Yana ganinta yarinya, mai tarin wauta, ashe-ashe tasan abinda take yi? Meye dalilin son kara aurensa? In har yanada komai da yake bukata a gidansa? Shine assignment dinda shima ya baiwa kansa a yanzu.
Dalilai da yawa masu muhimmanci sun yi mujazar wannan son karin auren, domin yana ganin shine kadai maslaha a gare su shida Safiyyah, don yana sha’awar mace irin Azeezah a gidansa da rayuwarsa, yana son mace ‘yar gayu, mai wayewar kai, domin likely mace mai body shape dinta da irin dirarrun dugadugan kafar Azeezah itace daidai shi. Ustazancin Sophie yayi masa yawa, tsayin. . .