Littafi Na Biyu
Wani abu da ya ja hankalin Mama akan Safiyyah shine har zuwa wannan lokacin Safiyyah ba haihuwa, ba ko batan wata balle a saka ran samuwar ciki. Duniya kam daidai gwargwado suna cikinta itada mijinta suna juya jin dadinta son rai, itada Zayyan basu nemi komai sun rasa ba, amma haihuwa shiru kake ji ko sama ko kasa kamar an aiki bawa garinsu, tuni anyi auren duka ‘ya’yan Mama saura Hatoon, itama din da saka ranarta a kanta.
Mama tana Katsina bata zuwa Abuja, amma kullum Zayyan yazo gabanta sai. . .