Ni ban ma cika son harkar maganin gargajiya ba Haj. Yabi, nafi yarda da asibiti, amma tunda na matsu na ga diyan Baffa gara a jarraba can din, ba’a san inda za’a dace ba, tunda anyi na asibitin duk ba nasara”.
Duk sauran matan suka ce “exactly, gara a jarraba na gargajiya”.
Baki daya falon sai ya karade da zancen rashin haihuwar Safiyyah har tsayin shekara goma da aure, kannen sa daga mai biyu sai mai uku, kowacce na tofa abinda take tunanin shi ya hana Safiyyah haihuwa, har da masu cewa ko PCOS gareta, don mafi akasari. . .