Don haka tun wuri ki nemi Kakar diyanki in kin haifa a can Dandume, bani Fatun Bello Rafindadi ba, don ban yarda da halaccin haihuwarsu a addinin musulunci ba...”.
Safiyyah kasa karasa sauraron Mama tayi, ta saki wayar a kan kujera tana fidda hawaye masu zafi.
Ba cin mutuncin Mama gareta ne ya sata kuka ba. Face jin a fakaice Mama na son tabo mutuncin iyayenta, cewa basu san Allah ba. Alhalin su ko sanin anyi dashen ma basu yi ba.
Zayyan bai san da wannan wayar da Mama ta bugowa Sophie ba, itama kuma bata gaya masa ba, ita. . .