Kuka ta saka masa, shi kuma ya soma lallashinta har da roko. Bai sakaya mata yadda bijirewarta gare shi ya saka shi sha’awar kara aure ba. Duk da bai fito fili ya fada mata har auren ya nema ba, an kuma bashi, amma kuma Safiyyah duk ta sha jinin jikinta.
Wanda hakan ya sa ta kara jin bacin ranta ya ninka na baya. Wani abu da Zayyan bai taba yi ba shi ne, tursasata kan ta yarda da shi, amma yau? Yadda yake so haka ya sarrafa Sophie, alhalin taki amincewa, yace saidai duk su mutu amma bazai iya. . .