Musamman saboda habaicin da Mama da ‘ya’yanta suke sakar mata directly and indirectly.
Ta jima tana sayen PT Strip a boye, bada saninsa ba tana gwada kanta, in taga babu komai haka zatayi kuka a toilet ta gaji ta wanke fuskarta ta fito, ta shiga harkokinta.
Ya zamanto cewa Safiyyah ko dan ciwon kai take yi ko zazzabi sai ta roki Allah yasa laulayin ciki ne. Haka zata shige toilet yin PT, amma kullum amsar daya ce “negative”.
Safiyyah ta fara tunanin ko bata gamsar da mijinta ne shiyasa ta kasa daukar ciki? Gashi ita bata yarda da wani. . .