An saka ranar daurin auren Zayyan da Azeezah sati biyu masu zuwa, wata daya da zuwan shi Lagos. Baya kiran Azeezah a gaban Safiyyah, haka ko ita ta kira shi in Safiyyah na wuri bai amsawa.
Ranar daurin auren na matsowa fargabar Zayyan na karuwa saboda silent treatment din Safiyyah gare shi. Ko da can Safiyyah mai biyayya da yakanah ce, da kula da shi, kai dai barta da kunya da nuku-nuku a gado da kin yi masa yadda yake so, da dressing irin yadda yake son ta yi masa. Kullum Safiyyah kara samun nutsuwa take saboda nasihohin Ammi. . .