malamina ya gaya min cewa akwai wacce ya fad’a tarkon k’aunarta, kuma da alama akwai wani rabo mai zafi a tare da ita, Mlm ya ce dole mu bari ya aureta shine kawai zamu bari burinmu ya cika yadda muke so, dole saita shigo gidan nan tukun, zamu iya cin galaba akansa harma ita, a lokacin zamu sa masa tsananin k’aunarki zamu sa Mlm yasa masa kasalar Ibada ta yadda zamu ci galaba akansa da wuri, ke kuma zamu sa ki rink’a shige masa ta yadda zaki rink’a had’a husuma tsakaninsa da matarsa, komai a shirye muke, ita kad’ai muke jiran zuwanta cikin gidan nan”

Tashi tsaye Salma tayi sab’anin da, da take zaune kusa da Haj Shuwa

Ta ce “tabbas kuwa kun iya dabara, ni kuma sauran aikin ku barsa a hannu na Umma”.

SURURE, LOGAS NIGERIA

“Wai mi kake cewa ne, Aliyu, na kasa fahimtarka Husainar ce aka nema ta aka rasa” Mimi ta k’are maganar had’e da tashi tsaye manne da waya a kunnanta  daga cikin wayar Aliyu muryarsa hankali a tashe ya ce “wallahi Mimi sai da na ce mata tahau jirgi idan zata tafi katsina tayi min gaddama. Mimi is privileged and pregnant, my mind is awake”

  “Wai abunda ban gane ba, kai kana ina harka bari hakan ta faru, kasan fa katsina hanyar bata cika kyau ba, the kidnappers have attacked the town a lot”

Mimi knows that, he talked to her since I told her to go and see home, ni kuma nabar mata komai na baro Abuja ina kwatano ni yanzu haka, munzo wani taro ne ashe ita kuma tasa direban gida ya kaita. I took my plane, she got on

“Insha Allah zata dawo lafiya, ka nemi wayarta ne?” “Mimi tun d’azo nake neman layinta baya shiga. And they didn’t get enough from morning to night, Mimi hankali ya kasa kwanciya kamar matata na cikin matsala hankali a mugun tashe yake wallahi”

Sauk’e lumfashi Mimi tayi tana k’ara kwantar mai da hankali, daga k’arshe ta ce “ina so karka sanar da danginta tukun muga mi Allah zaiyi, karmu tada masu hankali kasan Mahaifiyarta bata cika lafiya ba”

“Insha Allah Mimi, amma idan lokacin sanar dasu yayi dole su sani”

“Na sani Aliyu amma kabi komai a hankali tunda bamu tabbatar an sace tan ba, ni nafi ba ko dai motarce ta lalace masu kan hanya”.  “Hakane Mimi”

Sallama suke Mimi ta dawo dubanta wajan Lalaah dake tsaye a kusa da ita, tana ta dumunta da cewa mi yake faruwa hankali a tashe itama.

Fitowarta kenan, da murnarta na ta fad’ama Mimin Doctor Arman ya turo mata kud’in zanenta kusan Million goma, ita da bata d’auka yawan kud’in zai kai haka ba, ta d’auka bai wuce a bata dubu d’ari ba. Sosai ta rud’e har sai da Arman d’in da kansa ya kirata, tayi mamakin kiran sa. Inda take ce mai kud’in sunyi yawa, ina zata kai su?, sai dai yayi mata murmushi ya ce ta bada sadaka idan ba abunda zatai dasu, daga nan yayita janta da fira, har lokaci yaja. Tayi mamakinsa matuk’a yadda lokaci guda ya sake da ita, har ya tsaya yana zuba mata surutu haka, wadda ji take kwata-kwata kamar ba doctor Arman data sani take jin labarinsa ba, take gani a gidajan Tv da redio, wai shine a cikin waya yake mata sauk’in kai haka, ta kasa gaskata abun. Ta sakko ne da murna domin ta sanarma Mimi ta iske wannan tashin hankali da Mimi take ciki, na Y’ay’ansu Aliyu da matarsa, wadda auransu bai wuce shekara biyu da yinsa ba, matar y’ar asalin garin Katsina ce, acan suka gamu wajan wani taron kasuwancin Abbie d’aya wakilta zuwa suka had’u da Husaina.

“Bari Lalaah muna cikin tashin hankali, why da Husaina baza ta hau jirgi ba?, tasan hatsarin hanyar dake garin su”

“Dan Allah Mimi ku kwantar da hankalin ku insha Allah Aunty Husaina tana nan cikin k’oshin lafiya, kawai isane basu yi da wuri ba”

Lilaah ce ta shigo parlon itama duk hankalinta ba’a kwance yake ba. Amma ita damuwarta daban take da taso, domin ita dama kullum damuwarta bai wuce ta Arman ba. Ganin su haka yasa ta d’an tsaya kamar abun arzik’i ta ce “Mimi mi yake faruwa ne haka, na ganku haka”

“Hmm Aunty Husaina ce ta d’auki hanyar katsina daga Abuja gidanta, shine har yanzu bata isa ba, kuma wayarta ita da drivern bata shiga har yanzu kuma tun safe suka d’auki hanya, amma Kinga yanzu har tara na dare shuru basu isa ba. Can gidan nasu ma hankalinsu ya fara tashi soma, danma Y Aliyu na b’oye masu wani abun”

D’an jim Lilaah tayi kamar wacce zata ce abun arzik’i sai kuma ta ce “ai kaji matsalar d’an k’auye wallahi, ai shine yaji ya gani, Allah ya bayyana ta”

Ta na idasa fad’ar haka tayi sama abunta.

 Mimi cike da takaici zata mata magana Lalaah ta girgiza mata kai, alamar tayi hakuri.

Lilaah kuwa gani take ai ita wannan ba damuwarta bane. Shi Aliyun shita shafa, gashi dama haushinsa take ji yaje ya auro masu y’ar k’auye taso ya auri Bilkees k’awarta.

<< Kaddarar So 7Kaddarar So 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×